Jibwis social media nape yalwa

Jibwis social media nape yalwa r al mangiwi

07/04/2021

SUNAYEN MALAMAI DA ALARAMOMI DA JIBWIS TA KASA TA TURA TAFSIRI RAMADAN NA 1442/2021 A JAHOHIN NAJERIYA
1-Shaikh Dr. Abdullahi Bala Lau da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu, Jimeta Adamawa

2-Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo da Alaramma Mustapha Jalingo, Jalingo Taraba

3-Sheikh Usman Isa Taliyawa da Alaramma Abubakar Muhd Gombe, Gombe.

4-Sheikh Abbas Jega da Alaramma Abubakar Adam. B/Kebbi, Kebbi.

5-Shaikh Ibrahim Sabiu Jibiya da Alaramma Aminu Salisu Jibiya, Masjid Hamza Jibiya, katsina.

6-Sheikh Yakubu Musa Hassan da Alaramma Usman Birnin Kebbi, Masjid Kandahar Katsina

7-Sheikh Pro. Abdullahi Saleh P**istan da Alaramma Abbas Iliyasu Kano, Tudun Martala, Kano.

8-Sheikh Dr, Muh’d Kabir haruna Gombe da Alaramma Ahmad Sulaiman, T/Wada/Malali, Kaduna.

9-Sheikh Abubakar Giro Argungu da Alaramma Saifullahi Musa Makera, Kwantagora, Niger.

10-Sheikh Aliyu Abdullahi Telex da Alaramma Muhsin Ishaq, Aleiru, Kebbi

11-Sheikh Surajo Muhammad Gusau da Alaramma Jamilu Muhammed Dan Magi, Gusau, Zamfara

12-Sheikh Mas’ud Ibrahim Offa Offa, Kwara

13-Dr. Muhammad sani Umar R/lemo da Alaramma Abubakar Muhammad Rariya, Masjid Gwallaga, Bauchi

14-Sheikh Sani Yakubu da Alaramma Ridwan Kaduna, Zariya Kaduna

15-Sheikh Dr. Ismail Kumo Basirka da Alaramma Abdulrashid Sulaiman Jega, Minna, Niger

16-Sheikh Ahmad Muhammad Boyi da Alaramma Muhammad Aliyu Babangida, Masjid Finance Jalingo, Taraba

17-Dr. Ibrahim Abdullahi R/Lemo Alaramma Abdullahi Salisu, Western by Pass, Kano

18-Prof. Umar Labdo da Alaramma Aliyu P**i Abuja, Berger Masjid Abuja

19-Mal. Imam Aliyu bunza da Alaramma Sulaiman Adamu, Argungu Kebbi

20-Sheikh Gambo Kyari Maiduguri da Alaramma Adam Alhaji Allawan, Masjid Tashihul Aqida, Dikwa Low cost Borno

21-Sheikh Modibbo Muctar Gaundare da Alaramma Dahiru Musa Jega, Gire Adamawa

22-Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale da Alaramma Saifullahi Kira, Area 11, Abuja

23-Dr. Zakariya Idris da Alaramma Usman Ya’u Gido, Gumel, Jigawa

24-Dr. Bishir Iman, Masjid Amd. Yola, Adamawa

25-Dr. Sadau Salihu, Yola Adamawa

26-Dr. Magaji Zarewa da Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi, Lagos Lagos.

