Tigmein Gombe State Chapter

Tigmein Gombe State Chapter Wannan shafi zai dinga kawo muku duk abinda yake gudana acikin lamarin TIGMEIN a Jihar Gombe.

TIGMEIN REPRESENTED AT EFCC SCUML SENSITIZATION WORKSHOP IN GOMBEThe Tijjaniyya Grassroots and Empowerment Initiative of...
07/05/2026

TIGMEIN REPRESENTED AT EFCC SCUML SENSITIZATION WORKSHOP IN GOMBE

The Tijjaniyya Grassroots and Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMEIN), Gombe State Chapter, participated in the EFCC/SCUML Town Hall Sensitization Workshop on the Prevention of Terrorism Financing and Abuse of Non-Profit Organizations held on Tuesday, May 5, 2026, in Gombe State.

Representing TIGMEIN at the important capacity-building programme was the Director of Entrepreneurship and Empowerment, Mallam Abdullateef Modibbo Tukur, who joined other stakeholders and representatives of Non-Profit Organizations from Gombe, Bauchi, and Adamawa States.

The workshop was organized by the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) through the Special Control Unit against Money Laundering (SCUML) and took place at the GOFCECOM Hotel Innex Conference Hall, Gombe.

The sensitization focused on strengthening compliance among Non-Profit Organizations, especially on issues relating to transparency, accountability, prevention of terrorism financing, and adherence to SCUML reporting obligations under Nigeria’s Anti-Money Laundering framework.

Officials of the EFCC emphasized the need for organizations to operate within the law and remain proactive in safeguarding their institutions from abuse, while participants were encouraged to extend the knowledge gained to their various organizations and communities.

TIGMEIN Gombe State Chapter appreciates the EFCC and SCUML for organizing the impactful engagement and remains committed to promoting lawful, transparent, and community-driven initiatives for sustainable development.

Media Team
TIGMEIN Gombe State Chapter

‎RAHOTON MUSAMMAN NA ZIYARAR TIGMEIN GOMBE STATE CHAPTER‎Rana: Litinin, 27 ga Afrilu, 2026‎Wuri: Anguwar Bolari ta Gabar...
27/04/2026

‎RAHOTON MUSAMMAN NA ZIYARAR TIGMEIN GOMBE STATE CHAPTER
‎Rana: Litinin, 27 ga Afrilu, 2026
‎Wuri: Anguwar Bolari ta Gabar, Jihar Gombe


‎Ƙungiyar Tijjaniyya Grassroots and Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMEIN) reshen Jihar Gombe ta kai wata muhimmiyar ziyara zuwa reshen Anguwar Bolari ta Gabar, a ci gaba da shirinta na ƙarfafa tsari, haɗin kai da bunƙasa ayyukan al’umma.

‎Ziyarar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Gudanarwa na Jiha, Mal. Bashir Modibbo Tukur, tare da rakiyar Mal. Naziru Bashir, Mal. Ahmad Tijjani, da Mal. Abbakar Sadik Adamu, inda s**a gana da mambobin ƙungiyar na yankin.

‎Babbar manufar ziyarar ita ce ƙarfafa tsarin ƙungiya daga tushe, da kuma ƙara wayar da kan mambobi kan rawar da suke takawa wajen cigaban kansu da na al’umma baki ɗaya.

‎A yayin zaman, an mayar da hankali kan muhimman fannoni kamar haka:
An fara da ƙarfafa taimakon kai da kai, inda aka jaddada buƙatar gano marayu da marasa galihu domin tallafa musu ta hanyoyi masu ma’ana. Haka kuma, an ƙarfafa kowane ɗan uwa ya yi amfani da baiwarsa wajen taimakon al’ummar da yake rayuwa a cikinta.

‎Daga nan, an yi bayani kan ginin tsari mai ƙarfi na shugabanci (Excos), inda aka bayyana yadda za a haɗa shugabanni daga matakin ƙasa har zuwa wards da anguwanni, ta hanyar kai ziyara zuwa zawiyoyi, tsangayu da makarantu domin tabbatar da haɗin kai da daidaito.

