17/12/2025
AURE KO ZINA
(KASHI NA SHA BAKWAI {17})
Wani lokaci abinda dake hana yan mata yanzu samu aure da wuri sona ki zabi Allaah ne sai Allaah ya bari su da dabaran su.
Zaka samu budurwa tana addu'a Allaah yakawo mata miji nagari mai addini, ananan sai Allaah ya turo wani yace yana sonta abin mamaki sai kaga tace wanna bai cika sharudan ta ba, kila wanda yazo wajen ta baki ne ita kuma fari take so, ko kuma fari ne ita kuma baki take so, ko kuma dogo ne ita kuma gajere take so, ko kuma gajere ne ita kuma dogo take so, bazatayi lakari da sharuda da shawrwari da shari'a ta baya ba kai bazatayi tuna kila addu'an da tayi ne Allaah ya karba ya turo mata wanna ba sai ta yanke hukunci da kanta batare da sake kumawa da mayar da alamarin ga Allaah ba tayi sallatul isitkhara ba, kawai son zuciya da son ran ta zatabi koda wanda yazo nima auren ta ya cika kaidoji na shari'a bazatayi laakari da wanna ba, daga karshe wanna ya kuci mata ta dawo tana da na sani wanda ba tada amfani.
Wani lokaci akwai abinda k**e so amma ba alheri bani, akwai abinda k**e ki amma alheri ne gare ki mayar da alamari ga Allaah da kuma nima zabinsa shine mafita.
Allaah Wanda ya Daukaka yace: ﴿
﴿ وَعَسَى أَنْ تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَكُمْ وَعَسَى أَنْ تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ ﴾ [البقرة: 216].
Su da dama kuna ki abu a hali kuma alheri ne gare ku, su da dama kuna so abu a hali shari ne gari ku, (ba alheri bani) Allaah shine masani abinda yadace da ku, ku baku sani ba.
Don haka mafita gare ki yan uwa shine mayarda alamari ga Allaah koda wani lokaci saana nima shawara amitatun mutane kirki masu tsoron Allaah shine mafita.
Kidaina yi gaugawa wajen yanke hukunci ba tare da yin isitkhara na muslunci wanda Annabi sallaahu alayhim wassalam ya karanta da sahaban sa ba, saana nima shawara amintatu masana shari'a. Allaah madaukakin Sarki ya zaba mana mafi alheri.
Muslim Islam Z Alhassan
Ku kasance tare da mu a shafuka mu na sada zumuta
Facebook
https://www.facebook.com/share/1ABe6eUMg5/
Ko
https://www.facebook.com/share/182tgfjQta/
WhatsApp
https://chat.whatsapp.com/IpQ4f3ncVPB7XFWQh0BBts?mode=hqrt2
Telegram
https://t.me/dobecauseofAllaah