27-Dr. Abubakar Ali Bama, Karem Lamido, Taraba

28-Dr. Abdulrahaman Sani Yakubu da Alaramma Hudu Usman Ashiru, Juwa Emirate Council, Abuja

29-Mal. Usman AbdulHamid, Numan, Adamawa

30-Dr. Ibrahim Adam Umar Disina, Masjid Rahama, Bauchi

31-Sheikh Prof. Mansur Ibrahim sokoto da Alaramma Abubakr Gani, Masjid Abu Huraira, Sokoto

32-Dr. Muhammad Rabi’u Collage da Alaramma Sidi Ali, Gashua, Yobe

33-Mal. Hussaini Isa Abubakar da Alaramma Salihu Mukhtar, Makurdi, Benue

34-Mal. Muhammad Dawud Damaturu, Damaturu Yobe

35-Mal. Abdulbasir U/Maikawo da Alaramma Sani Malumfashi, Wukari Taraba

36-Mal. Ali Aliyu Jos da Alaramma Baba Abubakar Tambuwal, Tambuwal Sokoto

37-Mal. Umar Mai Damma da Alaramma Auwal Adam Sokoto, Masj Shk Ab Gumi Sokoto

38-Mal. Abubakar ladan Mai Idigami da Alaramma Muhamma Auwal Sokoto, Masj Lokoja Road Sokoto

39-Mal. Abdurrahman sani Mai Tawul da Alaramma Hassanu Abubakar Umar, Sultan Ibrahim Dasuki

40-Dr. Abubakar Usman Ribah da Alaramma Muhammad Bunza Borgu, Niger

41-Mal. Saifuddeen Yakubu musa, Masjid kandahar Katsina (Tafsirin Mata)

42-Dr. Nazifi Yunus Jos da Alaramma Faruq Jada Tambuwal, Jos plateau

43-Mal. Abdulwahid Abubakar Sulaiman da Alaramma Umar Ibrahim, Villa A Abuja

44-Dr. Ali Yunus, Usman Bn Affan Gado Kaya Kano

45-Dr. Sani Suleiman Jibia Da Alaramma Ahmad sani Sulaiman Masjid Mamman Barda, katsina

46-Dr. Uthman Sani Haruna da Alaramma Yusuf Ibrahim Jalo, Lafiya, Nasarawa

47-Dr. Zubairu Madaki da Alaramma Kabir Abdullahi Bauchi Masjid Umar bn Al khattab, Kofar Wambai, Bauchi

48-Dr. Adam Usman Nengere da Alaramma Usman Barikin Ladi, Jumeta, Adamawa

49-Mal. Abdulrahman Muhammad, Kano state University Wudil, Kano

50-Mal. Abdul Razak Yahaya Haifan da Alaramma Kabir Hussaini Daura, Gwagwalada, Abuja

51-Mal Abdullahi Umar Zaria da Alaramma Mustapha Shuaibu Garki Village, Abuja

52-Mal. Moh'd Auwal Abubakar (M/gaskiya) da Alaramma Aliyu Ibrahim P**i, Fed. Min. of Works Abuja

53-Mal. Abdullahi Karshi da Alaramma Salihu Gumi, Villa B Abuja

54-Mal. Adam Isah Sahibul Kuwa, Dakkwa Abuja

55-Mall. Aliyu Ladan da Alaramma Tukur Jakada, Life Camp Abuja

56-Mal. Umar Sadiq Jega da Alaramma Yusuf Suru, Kamba Kebbi

57-Dr. Abdallah Umar Gadon Kaya da Alaramma Baba Lawal, kanbarikin,(Water Board ) Kumo, Gombe

58-Mal Abdulrahman Alzamfari da Alaramma Muhammad Kabir Yunus/Abdulbasid Surajo Gusau, Masjid Muhajirun Wal-ansar Dutsen Alhaji, Abuja

59-Mal. Tajuddeen Imam da Alaramma Murtala Muhammad Prince & Princes, Abuja

60-Mal. Aliyu Saeed Gamawa da Alaramma Saeed Adamu, People Bank Masjid Gamawa, Bauchi

61-Mall. Ibrahim Idris Zakariyya da Alaramma Mujtapa Shuaibu Yusuf, Tirden Fulani, Bauchi

62-Mal. Nazifi Hashim da Alaramma Dauda Alkasim Wukari, Alkaleri Bauchi

63-Shk. Ahmad Tijjani Yusuf Guruntun da Alaramma Mahmud Zaharaddin, Masj S19 Dutsen Tenshe Bauchi

