29/12/2025
*🤝𝘽𝘼𝙍𝙆𝘼𝙉𝙈𝙐 𝘿𝘼 𝙎𝘼𝙁𝙄𝙔𝘼🤝*
Hakuri wani babban hali ne da ya kunshi juriya, natsuwa da kuma fahimta a cikin dukkan al'amuran rayuwa. Duk wanda Allah Ya azurta da karfin hakuri, to hakika an bashi wani babban arziki da ba kowa ke da sa'a ya samu ba. Hakuri shi ne ke hana mutum aikata kuskure a lokacin fushi, shi ne ke hana yanke kauna a lokacin tsanani, shi ne kuma ke tabbatar da cikar buri a cikin lokaci.