MATA MUMINAI

MATA MUMINAI Wannan shafi mun buɗe shine don ilimantarwa da ainihin fadakarwa musamman abubuwan da s**a shafi mata

02/06/2023

❤️video full HD👇

06/04/2023

Allah ka sada mu da rahamar ka, a duk in da take, mu ma kuma duk in da muke Allah kabar mu da rahamar ka.

06/04/2023

Rashin Uslubi a Da'awa

Cikin kwanakin nan wani Malami ya ce: ba ya bukatar taimakon Annabi (saw). Ma'ana; ba zai nemi taimakon Annabi (saw) ba, saboda ba a neman taimakon kowa sai Allah, kuma saboda Annabi (saw) ya rasu, neman taimako a wajen mamaci kuwa shirka ne.

To wannan ya sa 'yan bidi'a s**a dira s**a yi caaaa a kansa, suna zagi, da haukatarwa, da kafirtawa da sauransu.

Ta daya bangaren kuma, sai ga wasu cikin Ahlus Sunna sun fito suna s**arsa da cewa; ba shi da Uslubi mai kyau na Da'awa.

To ni kuma ba zan tsaya ina gani 'yan bidi'a sun yi caaa a kan malami Ahlus Sunna, don ya tabbatar da Tauhidi - a maimakon na taimake shi wajen tabbatar da wannar mas'ala ta Tauhidi - sai na tsaya cin gyaransa a kan Uslubi ba. Ni a ganina; cin gyaransa a kan Uslubi a wannan lokaci, a cikin wannan yanayi, ta wannar hanya shi ne asalin rashin Uslubi mafi girma.

Ni a ganina yanzu yakin kare Tauhidi da Akidar Sunna ne ya same mu, dole sai mu tsaya mu tinkare shi, idan an gama kare Tauhidi ma yi gyaran Uslubi wa malamin, ko mu bi wata hanyar da ta dace don yi masa gyaran Uslubin, ba mu fito Facebook muna s**arsa da cewa ba shi da Uslubi ba.

Duk da cewa akwai zargin cewa; wasu masu gyaran Uslubin suna yi ne don saboda malamin yana bata wa mutane rai, idan yana raddi wa malamai Ahlus Sunna. To ka ga duk wanda ya yi don wannan to shi akwai boyayyen ta'assubanci a cikin lamarinsa.

Idan 'yan bidi'a s**a sako Tauhidi da Sunna a gaba, Ahlus Sunna mantawa suke yi da sabanin tsakaninsu, su tsaya kare Sunna, daga baya idan an gama sai a dawo kan gyaran Uslubin. Kamar yadda idan Arna ko Zindikai s**a taba Addini duka Musulmai haduwa suke yi su kare Addini, a lokacin ajiye sabanin tsakani ake yi. Kamar yadda Musulmai s**a hadu don yakar zindikancin Abduljabbar, duk da girman sabanin da ke tsakaninsu.

✍️ Aliyu Muh'd Sani

06/04/2023

A wannan watan na Ramadan wata ne wanda ya dace ga dukkan musulmi ya tsayu sosai mu gyara halayen mu, mu kuma gyara kurakuren mu, mu tsayu sosai mu nemi gafarar ubangiji a kan taɓargazar da muka yi a baya mu yi nadama a kan abunda muka yi na kuskure, tun da yanzu muna watan karɓan tuba.

Yana da kyau kuma mu dage da halartan majalisan karatu sosai. Allah yasa mu dace

05/04/2023

Shin da Gaske Wani Malami a Bauchi ya yi Irin Abin da Abduljabbar ya yi?

Dazu na ga wani faifan bidiyo, na Baba Impossible, tsohon kwamishinan harkokin Addini a jihar Kano yana nuna cewa; -wai- an samu wani malami a Bauchi ya yi irin abin da Abduljabbar ya yi na cin mutuncin Annabi (saw).

To a bisa hakika idan ka saurari maganar malamin da yake nufin sai ka ga akwai zalunci mai girma idan aka kwatanta shi da Abduljabbar.

Abin da wancan malami ya ce shi ne; ba ya bukatar taimakon Annabi (saw), bisa ma'anar cewa; bai halasta a nemi taimakon Annabi (saw) bayan rasuwarsa ba. Saboda neman taimako a wajen mamaci shirka ne.

Saboda haka abin da malamin ya yi shi ne; FANA'I, wato FANA'I a nufar Allah shi kadai, ban da waninsa. Wato:
الفناء عن إرادة السوى

Wannan shi ne FANA'IN Ahlus Sunna Wahabiyawa, wato ba sa neman taimako a wajen kowa sai Allah, b***e abin da babu mai iko a kansa sai Allah. Wannan ya sa ba sa neman taimako a wajen mamaci, ko da Annabin Allah ne, saboda hakan shirka ne ma Allah.

Saboda haka malamin da ake nufi, ba shi da alaka da irin abin da Abduljabbar ya yi na zagin Annabi (saw). Saboda Akida ce ta Muslunci, a cikin Alkur'ani da Sunna, Akidar Annabi (saw) da Sahabbansa; ba a neman taimako a wajen kowa sai Allah. Allah ya ce:
{إياك نعبد وإياك نستعين}.

{Kai kadai muke bautawa, kuma a wajenka kadai muke neman taimako}.

Annabi (saw) ya ce:
[وإذا استعنت فاستعن بالله].

[Idan za ka nemi taimako KA NEMI TAIMAKON ALLAH].

Saboda haka Akidar Muslunci shi ne kada a nemi taimakon Annabi (saw), ko da a abin da mutum yake da iko a kansa ne, saboda Annabi (saw) ya rasu, neman taimako a wajen mamaci kuwa shirka ne ma Allah Madaukakin Sarki.

Don haka zargin da Baba Impossible ya yi ba dadai ba ne.

Aliyu Muh'd Sani

05/04/2023

DAUKAN MATSAKAICIYAR RAYUWA DA NISANTAR KARYA DA FARIYA NADA TASIRI SOSAI WURIN KAMEWAR BAWA DAGA AFKAWA HARAMUN DA KAMIYA-MIYA.

31/03/2023

Kalmar azumi tana ɗaukar ma'anar kiyaye gaɓɓai ba zaka saɓa ma Allah da su ba, wannan shi ma ana kiran shi azumi. Idan muka lura da wannan zamu gane ashe ba wai azumi shi ne kawai barin ci da sha ba.

A'a, a na so mutum ya rage yawan surutai marasa fa'ida, kuma ya nisanci saɓon Allah, amma kuskurene abun da waɗansu matasa da ƴan mata suma suke yi a yau.

Kai har ma da matan aure sai ka ganta ta shige ƙuryar ɗaki ta ɗauko littafan soyayya ta jibge su a gaban ta, tana ta faman karantawa daga ta sauke wannan sai wannan, kawai wai wannan karatun yana sawa bata jin azumi.

Kai ka ji irin wannan shashanci dan Allah, memakon ke da zaki ɗauki Alƙur'ani ki karanta wanda za ki samu lada kuma a kankare miki zunubi, amma kin ɗauki wannan littafan na ƙarya wanda za su iya ma ɓata miki azumi ko kuma ma suja a baki zunubi.

✍️ Jameel A Kabo (Abu Zulaikha)

Address

Jalingo

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MATA MUMINAI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share