64-Barr. Sheikh Garba Hassan Alaramma Abduljalal Usman, Masjid Abu Huraira New GRA Bauchi

65-Sheikh Sulaiman Yusuf Bashir da Alaramma Abubakar Usman T/former, Masallacin Adamu Jumba Housing Estate, Bauchi

66-Sheikh Babangida Sulaiman da Alaramma Adam Adam Muhammad, Masallacin Juma'a na Gwallga (Karatun Safe) Bauchi

67-Sheikh Kabiru Ahmed Azare da Alaramma Sulaiman Abdullahi, Masjidus Sunnah Sardauna Road Azare, Bauchi

68-Imam Muhammad Manga Abba Zadawa da Alaramma Idris Ibrahim Kolo, Masallacin Jibwis Zadawa Misau, Bauchi

69-Alkali Ridwan Abubakar Alaramma Yahaya Tudun Maliki, Masallacin Jibwis Fed. Lowcost Misau, Bauchi

70-Imam Magaji Bappa Sulaiman da Alaramma Aliyu Ahmad, Masallacin Ali bin Abi-Talib gandum Wambai A. Bauchi

71-Imam Ibrahim Adam Narabi, Masallacin Jibwis Magam Gumau, Bauchi

72-Sheikh Ibrahim Haruna Dambam da Alaramma Aliyu Ahmad, Masallacin Jibwis Dambam, Bauchi

73-Sheikh Yakubu Isma'il da Alaramma Ibrahim Musa, Masallacin Jibwis Dass, Bauchi

74 Sheik Haruna Musa Riban Garmu da Alaramma Sani ishaq, Masallacin Jibwis Kirfi, Bauchi

75-Sheikh Yunusa Abubakar, Masallacin Haudah Jibwis Jama'are, Bauchi

76-Sheikh Musa Yakubu da Alaramma Rufa'I Abdulqadir, Masallacin Jibwis Kafin Madaki Ganjuwa, Bauchi

77-Imam Habibu Garba Baima da Alaramma Abdulkarim Muhammad Baima, Masallacin Jibwis Warji Bauchi

78-Sheikh Sadisu Yusuf Konkiyal da Alaramma Mal. Yakubu Sabo, Masallacin Jibwis Darazo, Bauchi

79-Sheikh Muhammad Albashir Ningi da Alaramma Sulaiman Muhammad, Masallcin College of Health and Tech Ningi, Bauchi

80-Imam Abdurrahman Ibrahim idris da Alaramma Huzaifa Yakubu Sambo, Masjidus Sahaba New GRA Bauchi

81-Sheikh Dalhatu Babaji Mball da Alaramma Yusha'u Adam, Masallacin Jibwis Burga Tafawa Balewa, Bauchi

82-Sheikh Salisu Isa Saidu Kurgui da Alaramma Sale Abdussalam, Masallacin Jibwis Sabon Kaura, Bauchi

83-Sheikh Mahmud Ibrahim Shira, Masallacin Jibwis Ibrahim Bako, Bauchi

84-Sheikh Umar Baba Hanafari da Alaramma Yahuza Aliyu, Masjid Abubakar Gumi, Bauchi

85-Dr. Abdullahi Jaji da Alaramma Hussaini Alhaji Bauchi, Masjid Usman Bn Affan, Bauchi

86-Mal. Anas Adamu da Alaramma Faisal Abdulmumin, Masjid Umar Bn Alkattab, Bauchi

87-Mal. Tanimu Tahir da Alaramma Tahir Ahmed Alkaleri, Masjid Jibwis Alkaleri, Bauchi

88-Mal. Aliyu Yau Assurubun da Alaramma Dauda Ibrahim Katagum, Masallacin Jibwis Zaki, Bauchi

