Shekh Imam Bashir Jega

Shekh Imam Bashir Jega The Official Page Of Shekh Imam Bashir Jega, Jumu,ah Mosque Birin Yari.
002

Maulidi ba Addini baneAna Hada Maza da Mata Suyi Yadda s**aga dama Ana bada labaran karya wurin Maulidi Ana daga darajja...
17/08/2026

Maulidi ba Addini bane

Ana Hada Maza da Mata Suyi Yadda s**aga dama
Ana bada labaran karya wurin Maulidi
Ana daga darajjar Shehunnai Sufaye Fiye da Darajjar Annabi Muhammad S A W

A Musulunci Babu wani Wata da Ake Ke6ewa da sunan Maulidi 👌

Duk Ahlis sunnah Baya Maulidi kuma Bazai Yarda da Maulidi bah🤞

18/06/2026

KWADAITARWA AKAN YIN SALLAR NAFILA CIKIN DARE(QIYAMUL LAIL)🌘🌘

1-Annabi S.A.W yace:
(Mafi alkhairi da falalar Sallah bayan sallar Farillah,itace Sallar nafilar cikin Dare).
@رواه مسلم (1163).

2-Manzon Allah S.A.W yace:
(Inayi maku wasiyya akan kuyi riko da Sallar cikin dare,domin Dabi’ar mutanan kirkice ta wadanda s**a zo kafinku,Kuma tana kusantar da ku zuwa ga Ubangijinku,kuma kankarar zunubaice agareku,kuma tana goge laifuka).
@حسنه الألباني في إرواء الغليل (452)

2-Annabi S.A.W yana cewa:
(Lallai acikin aljanna akwai wani kataferan Bene,ana ganin cikinsa daga waje,kuma ana ganin wajansa daga cikinsa,)sai wani Balaraban Kauye yace:
“Na wanene ya Manzon Allah??” Sai yace:
(Na wanda yake:
-Kyautata magana
-Yake ciyar da abinci dan Allah
-Kuma yake azumin Nafila
-kuma ya tashi yake sallar dare lokacin da mutane suke barci).
@حسنه الألباني في صحيح الترمذي

TAYAR DA IYALI DAN YIN SALLAR DARE TARE YANA DA LADA MAI GIRMA

1-Daga Hindu Bintul Haris daga Ummu Salmata R.A Matar Annabi S.A.W tace:
“Wata rana Annabi S.A.W ya tashi cikin firgici acikin dare yana cewa:
•سُبحانَ اللهِ
SUBHANALLAH
Wani Abune Allah ya saukar na Taskoki,wani abune Allah ya saukar na Fitina Wazai Tayar min da iyalina koda zasuyi Sallar nafila acikin dare,sau da dama mai tufafi anan duniya zai tashi marar tufafi a lahira).
#صحيح البخاري ( ٧٠٦٩ ) ].

2-Annabi S.A.W yana cewa:
(Allah ya jikan bawan da ya tashi cikin dare sannan ya tayar da matarsa dan suyi Sallah acikin dare,idan taki tashi sai ya sanya mata ruwa a fuskarta dan ta tashi,kuma Allah ya jikan matar da ta tashi cikin dare sannan ta tayar da mijinta dan suyi Sallah acikin dare,idan yaki tashi sai ta sanya masa ruwa a fuskarsa dan ya tashi)
@صححه الألباني في
[📚 صحيح الجامع ( ٣٤٩٤ ) ].

3- 2-Annabi S.A.W yana cewa:
(Idan Namiji ya tashi cikin dare,sannan ya tada matarsa s**ayi Sallar raka’a biyu na nafila acikin dare,za’a rubuta su cikin bayin Allah masu ambaton Allah mai yawa).
@صححه الألباني في صحيح ابن ماجة ( ١١٠٦ ) ].

Al'mujahidu Imerm bashir jega

27/05/2026

Address

Birnin Yari Jega
Jega

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shekh Imam Bashir Jega posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category