‎Haka zalika, an jaddada buƙatar kafa Board of Trustees (BOTs) a kowace anguwa domin ƙarfafa shugabanci da kula da al’amuran ƙungiya yadda ya kamata.
‎A fannin wayar da kai, an yi ƙira ga mambobi da su fahimci muhimmancin mallakar katin zaɓe, domin su iya taka rawa a harkokin zaɓe da shugabanci.
‎An kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da tsari, inda aka bayyana cewa rashin tsari na daga cikin manyan dalilan da ke janyo koma baya. Saboda haka, an ƙarfafa mambobi da su haɗa kai domin cimma manufar cigaban kansu da na al’ummar da ke biye da su.
‎Bugu da ƙari, an yi bayani kan muhimmancin tattara bayanai (data) na Tijjanawa a kowace anguwa, domin samun ingantaccen tsari da sauƙin gudanar da ayyuka.

‎A ɓangaren tsarin shugabanci, an bayyana cewa ana buƙatar mambobin Excos guda 30 a kowace anguwa, domin tabbatar da ingantaccen wakilci da gudanarwa.

‎A ƙarshe, an yi cikakken bayani kan shirin Cooperative na TIGMEIN, wanda aka tsara bisa tsarin Musulunci ba tare da ruwa ba. An ƙarfafa mambobi da su shiga wannan tsari domin bunƙasa tattalin arziƙinsu da samun tallafin juna.


‎Tigmein Alkhairi ceh!

‎Tigmein Media Team Gombe

AlhamdulillahA cikin wannan lokaci mai albarka da ake bukukuwan Sallah, ƙungiyar TIGMEIN Gombe State Chapter ta samu nas...
23/03/2026

Alhamdulillah

A cikin wannan lokaci mai albarka da ake bukukuwan Sallah, ƙungiyar TIGMEIN Gombe State Chapter ta samu nasarar rabawa yara marayu sama da 250 kayan Sallah a sassa daban-daban na jihar, musamman a:
Gombe LGA
Yamaltu Deba LGA
Shongom LGA

An rabawa yaran kayan da s**a haɗa da:
Zannuwa
Yadin Shadda
Yadin Tuyobo
Kayan kanti
Abin farin ciki shi ne, yawancin waɗannan yara marayu ne, ciki har da Almajirai, kuma mafi yawansu ƙanana ne da ba su kai shekaru 15 ba.

Muna amfani da wannan dama wajen miƙa godiya ta musamman ga dukkan waɗanda s**a bada gudummawa wajen ganin an aiwatar da wannan aiki na alheri. Musamman:
✅ TIGMEIN State Exco
✅ TIGMEIN Gombe LGA
✅ TIGMEIN Yamaltu Deba LGA
✅ TIGMEIN Shongom LGA

Haka kuma muna godewa membobi da wasu Excos na kowani yanki waɗanda s**a bada gudummawa kai tsaye, ciki har da wanda ya bada yadi guda 10, da sauran da s**a haɗa kuɗi har ₦35,000.

Sauran dukkanin abubuwan da aka yi, ƙungiyar ta samar da su ne daga ƙoƙarin ta da gudummawar membobinta.

Muna addu’a Allah Ya saka da alheri, ya ƙara arziki, ya karɓi wannan aiki a matsayin ibada.

TIGMEIN Alkhairi ceh!

Raba Kayan Sallah Ga Marayu a Zawiyyar Malam Haruna Muhammad, Shongom LGAAssalamu Alaikum warahmatullah.Ana farin cikin ...
19/03/2026

Raba Kayan Sallah Ga Marayu a Zawiyyar Malam Haruna Muhammad, Shongom LGA

Assalamu Alaikum warahmatullah.
Ana farin cikin sanar da al’umma cewa an raba kayan Sallah ga marayu a Zawiyyar Malam Haruna Muhammad da ke ƙaramar hukumar Shongom, a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar TIGMEIN, reshen Gwandum Ward.

Wannan tallafi ya shafi marayu guda 10, inda aka samar musu da kayan da za su taimaka musu wajen gudanar da ibadun Sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na kula da marasa galihu, musamman marayu, tare da ƙarfafa zumunci da jin ƙai a cikin al’umma.
Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka da alheri ga duk waɗanda s**a bayar da gudunmawa, Ya kuma ba da ikon ci gaba da irin waɗannan ayyukan alheri.

An Gudanar da Rufe Tafsir a Anguwar Nassarawo, An Raba Takalman Sallah Ga Marayu.An gudanar da taron rufe Tafsirin Alƙur...
19/03/2026

An Gudanar da Rufe Tafsir a Anguwar Nassarawo, An Raba Takalman Sallah Ga Marayu.

