Jibwis National HQ Jos

Jibwis National HQ Jos Official Page Of Jibwis National HQ Jos Founded By Late Sheikh Ismail Idris Bin Zakariyya
(18)

23/08/2026
MAZAN JIYAMarigayi Sheikh Abbas Hamid Abbas BUK ya bar duniya yana da shekaru 86.Sheikh yana daya daga cikin manyan mala...
21/08/2026

MAZAN JIYA

Marigayi Sheikh Abbas Hamid Abbas BUK ya bar duniya yana da shekaru 86.

Sheikh yana daya daga cikin manyan malamai na Ahlus-Sunnah a wannan kasa wadanda s**a yi gwagwarmaya wajen karantar da Sunnah, musamman a karkashin wannan kungiya mai albarka: Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'ikamatis Sunnah, wadda hedkwatarta ke Jos, Nigeria.

Malam ya rasu a ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamba 2008 a birnin Kano, kuma a ranar aka yi masa Jana'iza.

Sheikh Abbas limamin Juma'a ne a babban Masallacin Juma'a na Jami'ar Bayero University Kano, BUK.

Kuma shine Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izala ta Jihar Kano na farko kafin Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam. Bayan Sheikh Jafar ya tafi karatu a Madina, sai aka sake bawa Sheikh Abbas ya rike wannan mukami har zuwa kafin rasuwarsa.

Sheikh wa'azinsa na karshe a matakin kasa da kasa shine Wa'azin Kasa da aka gudanar a filin Polo, a Maiduguri, Jihar Borno a shekarar 2008, shekarar da ya rasu. A lokacin yayi wa'azi sosai akan masu ra'ayin Boko Haram kuma da harshen Kanuri yayi wa'azin.

Asalinsa kabilar Shuwa ne, kuma dan karamar hukumar Kala/Balge ne a Jihar Borno. Dalilin neman ilimi ne ya kaishi Jihar Kano, har ya zama ya rike wadannan mukamai masu daraja.

Allah ya jikansa, ya gafarta masa, ya haskaka kabarinsa. Ameen.

Jibwis Internet Media Committee
JIBWIS National HQ Jos- Nigeria 🇳🇬
Friday, 21st August, 2026
[email protected]

21/08/2026

Tafsir t3lam kanuriye suratu Hadid

Masjid Imam Bukhari moduganari bypass, Maiduguri.

14/08/2026

Tafsir t3lam kanuriye= suratu Hadid

Masjid Imam Bukhari moduganari bypass, Maiduguri.
Sheikh Muhammad Mustapha Albarnawi

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..Izalah Tayi Babban Rashi na Daya Daga Cikin Alarammomin Farko...Allah ya karbi rayuw...
14/08/2026

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un
..Izalah Tayi Babban Rashi na Daya Daga Cikin Alarammomin Farko...

Allah ya karbi rayuwar Alaramma Malam Yakubu Garba Maiduguri.

Za'ayi Jana'izarsa
Yau Jumma'a, 14th August, 2026
Lokaci: 4:00pm, bayan Sallar La'asar
Wuri: Masallacin HQ JIBWIS Borno, dake Gwange zuwa da wuri junction, Maiduguri.

Marigayi Alaramma Yakubu Garba yana daya daga cikin Alarammomin Kungiyar Izala tun farkon kafuwarta.

Muna rokon Allah SWT ya jikansa da rahama, ya gafarta masa, hidimar da yayi Allah ya sanya ta a mizani.

JIMC BORNO STATE
Jumma'a, 14th August, 2026

Address

Yan Taya
Jos
930221

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis National HQ Jos posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis National HQ Jos:

Shortcuts

Share