Al'ilmu nour foundation

Al'ilmu nour foundation *BABBAR DAMA TA SAMU*

Assalaumu'alaikum

Wannan babbar dama lura dacewa halinda muka tsinci kanmu a

22/11/2021

*WANKAN GAWA DA YADDA AKEYINSA.*

*DON ALLAH MU KARANTA KUMA MU YI SHERING ZUWA 3 GA SAURAN ƳAN UWA MUSULMAI.*

SABODA YANZU ABUN YA ZAMA MATSALA TA WANNAN AL'AMMARIN, IDAN ANYI MUTUWA SAI KAGA AN RASA MAI YIWA WANNAN GAWAR WANKA, KO
KUMA KAGA MALAMIN DA ZAIYI
WANKAN YANA TA MULKI SAI LOKACIN DAYA GA DAMA ZAI ZO YAYI WANKAN.

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI.

FALALAR WANKAN GAWA.

Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi
Wanda Manzon Allah (S.A.W)
Yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke
mamaci, kuma ya rufa masa
asiri, Allah Zai gafarta masa sau
arba’in.’’

A wani hadisin kuma Manzon Allah
(S.A.W) Yace, ”Duk wanda ya
wanke mamaci kuma ya rufa masa
asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljanna Kwarra (wato Launin Tufafin).

SHARUƊƊAN WANKAN GAWA.

Daga cikin sharaɗan wankan gawa
sune:-

1. Ana buƙatar waɗanda zasu wanke
mamacin su zamanto makusantan sa (misali, Iyaye, ƙanne, yayye, ko ƴaƴa, da sauransu).

2. Ana buƙatar maza su jiɓinci wanke maza, suma mata su jiɓinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa hakama Mace zata iya wanke Mijinta).

3. Ba sharaɗi bane lallai sai anyi
amfani da ruwan zafi ba.

YADDA AKE YIN WANKAN GAWA

Ana yin wankan gawa mara-mara ne
(misali, Sau Uku(3) ko Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9)).

Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a cikin hadisin Ummu Adiya(R.A).

Waɗanda zasu yi wa mamaci wanka su zasu yi la’akari suga wanka nawa ya dace suyi masa.

Da farko dai kafin a fara wankan
akwai abubuwa guda Uku(3) da za’a fara yi wa mamacin. Su ne kamar haka:-

1. Za’a cire masa suturar da take
jikinsa, amma za’a sami ɗan kyalle a rufe masa al’aurarsa.

2. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi masa tsarki, na ɓangaren mafita biyu wato (Bawali da Gayadi).

3. Idan macace, za’a tsefe kitsan dake kanta, a wanke kan, sannan ayi Lallaɓi uku a kan ( wato Kalba guda Uku). Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata.

Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba ɗaya.

YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)

Idan masu yiwa mamaci wanka sun

16/08/2021

Assalamu alaykum insha Allahu rabbi za a yi azumin ashura da tashura ranar talata da laraba Kada mu manta Allah ya bamu ikon yi ameen kuyi forward ga Yan uwanku Dan kowa ya samu wanan lada

06/06/2021

Assalamu'alaikum

Yan uwana dalibai yau laraba 21/10/1442h daidai da 02/06/2021 insha Allah zamu dawu da cigaba da karatuttukanmu kamaryan aka saba insha Allahu ta'ala, sanan muna bawa yan uwa hakuri najinmu shiru da akayi Muna matuka bakowa hakuri Allah ya taimakemu yasanya ikhi lasi cikin aiyukanmu