89-Sheikh Muhammad Bukar Albagawy da Alaram Bako Bello, Ningi Bauchi

90-Mal. Yaqub Isah da Alaramma Adam Muhammad, Kwaya kusar, Borno

91-Mal. Abba Musa da Alaramma Aminu Ibrahim Potiskum, Maiduguri, Borno

92-Shk. Muhammad Abubakar Kachalla da Alaramma Ahmad Isma’il, Maiduguri Borno

93-Mal. Zainu Usman Baban Tine, NNPC Kaduna

94-Prof. Ahmad Jafar Abdulmalik da Alaramma Tajuddeen Muhammad, Masallacin Jumaa na Sheikh Jaafar U/Dosa, Kaduna

95-Imam Saidu haruna Kankiya, Masallacin Jumaa na Kabala Costing, Kaduna

96-Ustaz Nura Mujahid da Alaramma Sulaiman Musa, Masallacin Jumaa na kwaru, Kaduna

97-Dr. Tukur Adam Almannar, Masallacin Juma'a na Almannar, Kaduna

98-Imam Ishaq Ibrahim da Alaramma usman Yusuf, Sa'ad Bin Abi Waqqas hayin banki, Kaduna

99-Mal. Abubakar Buba Luwa da Alaramma Abubakar Muhammad Rabiu, Sheikh Abubakar Muh'd Gumi Jumaat Masjid Kawo, Kaduna

100 Alkali Tahir Lawal Abubakar.

KU SHIGA WANNAN LINK DOMIN GANIN SAURAN SUNAN MALAMAI NA NAIJERIYA DA KASASHEN AFURKA.

https://jibwisnigeria.org/Tafseer/Applications.html

Domin karin bayani game da shiga website din jibwis ku tuntubi wadannan lambobi.
08025178750
08061330072

Sanarwa daga ofishin sakataren JIBWIS na kasa, Sheikh Dr. Kabiru Gombe, ta ofishin shugaban JIBWIS Social Media na kasa, Alhaji Ibrahim Baba Suleiman.

Jibwis Nigeria Social Media

06/04/2021

SADAQA , CIYARWA DA KYAUTATAWA AL-UMMA SU NA YAYE DAMUWA DA KUNCI.

Ya mu 'yan uwa Musulmai masu Albarka. Muyi Amfani da wannan Damar domin Allah ya Yaye Mana Dukkan Damuwoyin mu, mu samu kyakykyawar Rayuwa Mai Albarka.

Musamman ma a wannan watan dake tafe Mai cike da Albarka (Ramadan)

Allah ya bawa kowa Damar da zai iya bada Sadaqa ko ya ciyar koda da Dan Dabino ne.

05/04/2021

LADUBBA GUDA SHABIYAR LOKACIN ADDU'A:

1. Yin imani DA kuma yarda Allah yana amsa kiran bawansa kuma yabiya masa bukatunsa, DA kuma yiwa Allah biyayya DA barin Saba masa.

2. Yin ikhlasi, wato kada karoki kowa sai Allah shikadai a lokacin addu'arka DA kuma sauran ibadu gaba daya.

3. Yin roqon Allah DA sunayensa madaukaka.

4. Ya Fara DA yabon Allah DA girmamashi DA yiwa Allah kirari, sannan yaroki abinda yake bukata.

5. Sannan yayi salati ga annabi s.a.w saboda duk addu'ar DA babu salatin annabi s.a.w acikinta, ba'a bude Mata kofofin SAMA.

6. Fuskantar alqibla a lokacin yin addu'a.

7. Daga hannaye a lokacin yin addua.

Tambihi: Hadisin dayake bayani akan shafar fuska bayan angama addu'ah baitabbata daga annabiba s.a.w duba silsilatu da'ifa Albany.

