Jibwis Hadejia

Jibwis Hadejia Shafin kungiyar izala ta karamar hukumar Hadejia, don yada da'awah, karantarwa sanarwa sada zumunci da yayata ayyukan wannan kungiya.

28/05/2026
24/05/2026

🕌🕌SADAƘAR FATUN LAYYAH🕌🕌

Ƙungiyar Izalah ta karamar hukumar Haɗejia ƙarƙashin Jagorancin Shugaba Sheikh Mu'az Idris Mua'az, ta kafa kwmt dazai tabbatar da nasarar tara sadakar fatun Layya, Ga kungiyar kamar yadda muka saba Zama Zakara a Duk Shekara.

Kwamatin ƙarƙashin Jagorancin sakatare na wannan ƙungiya Malam Aminu Hassan Hadejia. Na miƙa gdy ga dukkan Musulmai dake bawa wannan aiki gudummawa a kowace Shekara. Mussmman fadar maimartaba Sarkin Haɗejia Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON, Saboda gagaumar gudummawar su.

A bana an tsara ayyukan karɓar fatun kamar haka:

1- Dukkan Majalisai da Masallatan mu su tabbatar da karbar fata da kuma kula da sa mata gishiri kafin karɓa.

2- ƴan agaji masu kayan Sarki kaɗai aka yarda a bawa Fatu da aka tara a Majalisai da Masallatai.

3- Majalisai dake Lunguna su taimaka su kawo fatun su bakin T**i don saukin ɗauka.

4- Ana iya kawo Fata da ƙirgi kai tsaye a Babbar cibiyar Tattara fatu dake Babban Masallacin Izalah Unguwar Matsaro,Haɗejia.

5- A kula da masu Fiɗa saboda gudun asarar fatu kamar yadda aka samu hakan a bara. A samu wanda S**a iya kuma asa gishiri.

6- Akwai Risitai na gudummar Kuɗi musamman ga wanda basu samu yin layya ba. Akwai ₦100.₦500. Sai a kawo masallatai dake kusa.

Zaa iya tuntuɓar waɗannan Lambobi don karɓar Fatun Kamar haka:

07032669478
08138297994
08066001913
08063157445
07036122995
08033897966.

✒️✒️✒️✒️✒️
Abu-Humairaa
Jibwis Haɗejia
24/05/2026

LOKUTAN SALLAR IDI BABBA !      Jibwis Hadejia 1447Ana sanarda Jamaar Musulmai na Hadejia da Kewaye, in Allah ya kaimu R...
24/05/2026

LOKUTAN SALLAR IDI BABBA !
Jibwis Hadejia 1447

Ana sanarda Jamaar Musulmai na Hadejia da Kewaye, in Allah ya kaimu Ranar Laraba 27/05/2026....Zaa tayar da Sallar idi kamar haka;

1- Masallacin NTA -
Sheikh Isah Abdullahi
Karfe 7:30 na Safe.

2- Masallacin Hadejia/Jamaare-
Sheikh Mu'az Idris Mu'az
Karfe 8:00 na Safe.

Allah ya amsa mana 🙏

✍️ Jibwis Hadejia.

*SANARWAR FARA TAFSIR*A madadin Shugabannin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa ikamatis Sunnah (Jibwis) Reshen Karamar...
18/02/2026

*SANARWAR FARA TAFSIR*

A madadin Shugabannin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa ikamatis Sunnah (Jibwis) Reshen Karamar Hukumar Hadejia, Jihar Jigawa.

Muna farin Shaidawa 'Yan Uwa cewar, Babban Malamin mu Kuma Shugaban Kungiya Sheikh Mu'az Idris Mu'az zai Fara Gabatar da Tafsiri, a Yau Laraba 1 ga Ramadhan 1447. A Babban Masallacin Jibwis Matsaro tare da Alaramma Muhammad Sani. Daga Karfe 9 na dare Zuwa karfe 10. Inshaa Allah (Kafin Zuwan Malamin da zaa Turo daga Uwar Kungiya ta kasa, Kamar Kowace Shekarar).

Allah ya bada Ikon Halarta ya Kuma Amsa Daga Garemu🙏

✍️ *Jibwis Hadejia*

Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun! A madadin Shugabannin wannan Kungiya na Karamar Hukumar Hadejia, karkashin Jagorancin...
21/01/2026

Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun!

A madadin Shugabannin wannan Kungiya na Karamar Hukumar Hadejia, karkashin Jagorancin Sheikh Mu'azu Idris Muaz Muna meka sakon Taaziyyar mu ga Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da Dukkan 'yan uwa da Iyalai da Al'ummar Musulmai...Kan Rasuwar Babban Malamin mu Sheikh Habibu Kaura Wanda Allah yaiwa Rasuwa a Yau Laraba 21/01/2026.

Allah ya Jikan Malam ya yafe kusakurai ya bashi Aljannah, ya bamu hakuri jure wannan Rashida.

✍️ Usman Muhd Isma'il
Jibwis Social media
Chairman Hadejia.

31/08/2025

Address

Hadejia
Hadejia
HJA

Telephone

+2348033897966

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Hadejia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis Hadejia:

Share