Fassarar kawa idi da transliteration na hausa

Fassarar kawa idi da transliteration na hausa Assalamualaikum ahlan wa sahlan

TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD(SAW):Kashi Na 01Nasabarsar ta bangaren mahaifinsa: Muhammad(saw) dan Abdullahi, dan ...
08/11/2022

TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD(SAW):

Kashi Na 01

Nasabarsar ta bangaren mahaifinsa: Muhammad(saw) dan Abdullahi, dan Abdul-Mutallib, dan Hashim dan Abdul-Manaf, dan Kusayyi dan Kilabi… nasabarsa(saw) madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Adam(as) a tsatson masu sujadah da tsarki.

Nasabarsa ta bangaren Mahaifiyarsa: Ita ce Aminah ‘yar Wahabi, dan Abdul-Manaf dan Zuhrata dan Kilabi… nasabarsa ta fuskar mahaifinsa da mahaifiyar tahadu wajen Kilab zuwaga Annabi Adam da Hauwa(as).

Wadanda s**a reneshi: Abdul-Mulib, Halimah As-Sa’adiyya, da Abu Talib.

Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Lakabinsa: Al-amin, Al-mustafah…

Sunayensa da s**a zo a cikin Kur’ani mai girma: Khatamun-nabiyyin, Al-ummi, Al-muzzammil, Al-muddassir, An-nazir, Al-mubin, Al-karim, An-nur, Anni’ima, Ar-rahma, Al-abdu, Ar-ra’uf, Ar-rahim, As-shahid, Al-mubasshir, An-nazir, Ad’da’i…

Tarihin haihuwarsa: An haifi Monzon Allah(saw) a Ranar Jumu’ah, 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571 M) (bisa mash’hurin zance daga Ahlul-Bayt(as) (amma a wata ruwayar an haifeshi(saw) ranar Litinin 12 Rabi’u-auwal).

Inda aka haifesa: Makka.

Tambarin zobensa: Muhammadur-Rasulullah!

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.

Aikoshi: An aiko shi a Makka, 27 Rajab; yana dan shekara 40.

Koyarwar sakonsa: ya zo don daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame, sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah(swt), su kuma Musulmi s**a karba daga gare shi.

Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Qur’ani, amma wadanda s**a faru a farkon Musulunci suna da yawa; ba zasu kirgu ba, misali, tsagewar wata.

Kiransa

Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara 3, ya kuma kira su a bayyane shekara 10.

Hijirarsa:

ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal, bayan shekara 13 daga aikosa, wannan ya faru ne sak**akon cutarwa daga kafirai; gare shi da kuma Sahabbansa.

https://youtube.com/channel/UCjESFp9bFn

05/11/2022
05/11/2022

Girgije Mai shayarwa
Arziki Mai yanke talauci Farin ciki maganin Bakin ciki da Takaici 🤲Muhammadu Rasulillah 🤲💚🤲

05/11/2022

Muminai Zasu Fito
Daga Cikin Kabari Suna Fa'din
لا إله إلا الله محمد رسول الله

💚💚💚💚💚💚💚💛💛💛💛💛💛_💜NI'IMOMIN DA ALLAAH YA MA MUSULMI KA'DAI!💚~~_1. Aiko Annabi Muhammad (SAW)._ _2. Sauko da Alkur'ani.__3. ...
05/11/2022

💚💚💚💚💚💚💚💛💛💛💛💛💛
_💜NI'IMOMIN DA ALLAAH YA MA MUSULMI KA'DAI!💚
~
~
_1. Aiko Annabi Muhammad (SAW)._
_2. Sauko da Alkur'ani._
_3. Imani da Allaah (SW)._
_4. Imani da Annabi Muhammad (SAW)._
_5. Yarda da Alkur'ani._
_6. Bauta Ma Allaah a bisa tsarin da Annabi ya bada umurni._
_7. Fata da zaton samun shiga Aljanna._
°
°
_Wace ni'ima tafi wannan?!!! Duk Duniya babu ni'imar da tafi wannan. Babu mai samun haka face wanda Allaah Ya so shi da alkhairi. Allaah Ya tabbatar da mu akan aqida da manhaji na 'kwarai har cikin Aljanna._
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

05/11/2022

Kanada lokacin Rubuta
🕋🕌 S 🕌🕋
🕋🕌 A 🕌🕋
🕋🕌 W 🕌🕋

05/11/2022

cikin kyawawan sunan allah me rahama daure ka fadi daya domin girman annabi

05/11/2022

Salati goma ga Annabi
Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam

04/11/2022

Wa'azi Akan Zina

Ma’anar zina da hukuncinta:
Lafazin zina a shari’ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, k**ar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata.” Muslim.
A cikin wannan Hadisi za mu ga yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa kowane dan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai samu wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a k**a shi da laifi ba, har sai idan ya gaskata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko kafarsa s**a jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan bukatar wadannan gabbai. Wannan shi ne ma’anar fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a karshen Hadisin, “farji shi yake gaskata haka ko ya karyata.” (Sharhin Sahih Muslim na Imam Nawawi Juz’i na 16, shafi na 216).
Hukuncin zina:
Zina haramun ce a addinin Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Ya haramta ta inda Yake cewa : “Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna.” (Isra’i:32).
Malamai suna cewa, fadin Allah “kada ku kusanci zina,” kai matuka ne wajen hana ta, don ya fi a ce “kada ku yi zina.

04/11/2022

Duk Mai Son Cigaba,To Ya Hori Kansa Da Yiwa

Annabi Salati❤️
Sallallahu Alaihi Wasallam💖

04/11/2022

God bless proper annabi Muhammad sallallahualaihiwasallam. No body can stop nasiya annabimuhd

Address

Jos

Telephone

+2347045485111

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fassarar kawa idi da transliteration na hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Fassarar kawa idi da transliteration na hausa:

Share