13/04/2021

RAMADAN YAZO AN DAURE SHEDAN DA RUDUNARSA MUYA FEMA JUNA KUSAKURAN JUNA A TSAKANIN MU

05/03/2021

MATA KU DAINA RUDUWA DA ‘YAN BOKO AQIDAH, WADANDA KE KOKARIN KASHE MUKU AURE !!!
Acikin kwanakin nan munci karo da vedeo na wata Mace Bagidajiya tana Kiran Mata da su hakikance wajen bude wayoyin mazajen su ko ta halin kaka, take Kira da cewar duk namijin da ya haramtawa Matarsa ganin cikin wayarsa ba abokin rayuwa bane.
Tace ita idan mijin ta bai bari ta duba wayar sa ba akwai matsala... Abu na farko a wannan gabar ta aika saƙon.
Ta bar kowacce mace da ta dauki shawarar ta cikin ruɗani na zabar kalar matsalar da zata faɗa a yunkurin binciken wayar mijin ta.
Abu na biyu ko namiji bayi da gaskiya ba inda aka ce sai kin duba wayar sa domin addini bai yarda da abunda zai kawo tashin hankali ba har ya kai ga mutuwar aure.
Karya take yi ta rasa aurenta tana Kiran ku Kuma ku kashe auren ku, ku zamto irinta.
Munga Mata da dama suna gaskata ta, toh wallahi kuyi karatun ta nutsu matukar kuka biye Mata zaku dawo zawarawa, yayanku su Zama Kara zube.
Waye yace wajibi ne sai Matar mutum tasan sirrin mijinta gaba daya ??? Me yasa addini yayi hani da zato acikin aure, me yasa addini ya ambaci kada ayi bincike a wasu wurare, saboda a zauna lafiya.
Haka kuma shi namiji yanada mu'amuloli da yawa, ba sirrin sa kawai ne a hannun sa ba, ashe kenan ba lallai ne komai na shi sai kin sani ba ta yanda zaki iya sanin sirrin wasu. Ko ma dai meye, da sanin da rashin sanin ba abund zai ƙare ki, ke dai kiyi kokari ki zauna lfy da mijin ki, domin rayuwar zawarci ba ita ce duk mai hankali ke so ba.
Toh ‘Yar-uwa Ina mai tabbatar miki idan kika sanyawa zuciyarki dole sai kin bincika wayar mijinki toh kina gab da zamowa Bazawara kamar wannan Mata da take hura Miki kunne take aika miki da sakon Shaidan, ita ma Karan kanta Shaidan ce, domin Shaidan Babban burinsa shine ya shiga tsakanin ma’aurata.
‘Yar-uwa ina Kira zuwa gare ki, ki sani cewa auren nan ibadah ne Kuma zaman hakuri Shima ibadah ne, ki tsarkake zuciyarki ki cire zato da zargi acikin rayuwar aurenki kiyi Zama da zuci

02/03/2021
26/02/2021

AL HALAL ISLAMIYA

TAHFIZUL QUR'ANI

ARABIC CLASS

Hukumar makarantar AL'ILMU NOUR FOUNDATION tasanar da rage kudaden shi makarantar daga naira  #1000 zuwa naira #500 haka...
23/02/2021

Hukumar makarantar AL'ILMU NOUR FOUNDATION tasanar da rage kudaden shi makarantar daga naira #1000 zuwa naira #500 hakan yafarune sakomakon lurada halinda al'umma sukeciki na fatara da talauci munsamu wannan sanar wane daga bakin DIRECTOR makarantar suwaiba suleiman baba; hakan yabiyobayan wata tattaunawa da sukayi da sauran malaman makarantar.

22/02/2021

Dokoki makaranta

1. Baza a saka dalibi a group din makarantaba sai yayi rigestration.

2. Ba'ayarda wani daga cikin dalibai yashigo da wani posting ba inba Wanda yashafi karatunsaba.

3. Yazama wazajibi kan kowane dalibi ya halarta karatu ranar da ake karatu.

4. Dalibi zai shigo da tambayarsa bayan ankammala karatu.

5. Malamai zasu ansa tambayoyin dalibai duk lokaci da aka gama karatu.

6. Hukumar makaranta zata iya sabunta wata daga cikin wayannan dokokin idan bukatar hakan tataso

7. Ba'ayar da wani ko wata ya dauki number wani ba yayi magana da shi ta private duk wannan akawu kararshi toh humar makaranta zata dauki matakin da ya dace akasa

8. Wajibine kan kowane dalibi ya halarci duk ni darasi wanda yafi makaranta da yake inma yanada wani uzuri ya kira malamin mai wannan da rasin ya sanar dashi.

9. Wajibine gakowane dalibi ya kayaye wayannan dokokin kuma yayi biyayya garesu.

Address

Gusau

Telephone

+2348069406466

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al'ilmu nour foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Al'ilmu nour foundation:

Share