8. Yaroki DA tafukan hannayensa cikinsu yana kallon SAMA.

9. Yarika yakini akan Allah yana amsa addu'arsa.

10. Yawaita rokon Allah akowane lokaci DA rashinyin gaggawa acikin addu'a.

11. Halarto DA hankalinka acikin addu'a DA kuma yin azama wajan rokon Allah.

12. Yin kwadayi DA fargaba DA qanqan dakai ga Allah alokacin yin addu'a.

13. Maimaita addu'a sau ukku a lokacin yinta.

14. Nisantar cin haramun DA kokarin Dora rayuwa a cin halas.

15. Boye sauti a lokacin yin addu'a sirrice tsakanin bawa DA mahaliccinsa.

Tambihi: idan bawa zairoki Allah anaso ya halarto DA abubuwa guda shida aransa:
-Allah ne kadai ake roko
-Shikadai yake biyan bukata
-Shikadaine mawadaci, kowa faqirine awajansa ake nema
-Idan ya hanaka babu maibaka
-Yanada ikon baka
-Rokonsa dolene.

Allah kasanyamu cikin bayinka masu yimaka da'a kuma ka amsa mana addu'o'inmu.

02/04/2021

FALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA.

1. Yawan zikri yana korar sheɗan
2. Yawan zikri yana jawo samun yardar Allah
3. Yawan zikri yana gusar da damuwa da baƙin ciki daga zuciya
4. Yawan zikiri yana jawo farin ciki da annushuwa da nasaɗi a zuciya
5. Yawan zikiri yana ƙarfafa zuciya da jiki.
5. Yawan zikiri yana haskaka fuska da zuciya
7. Yawan zikri yana jawo arziki
8. Yawan zikri yana jawo samun kwarjini da jin dadi da farin jini
9. Yawan yana jawo samun ƙaunar Allah ta'ala, samun ƙaunar Allah shine babban buri.
10. Yawan zikri yana jawo kusanci da Allah, har a wayi gari mutum ya samu matsayin ihsani.
11. Yawan zikri yana jawo komawa zuwa ga Allah ta'ala, cikin farin ciki
12. Yawan zikri yana buɗewa mutum kofa ta samun yarda, da kusanci (Alƙurbiyya) tsakanin sa da Allah ta'ala.
13.. Yawan zikri yana buɗewa mai yinsa babun ilmi, duk sanda ya yawaita ambaton Allah, zai ƙara sanin Allah ta'ala.
14. Yawan zikri yana buɗewa mutum matsayin ganin buwayar Allah ta'ala, da isar sa.
15. Yawan zikri zai sa Allah ya ambaci mai yawan yi, duk sanda ya Ambani Allah, shima zai ambace shi.
16. Yawan zikri yana raya zuciya domin zikri ga zuciya kamar kifi ne a cikin ruwa, yaya kifi yake kasancewa idan aka raba shi da ruwa? Haka mutum zai kasance idan baya ambaton Allah ta'ala.
17. Yawan ambaton Allah yana zama kamar abinci ga zuciya da rai.
18. Yawan zikri yana washe zuciya ya goge tsatsa daga cikin zuciya.
19. Yawan zikri yana kankare zunubi
20. Yawan zikri yana kare mutum daga ɗimuwa da gafala.
21. Yawan zikri idan yana tuna Allah a cikin yalwa da wadata , Allah zai fidda shi daga cikin halin tsanani.
22. Yawan zikri yana tsaratarwa daga saukar azaba.
23. Yawan zikri yana jawo saukar nutsuwa da saukar rahma, da lulluɓewar Mala'iku,
24. Yawan zikri yana shagaltar da harshe ga barin giba da gulma da ƙarya Annamimanci, da ashariya.
25. Majalisin da ake zikri, sheɗan baya zama a wajan
Albarka tana sauka a Majalisin da ake zikiri.
26. Yin zikri yana kare mutum daga hasarar lokaci, da tashi da warin mushen jaki daga majalisi.
27. Duk wanda ya ambaci Allah a ɓoye, har ya yi hawaye don ganin girman Allah, zai shiga inuwar al'arshi ranar Alƙiyama.