An gudanar da taron rufe Tafsirin Alƙur’ani Mai Girma a Anguwar Nassarawo, ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar TIGMEIN, inda Malam Hafiz Alkali Bello ya kasance mai gabatar da Tafsirin.

Taron ya gudana cikin nasara tare da halartar al’umma da dama, inda aka amfana da darussa masu zurfi daga Alƙur’ani, musamman a wannan wata mai alfarma.

A wani ɓangare na ayyukan jin ƙai da tallafa wa marasa galihu, an raba takalman sallah ga marayu, domin taimaka musu wajen gudanar da ibadunsu cikin sauƙi da kwanciyar hankali.

Masu halartar taron sun yaba da wannan kyakkyawan tsari, tare da bayyana cewa irin waɗannan ayyuka na ƙara ƙarfafa zumunci da taimakon juna a cikin al’umma.

An kuma yi addu’o’i na musamman, inda aka roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ibadun da aka gabatar, Ya saka da alheri ga waɗanda s**a ɗauki nauyin shiryawa da gudanar da wannan taro, tare da fatan a ci gaba da irin waɗannan ayyuka masu albarka.

‎TIGMEIN Jekadafari Ta Kai Ziyara Gidan Gyaran Hali na Jihar Gombe.‎‎A wani ɓangare na ayyukan jin ƙai da wayar da kai, ...
18/03/2026

‎TIGMEIN Jekadafari Ta Kai Ziyara Gidan Gyaran Hali na Jihar Gombe.

‎A wani ɓangare na ayyukan jin ƙai da wayar da kai, reshen ƙungiyar TIGMEIN na Anguwar Jekadafari a jihar Gombe ya kai ziyara zuwa gidan gyaran hali da ke fadar jihar a ranar Talata 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026.

‎Ziyarar ta samu halartar wakilai daga matakin jiha da kuma ƙaramar hukumar Gombe, inda aka gudanar da ayyuka masu muhimmanci da s**a haɗa da taimako da kuma faɗakarwa ga waɗanda ke tsare.

‎Daga cikin abubuwan da aka aiwatar; an samu damar 'yantar da mutum guda ɗaya ta hanyar biya masa tarar da ke kansa. Haka kuma, an raba kayan abinci ga mazauna gidan gyaran halin, ciki har da biredi, ruwan sha (sachet water), Maggi da sauran kayayyaki.

‎A yayin ziyarar, an gabatar da jawabai da wa’azi masu ratsa zuciya, inda aka jaddada muhimmancin gyaran hali da tsarkake zuciya, tare da jan hankali kan cewa zuciya ita ce tushen aikata kyawawan ayyuka ko kuma sabanin haka.

‎A nasu ɓangaren, jami’an gidan gyaran halin sun bayyana matuƙar godiya ga wannan ƙungiya bisa irin gudunmawar da ta bayar, tare da fatan Allah Ya saka da alheri, Ya kuma ba su ikon ci gaba da irin waɗannan ayyukan alheri.

‎Wannan ziyara na daga cikin ƙoƙarin TIGMEIN na tabbatar da kyakkyawar al’umma mai cike da tausayi, gyara, da kuma taimakon juna.


Tigmein Alkhairi ceh

‎A ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026, Alhaji Sani Nono ya bada gagarumar gudunmawa ga aikin al’umma ta hanyar ba...
21/02/2026

‎A ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026, Alhaji Sani Nono ya bada gagarumar gudunmawa ga aikin al’umma ta hanyar bai wa TIGMEIN reshen Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, Jihar Gombe roduna 12mm guda 53, domin ci gaba da gudanar da aikin gina Masallaci da reshen ke jagoranta.

‎Wannan kyauta ta zo a kan lokaci, kuma ta ƙara ƙarfafa gwiwarmu wajen ganin an kammala aikin masallacin cikin nasara, domin amfanin al’umma baki ɗaya.

‎Muna miƙa godiya ta musamman ga Alhaji Sani Nono bisa wannan karamci da jajircewa wajen tallafa wa ayyukan alheri da ci gaban addini dama al’umma.

‎Muna roƙon Allah (SWT) Ya saka masa da alkhairi, Ya ƙara masa arziki, lafiya da tsawon rai.
‎Ameen.

