Jibwis Gwarzo 01

Jibwis Gwarzo 01 An bude wannan page ne domin yada da'awar Sunnah

Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji‘ūnShugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Ƙasa, Sheik...
21/01/2026

Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji‘ūn

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Ƙasa, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau,
yana sanar da dukkan ‘yan uwa Musulmi da mambobin Kungiyar JIBWIS rasuwar:

Sheikh Habibu Yahaya Kaura
Shugaban Working Committee na Kungiyar JIBWIS ta Ƙasa, wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya karɓi rayuwarshi bayan jinya da yayi fama da ita.

Za a gabatar da Sallar Jana’iza da misalin karfe 4:30 na yamma, a Hedikwatar Kungiyar JIBWIS,
Utako Bega Junction, Abuja.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, kuma Ya ba iyalansa, ‘yan uwa da al’ummar Musulmi haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

JIBWIS GWARZO

Sanarwa Ga Jama'a13/12/2025.Za'a Gudanar Da Seminar Ta Jihar Kano Ta 'Yan Agaji Sama Da Mutum Dubu Goma (10,000)Sakamako...
13/12/2025

Sanarwa Ga Jama'a
13/12/2025.

Za'a Gudanar Da Seminar Ta Jihar Kano Ta 'Yan Agaji Sama Da Mutum Dubu Goma (10,000)

Sakamakon Bayan Taron Majalisar Zartarwar Agajin Izalar Jihar Kano Karkashin Jagorancin Daraktan Agajin Izala Na Jihar Kano Malam Mukhtar Lawan Tudun An Zartar Da Cewa Za'a Gabatar Da Seminar Ta Jihar Kano Insha Allah A Ranar Juma'a 02/01/2026 Zuwa Ranar Lahadi 04/02/2026 A Jihar Kano.

Darakta Tudun Wada Yayi Kira Ga Yan Agaji Da Su Dukufa Wajen Cigaba Da Shirye-Shiryen Gudanar Da Taron Seminar.

Sa Hannu:
DSP A. Bello
Babban Jami'i,
Sashen Yaɗa Labarai Da Hulɗa Da Jama’a Na
Majalisar Agajin Izala Ta Jihar Kano.

Congratulations Congratulations a Madadin Jibwis Gwarzo L.G Muna Taya Daya Daga Cikin Malaman muMal Abubakar KayyuWanda ...
01/12/2025

Congratulations Congratulations

a Madadin Jibwis Gwarzo L.G
Muna Taya Daya Daga Cikin Malaman mu
Mal Abubakar Kayyu

Wanda Ya zama Doctor of Philosophy
Dr Abubakar Kayyu Daga Jami'ar Bayero University Kano
Muna Rokon Allah Yasa Albarka Amin

InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un!A madadin kungiyar Izala, Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na miƙa ta'aziy...
13/07/2025

InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un!

A madadin kungiyar Izala, Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na miƙa ta'aziyya ga ƴan uwa da iyalai, da sauran yan uwa na garin Daura dana jahar Katsina dama ƙasa baki ɗaya, bisa rasuwar Tsohon shugaban kasar Nijeriya wanda Allah ya ƙarɓi rayuwarsa a birnin Landan na ƙasar Ingila yana da shekaru 83 bayan fama da jinya. "Mutuwa Rigar kowa!!

Allah ka jiƙan Muhammadu Buhari ka kyautata makwancin sa, ka haɗamu da shi a gidan aljanna firdausi ranar gobe. Allah ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kura-kuransa, Ka sanya Aljannah ce makomar sa, Ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana, tare da sauran Musulmai Muminai. Ameen

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Shugaban JIBWIS Nigeria.

Jibwis Nigeria

MALLAM LAWAN TRIUMPH, GASKIYA DAYA CE: ABINDA YA FARU YAU A SHARI'A COMMISSION TA JIHAR KANO...An samu wasu gungun mutan...
10/07/2025

MALLAM LAWAN TRIUMPH, GASKIYA DAYA CE: ABINDA YA FARU YAU A SHARI'A COMMISSION TA JIHAR KANO...