28. Idan yawan zikri ya ɗaukewa mutum hankali, har ya zama baya rokon wata bukata, Allah zai bashi fiye da dukkan masu roƙo s**a roƙa.
29. Zikri shine mafi saukin ibada mara wahala kuma ga yawan lada.
30. Daga cikin falalar zikiri, yana jawo a dasawa mutum bishiya a gidan Aljanna, kamar yadda yazo a hadisi, Duk wanda ya ce Subhanallahil azeem wa bihamdihi.
31. Daga cikin falalar zikri, Kalmomi guda biyu masu saukin faɗa akan harshe masu nauyi akan sikeli, abin ƙauna a wajan Allah, Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azeem.
32. Dawwama a cikin zikiri yana ƙare mutum daga taɓewa.
33. Zikri yana zama a kowane hali, babu sharaɗin sai da Alwala ko tsarki.
34. Yawan zikri haske ne, a duniya da ƙabari da makoma da siraɗi.
35. Yawan ambaton Allah shine tushen komai, idan ka sami arziƙin yawan sa ka gama sumun dukkan komai daga Allah.
36. Zikri yana kusanta abinda yake nesa, na buƙatu kuma yana nisanta abinda yake kusa, na damuwa da baƙin ciki.
37. Zikri yana tashin zuciya daga baccin gafala.
38. Yawan zikri yana jawo samun ɗanɗano mai faranta rai.
39. Mai yawan ambaton Allah, kada ka damu domin Allah yana tare da kai.
40. Yawan zikri yayi daidai da fita yaƙi da ciwar da dukiya mai yawa.
41.. Ambaton Allah shine tushen nuna godiya ga Allah, domin duk wanda baya zikri baya godiya.
42. Zikri yana jawo samun ni'ima daga Allah kuma yana tunkuɗe Sakar fushin Allah. Mafi darajar mutane a wajan Allah shine wanda harshen sa ya zamo ɗanye a wajan ambaton Allah ta'ala.
43. Allah ta'ala da Mala'ikun sa suna yin salati ga mai yawan ambaton Allah.
44. Yin zikri shine Asalin samun soyayyar Allah da tsira daga faɗawa cikin maƙiya Allah ta'ala.
45. Yawan zikri yana jawo a sami katon dausayi a cikin aljanna.
46. Majalisin zikri wajan zaman Mala'ikun Allah ne.
47. Dukkan ibadu da Allah ya yi umarni a yi babbar Manufar su shine yawan ambaton Allah.
48. Dukkan ibadar da ake ambaton Allah da yawa a ciknsa tafi dukkan sauran ibadu kamar sallah bayan Tauhidi.
49. Yin zikri yana tsayawa a matsayin Sadaƙa da Aiyukan lada da ake yi da dukiya.
50. Ambaton Allah yana ƙara ƙarfin imani.
51. Yawan zikri yana sauƙaƙewa mutum duk wani abu mai wahala.
52. Yawan zikri yana jawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
53. Zirki yana zama kariya daga sharrin magauta da maƙiya, musamman zikirin safe da yamma, da lokacin bacci.
54. Yawan zikri yana ƙare mutun daga munafunci domin munafukai basa ambaton Allah da yawa.

Misalin zikri,لااله الاالله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير
duk wanda ya karanta wannan zikri ƙafa 100, da safe zai sami abubuwa guda biyar:
Kamar ya ƴanta bayi goma, sai lada 100, za a kankare masa zunubi 100, zai zame masa tsari daga sheɗan a wannan rana har zuwa yamma, babu kuma wanda yazo da wani abu da yafi nasa a wannan rana. Bukhari da Muslim.

Address

Jos
JOS

Telephone

+2348122904722

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis social media nape yalwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis social media nape yalwa:

Share