FIRST AID GROUP of Jibwis Mariri Detachment

FIRST AID GROUP of Jibwis Mariri Detachment Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from FIRST AID GROUP of Jibwis Mariri Detachment, Religious organisation, Binawa Road Mariri, Kaduna South.

Hotuna: Tattaunawar shugaban IZALA da tawagarsa sun gana DA shugabannin Dalibai mazauna kasar Egypt (Masar) domin tallaf...
18/09/2022

Hotuna: Tattaunawar shugaban IZALA da tawagarsa sun gana DA shugabannin Dalibai mazauna kasar Egypt (Masar) domin tallafa musu da shawarwari akan karatu.

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

Allah y karawa Malam lafiya Mai albarka Ameen
16/09/2022

Allah y karawa Malam lafiya Mai albarka Ameen

Shugabannin Makarantar Marayu Mallakin Kungiyar Izala ta jihar Kaduna na Kafin Allah Gaba Academy da s**a kawo ma Shugab...
16/09/2022

Shugabannin Makarantar Marayu Mallakin Kungiyar Izala ta jihar Kaduna na Kafin Allah Gaba Academy da s**a kawo ma Shugaban Kungiyar Izala na Jihar Kaduna Alh Adamu Ibrahim ziyarar aiki a Ofishin sa a safiyar yau.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'unShugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, na mika sakon ta'aziyya a madadin kungi...
14/09/2022

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, na mika sakon ta'aziyya a madadin kungiyar IZALA ga 'yan uwa da iyalai da al'ummar jihar Taraba bisa rasuwar daya daga cikin 'yan agaji amatakin kasa, Malam Hassan Abdullah Jalingo.

Marigayin ya rasu a safiyar talatar nan ba tare da wani jinya ba, illa Ajali yazo. kuma za'a masa janaza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a kofar Gidan sa dake bayan Tukur Firamare Sukul a cikin birnin Jalingo dake jihar Taraba.

Sheikh Bala Lau yayi addu'ar Allah ya jikansa da rahama, ya baiwa iyalensa damu hakurin rashi, ya hadamu da shi a jannatul fir'dausi ranar gobe kiyama.

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

AN KADDAMAR DA NI'SA'USSUNNAH A MASARAUTAR RANO✍️ A BelloShugaban JIBWIS na jihar Kano Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Pa...
12/09/2022

AN KADDAMAR DA NI'SA'USSUNNAH A MASARAUTAR RANO

✍️ A Bello

Shugaban JIBWIS na jihar Kano Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya jagoranci ƙaddamar da shugabannin matan Nisa'ussunnah na ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin masarautar Rano, wanda s**a hada da Rano, Takai, Sumaila, Tudun Wada, Bunkure, Kibiya, Kura, Garun Malam, Doguwa Da Bebeji.

An ƙaddamar da shugabancin na su ne a ranar Asabar 10-09-2022 a babban masallacin Juma'a na JIBWIS dake garin Tudun Wada.

A cikin jawabin da farfesan ya gabatar a yayin taron ta bakin wakilin sa kuma babban sakataren ƙungiyar na jihar Kano Malam Hassan Bunyamin Mandawari, ya yi kira da waɗannan shugabanni dasu sani cewa Nisa'ussunnah wani yanki ne daga cikin kungiyar Izala wanda ya shafi mata domin ilimantarwa, wayar da kai da kuma wa'azi ga junansu. Su kasance masu aiki tuƙuru domin tabbatuwar cigaban addinin musulunci, sannan ya ƙara da cewa mata suna da matuƙar muhimmanci a addini da cigabansa musamman idan aka yi duba da irin yadda mata magabata s**a yiwa addini hidima wanda tun farko musulunci ya fadi irin gudummawar da s**a bayar da kuma wacce suke bayarwa har yanzu.

A na ta ɓangaren Malama Zainab Ja'afar Mahmud Amirar Nisa'ussunnah reshen jihar Kano ta sanyawa kowacce ɗaya daga cikinsu maratayi mai dauke da sunan karamar hukumar su a jiki wanda hakan ke nuna an shugabantar da su a ƙananan hukumomin da s**a fito. Acikin jawabin da ta gabatar gare su tayi kira na musamman kan cewa dukkansu su san cewa babbar manufar da aka saka a gaba shine yaɗa sunnar Annabi (S.A.W) lungu da saƙo na al'umma musamman wannan tafiya ta ɓangaren mata ya zamto ko ina idan aka bude ido a ga sunnah ita ce ke haskawa ta ɓangaren sanin ilimi da mu'amala, samun ingantacciyar tarbiyya da gyaruwar al'umma baki-ɗaya shine babban abinda wannan tafiya ta ƙunsa. Tayi kira na musamman ga gwamnati, mawadata da sauran al'umma da su kasance masu bawa wannan tafiya gudummawa ta kowacce irin fuska domin cigaban al'umma baki-ɗaya.

09/09/2022

Happy Juma'a
2 All Muslim

Gudunmowan fatun layya!A taimaka domin cigaban aiyukan Alkhairi d ake yi.
07/07/2022

Gudunmowan fatun layya!
A taimaka domin cigaban aiyukan Alkhairi d ake yi.

SANARWA  SANARWA  SANARWA
26/03/2022

SANARWA SANARWA SANARWA

Shugaban Kungiyar Jibwis na Jihar Kaduna Alh Adamu Ibrahim na sanar da Seminarn Tafseer na kwana 1, wanda Majalisar Malamai ta jihar ta shirya, wanda za'a gudanar gobe Lahadi in Allah ya kaimu, a Filin Musabaqah Kinkinau Kaduna.

Allah ya bada ikon halarta.

Ibrahim Shehu Giwa.
PRO JIBWIS Social Media Kaduna State.

Address

Binawa Road Mariri
Kaduna South

Telephone

+2349166873605

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FIRST AID GROUP of Jibwis Mariri Detachment posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share