‎Allah Ya sanya wannan gudunmawa ta zama sadaukarwa mai gudana (Sadaqatul Jariyah) gare shi.

Tigmein Alkhairi ceh!

‎RAHOTON ZAMA NA BIYU NA TIGMEIN – KWAMITIN MANYAN MAKARANTU (GOMBE STATE)‎‎A ranar 15/02/2026, Kwamitin TIGMEIN kan Kul...
16/02/2026

‎RAHOTON ZAMA NA BIYU NA TIGMEIN – KWAMITIN MANYAN MAKARANTU (GOMBE STATE)

‎A ranar 15/02/2026, Kwamitin TIGMEIN kan Kula da Manyan Makarantu (Higher Education Coordination Unit) ya gudanar da zama na biyu a cikin shekarar 2026 a Gombe State University, ƙarƙashin jagorancin State Coordinator, Sayyadi Bashir Modibbo Tukur.

‎Taron ya gudana ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobin TIGMEIN a fadin manyan makarantu na Jihar Gombe, da kuma bibiyar manufofi da tsare-tsaren da aka shimfiɗa a zamuka na baya.

‎Dukkan manyan makarantu da ke Jihar Gombe sun samu wakilci a wannan zama, ciki har da:
‎Federal University of Kashere
‎Gombe State University
‎Federal Polytechnic Kaltungo
‎Federal College of Education Technical Gombe
‎Federal College of Horticulture Dadinkowa
‎State Polytechnic Bajoga
‎College of Education and Legal Studies Nafada
‎College of Education Billiri

‎A yayin zaman, an jaddada muhimmancin:
‎Haɗin kai da jajircewa (commitment) a tsakanin Tijjanawa ma’aikatan manyan makarantu.
‎Wakilcin TIGMEIN a wuraren aiki da kuma shiga harkokin ƙungiyar.
‎Tallafawa daliban Tijjaniyya a makarantu.
‎Ƙarfafa wayar da kai (awareness) kan manufofi da ayyukan TIGMEIN.
‎Tsara short, medium da long-term goals domin dorewar ayyukan ƙungiyar.
‎Taron ya ƙare cikin yanayi na fahimta da ƙudurin ƙara ƙarfi da tasiri a harkokin ilimi, tare da burin ciyar da TIGMEIN gaba a Jihar Gombe da ma kasa baki ɗaya.


‎— TIGMEIN Media Team.

TIGMEIN TA RABA BASHIN JUYA JARI GA MATA A JIHAR GOMBEƘungiyar Tijjaniyya Grassroots and Empowerment Initiative of Niger...
25/01/2026

TIGMEIN TA RABA BASHIN JUYA JARI GA MATA A JIHAR GOMBE

Ƙungiyar Tijjaniyya Grassroots and Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMEIN), reshen Jihar Gombe, ta sake nuna jajircewarta wajen bunƙasa rayuwar mata masu ƙananan sana’o’i, ta hanyar ci gaba da rabon bashin juyar da jari ba tare da kuɗin ruwa ba.

A ranar Asabar, 24 ga Janairu, 2026, ƙungiyar ta raba jimillar kuɗi har Naira 760,000 ga mata 35, wanda ke matsayin kashi na farko (First Batch) na shekarar 2026 a ƙarƙashin shirin.

Wannan shiri ya kasance ginshiƙi na ƙoƙarin TIGMEIN wajen ƙarfafa dogaro da kai da bunƙasa tattalin arziƙin mata a matakin tushe, tare da tabbatar da cewa masu amfana sun fito daga sassa daban-daban na Jihar Gombe, ba tare da nuna bambanci ba.

A cewar bayanan da aka tattara, shirin ya riga ya amfanar da:
– mata 100 a shekarar 2024,
– mata 100 a shekarar 2025,
– yayin da a bana ma (2026) aka fara da mata 35, inda ake sa ran ƙarin masu amfana nan gaba kamar dai kowace shekara.

TIGMEIN ta jaddada cewa shirin bashin juyar da jari na daga cikin muhimman dabarunta na rage talauci, ƙarfafa tattalin arziƙin mata, da gina al’umma mai zaman kanta.

Tigmein Alkhairi ceh!

