Muryar Halkal Laranto Jos

Muryar Halkal Laranto Jos Bismillah. Wannan shine shafin Halkal Imam Baqeer (a.s) wanda aka fi sani da Halkal Laranto Jos.

09/04/2026
بسم الله الرحمن الرحيم یاَ اٴَیَّتُھَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةّ ارْجِعِی اِٴلٰی رَبِّکِ رَاضِیَةً مَرْضِیَّةً فَادْخُل...
01/03/2026

بسم الله الرحمن الرحيم

یاَ اٴَیَّتُھَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةّ ارْجِعِی اِٴلٰی رَبِّکِ رَاضِیَةً مَرْضِیَّةً فَادْخُلِی فِی عِبَادِی وَ ادْخُلِی جَنَّتِی

اِنَّا لِلّٰہِ وَاِنَّآ اِلَیْہِ رَاجِعُوْنَ' 😭

Muna Taya Al'ummar Musulmi Murna Da Zagayowar Ranar Haihuwar Imam Mahadi Bn Hassan (Ajf), Khalifan Manzon Allah (Saww) N...
03/02/2026

Muna Taya Al'ummar Musulmi Murna Da Zagayowar Ranar Haihuwar Imam Mahadi Bn Hassan (Ajf), Khalifan Manzon Allah (Saww) Na 12 Kuma Na Ƙarshe🌹.

قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم؛

افضل الأعمال الإنتظار الفرج.

Fassara......

Manzon Allah (Saww) Ya Faɗa Acikin Hadisi Cewa;

''Mafificin Ayukka Shine Jiran (Mafita), Wato Jiran Bayyanar Imam Mahadi (AJF)''.

An Haifi Sahibul Asr Wazzaman Imam Mahadi (Ajf), Ranar 15 Ga Watan Sha'aban Shekara Ta 255 Bayan Hijirah, a Daren Jumu'a, Sunan Mahaifinsa Shine Imam Hassan Al'askari (AS) Khalifan Manzon Allah (Saww) Na (11), Mahaifiyarsa Itace Sayyidah Narjis (AS).

Imam Mahadi (AJF) Shine Cikamakon Imamai 12 Bayan Manzon Allah (Saww), Kuma Shine Mai Ɗaukar Fansar Iyalan Gidan Manzon Allah (Saww), Imam Yayi Fakuwa Ƙarama (Gaibatus Sugra) Daga Baya Yayi Fakuwa Babba (Gaibatul Kubra) Saboda Ya Rasa Mataimaka a Lokacin, Kuma Bazai Dawo Duniya Ba, Sai Ya Samu Mataimaka 313, Kuma Annabi (Saww) Yace Idan Ya Bayyana Zaiyi Yaƙi Da Azzalumai Irinsu Dujjal (L), Kuma Shizaiyi Nasara Akansu Insha Allah, Kuma Wannan Zamanin Da Muke Ciki Zamaninsa Ne Kuma Shi Muke Jira, Domin Yadawo Ya Ƙwato Ƴancin Addinin Musulunci, Kuma Daga Cikin Sharaɗin Bayyanar Sa Sai Duniya Ta Cika Da Zalunci Da Fajirci, Sannan Ya Bayyana Ya Dawo Da Gaskiya Da Adalci a Duniya.

Muna Roƙon Allah (SWT) Yasamu Cikin Masu Jiransa Na Haƙiƙa🤲🏻.

Kuma Yau Yayi Daidai Da Ranar Da Aka Haifi Babban Mataimakin Imam Mahadi (Ajf), Shine Sheikh Ibrahim Yaqub Zakzaky (H), a Yau Yake Cika Shekara 75 a Duniya, Muna Taya Su Malam (H) Murna, Muna Roƙon Allah (SWT) Ya Ƙarawa Su Malam (H) Lafiya, Kuma Ya Cika Masu Burinsu Na Tabbatar Addinin Musulunci a Wannan Nahiyar Tamu, Mu Kuma Allah (SWT) Kasa Muna Cikin Mabiyansa Na Haƙiƙa🤲🏻.

@ Abubakar Nuhu T/Mafara.
@
@
@
@ .
15/Sha'aban/1447H.
03/February/2026M

HOTUNA daga gurin taron Maulidin Sayyida Zahra (s.a) da Mijinta ZAKIN ALLAH Imamu Aliyu (k) wanda yan uwa na Majalisin N...
13/01/2026

HOTUNA daga gurin taron Maulidin Sayyida Zahra (s.a) da Mijinta ZAKIN ALLAH Imamu Aliyu (k) wanda yan uwa na Majalisin Nefa/Mista-Ali dake Halkal Laranto s**a shirya a ranar Lahadi 11/1/2026.

MASHAALLAH, ALLAH YA KARƁA MANA

11/01/2026

Raɗin suna 3️⃣ cikin sati 2️⃣ a Laranto wanda Mal. Sulaiman Aliyu ya jagoranta.
Fatima (BATULA) yar wajen Mal. Haruna Hassan, Fatima (ZAHRA) yar wajen Mal. Suyuɗi sai kuma AHMAD ɗan wajen Mal. Abdulƙadir Yahaya.

🎉🎉🎉

mashaAllah. Sheikh Jawad Adamu Tsoho Jos Halkal Laranto na matukar godiya 🙏 ALLAH ya saka muku da mafificin Alkairi ya k...
04/01/2026

mashaAllah. Sheikh Jawad Adamu Tsoho Jos Halkal Laranto na matukar godiya 🙏 ALLAH ya saka muku da mafificin Alkairi ya kuma ƙara jaddada Rahama ga ruhin Mahaifin ku kuma Uban Mu MARHUM SHEIKH ADAMU TSOHO🤲😭

Gayyatar Taron Maulidin Sayyida Zahra (s.a) da Imam Ali (k)---------------------------------------- Madarasatul Saqafa I...
02/01/2026

Gayyatar Taron Maulidin Sayyida Zahra (s.a) da Imam Ali (k)
----------------------------------------
Madarasatul Saqafa Islamiyya Laranto Jos na farin cikin gayyatar wanda ALLAH ya bawa ikon zuwa gurin Taron Maulidin Nana Faɗima da Mijin ta Imam Aliyu (amincin ALLAH ya tabbata gare su) wanda zai gudana kamar haka.

RANA:- Asabar 14/7/1447 -- 3/1/2026
LOKACI:- Karfe 7:30nd
MUHALLI:- Ung/bayan Seminary Laranto.

Babban Baƙo mai jawabi:- Sheikh Jawad Adamu Tsoho Jos

Allah ya bada ikon halarta.

Address

Katako Laranto Jos
Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Halkal Laranto Jos posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share