An samu wasu gungun mutane masu son tayar da hankalin al'umma, masu son nemawa Abduljabbar abokin mutuwa ta ko wane irin hali, s**a ta shi s**a tafi Shari'a Commission su ka kai korafi akan kazafi, sharri, da juya maganar da s**a yi wa Sheikh Lawan Abubakar Triumph. Kuma a karon farko Shari'a Commission ya dauki zafi akan lamarin bisa irin korafe-korafen da aka shigar mata. Wanda hakan ya sa su ka gayyaci Mallam din.

Bayan isar su Sheikh Lawan Triumph a wajen, an so a fara yin maganganu, sai Mallam Lawan Ya ce: "Kafin a yi nisa a cikin bayani, shin an saurari ainahin maganganun da ake magana a kansu?" Aka ce ba'a saurara ba. Sai aka ce to a kunna kowa ya ji.

Ana kunna Audio din Mallam Lawan, sai jikin kowa ya yi sanyi a wurin. Nan da nan kuma sai masu korafi s**a koma kame-kame da neman a zauna lafiya. Da alama ko dai su ma duk jita-jita su ka bi, ko kuma sun san ba haka abin yake ba, amma kawai so suke dole sai an shafa wa Mallam Lawan bakin fenti.

Bayan an kunna Audio din, sai wani jigo a Shari'a Commission, Mallam Ali Dan Abba, sau biyu yana tambaya ko akwai mai magana a cikin waɗanda s**a dauki zafi a hukumar a karon farko? Shiru, ya kuma tambaya, akwai mai tambaya ko neman karin bayani? Amma Shiru.

Kafin batun Shari'a Commission, muna da labarin an kira DSS an kai musu korafi su ma. Sannan ana cigaba da wasu kulle-kullen.

Abinda mu so ku sani shi ne:

1. A ko yaushe gaskiya ce take yin Nasara
2. Karya, sharri, kage, da kulle-kulle, ba hanya ce da za ta bulle wa magauta ba.
3. Da gaskiya mu ke yin addini, kuma da wayewa, mun fi karfin cin mutunci ko dauki dai-dai.
4. Kaunar Annabi SAW mu ke yi da gaske. Allah Ya kiyaye, da ace wani a cikinmu zai yi gangancin aikata laifin da makiya suke zargi a yanzu, da mu ne zamu fara yaƙarsa kafin kowa. Amma duk wanda za'a yi wa sharri a cikinmu, za ku kare shi da iyaka karfin da Allah Ya h**e mana, domin mu aka taba gaba.

InnalilLahi wa Inna Ilaihi Raji'un!!!Kungiyar JIBWIS tana miƙa ta'aziyyar rasuwar Marigayi Alhaji Auwal Yusuf Sambo Riga...
20/01/2025

InnalilLahi wa Inna Ilaihi Raji'un!!!

Kungiyar JIBWIS tana miƙa ta'aziyyar rasuwar Marigayi Alhaji Auwal Yusuf Sambo Rigacukun da Allah ya karɓi rayuwarsa bayan gajeruwar jinya a daren Litinin.

Shugaban JIBWIS Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau a madadin ƙungiyar, ya aike da ta'aziyyar daga ƙasa mai tsarki, a Lokacin da yake gudanar da ibadar Umrah.

Sheikh Bala Lau yace, rashin Auwal a daidai wannan lokaci ba ƙaramin rashi bane, wanda baza mu taɓa mantawa da alkhairan mamacin ba, "Muna ta'aziyya ga mahaifinsa Sheikh Muhammad Yusuf Sambo Rigacukun, da sauran ƴan uwa da iyalai, da fatan Allah ya bamu haƙurin rashin baki ɗayan mu, ya haɗa mu da shi a Aljanna Firdausi, ya bashi ikon kwanciya cikin aminci a kabarin sa. Amin.

Jibwis Nigeria

01/01/2025

Address

Gwarzo

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Gwarzo 01 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis Gwarzo 01:

Share