Tigmein Media Team Gombe

Rahoton Zaman Tattaunawa daga Yamaltu Deba LGA.‎‎Alhamdulillāh, a ranar Asabar, 24/01/2026, reshen TIGMEIN na Yamaltu De...
24/01/2026

Rahoton Zaman Tattaunawa daga Yamaltu Deba LGA.

‎Alhamdulillāh, a ranar Asabar, 24/01/2026, reshen TIGMEIN na Yamaltu Deba LGA ya gudanar da zaman tattaunawa mai muhimmanci ƙarƙashin jagorancin Coordinator na yankin, domin duba ci gaba, tsare-tsare da kuma ƙarfafa manufofin ƙungiya.

‎Abubuwan da aka tattauna sun haɗa da:
‎– Ƙarfafa haɗin kai da fahimtar manufofin TIGMEIN wajen yi wa al’umma hidima, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai domin samun nasara.
‎– Shirin Empowerment na mata 50 a kowane Ward, wanda zai kai jimillar mata 550, domin tallafa wa mata ta fuskar dogaro da kai, sana’o’i da ci gaban rayuwa.
‎– Tsarin ƙaddamar asusun aikin gina Masallaci, Makaranta da Shaguna, a matsayin manyan ayyukan al’umma da za su samar da ci gaba mai ɗorewa.
‎– Hanyoyin tattara gudunmawar kowane Ward, domin tabbatar da haɗin kai da samun nasarar aiwatar da tsare-tsaren da aka shimfiɗa.

‎Tattaunawan ya gudana cikin nasara, fahimta da ɗaukar alƙawarin cigaba da aiki tuƙuru, tare da ƙudirin ciyar da ayyukan TIGMEIN gaba a Yamaltu Deba LGA.


‎TIGMEIN Media Team Gombe.

‎RAHOTON ZAMAN TATTAUNAWA‎‎A ranar Lahadi 18/01/2026, Kwamitin TIGMEIN kan Kula da Manyan Makarantu (Committee on Higher...
20/01/2026

‎RAHOTON ZAMAN TATTAUNAWA

‎A ranar Lahadi 18/01/2026, Kwamitin TIGMEIN kan Kula da Manyan Makarantu (Committee on Higher Education Coordination Unit) ya gudanar da zama a ƙarƙashin jagorancin State Coordinator, Sayyadi Bashir Modibbo Tukur, inda shugabanni da mambobi s**a hallara domin tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi cigaban ƙungiyar.

‎A jawabin da State Coordinator ya gabatar, an yi cikakken recap kan TIGMEIN tare da fayyace dalilan kafuwar ƙungiyar.

Daga cikin muhimman manufofin da aka jaddada sun haɗa da:
‎Ƙarfafa sanin juna da haɗin kai tsakanin ma’aikatan manyan makarantu.
‎Wakiltar TIGMEIN a wuraren ayyukan mambobi.

‎Ƙarfafa shiga da bada gudunmawa a harkokin TIGMEIN.
‎Tallafawa ɗalibai Tijjanawa a makarantu,
‎bada gudunmawa wajen empowerment ta fannin ilimi.

‎Taron ya kuma tattauna kan commitment da haɗin kai a tsakanin Tijjanawa, inda aka jaddada muhimmancin aiki tare domin cimma manufofin TIGMEIN.

‎Daya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna shi ne bada gudunmawar kuɗi, inda aka kawo shawarar direct deduction daga asusun ma’aikata Tijjanawa, ta hanyar haɗin gwiwa da Bursary Unit, domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan TIGMEIN cikin tsari mai ɗorewa.

‎Haka kuma, an yi nuni da buƙatar ƙara wayar da kai (awareness) kan manufofi da ayyukan TIGMEIN, musamman a cikin manyan makarantu da wuraren ayyuka.

‎A ƙarshe, taron ya amince da muhimmancin tsara manufofi da burace-burace na gajeren lokaci, matsakaici da dogon lokaci (short, medium & long-term goals) domin tabbatar da ingantaccen tsari, ci gaba da ɗorewar ayyukan TIGMEIN.

‎Taron ya gudana cikin kwanciyar hankali, tare da ƙudurin ƙara haɗin kai da jajircewa wajen ciyar da TIGMEIN gaba, musamman ta fannin ilimi da walwalar Tijjanawa.


TIGMEIN Media Team Gombe

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tigmein Gombe State Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Tigmein Gombe State Chapter:

Share