07/04/2026
TIJJANIYA FACEBOOK CONNECT JIBIA...
Wannan kyakkyawan yunƙuri ne don sada zumunci da kuma ƙarfafa shi tsakanin 'yan uwa mabiya ɗariƙar Maulanmu Sheikh Abul Abbas (RTA) da Khalifansa Sahibul Faidha Gausul Waqati Sheikh Ibrahim Nyass (RTA).
Wannan taro yana da manufofin da yake so ya cimmawa, duk da ba zai yiwu a iya rubuce su ba. Amma ga kaɗan daga cikinsu:
1. Ƙarfafa zumunci da faɗaɗa sanayyar juna
2. Zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya a matsayinmu na mabiya hanya guda
3. Bayyanar da haƙiƙanin sufanci
4. Wayar da kai a ɓangarorin rayuwa
5. Ilimantarwa da zaburarwa a sauƙaƙe cikin hikima
In sha Allah a wannan taro za a gabatar da maƙalolin da za su shafi ɓangarori kamar haka:
1. Sufanci
2. Ilimi
3. Kasuwanci da dogaro da kai
Da zarar kwamitin shiryawa ya tantance ainihin maƙalolin, za a sanar da 'yan uwa.
Za a gayyaci masana, da ƙwararru na cikin gida da na waje da shehanai da muƙaddamai domin rayar da farfajiyar taron.
Za mu sada zumunci, mu ci, mu sha, mu yi zikiri.
Domin Tuntuɓa: 0813 4348734, 09026591915, 08035033492