05/06/2026
Tukunnama
Jam’iyyar APC A Jihar Gombe Ta Yi Dana-sanin Rashin Bai Wa Pantami Tikitin Takarar Gwamna
Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Jihar Gombe sun bayyana cewa jam’iyyar na ci gaba da fuskantar tasirin rashin bai wa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami tikitin takarar gwamna gabanin zaɓen 2027, lamarin da s**a ce ya haifar da rabuwar kai da kuma rage ƙarfin jam’iyyar a wasu sassan jihar.
A cewarsu, Pantami na daga cikin fitattun jagororin siyasa da s**a yi tasiri sosai a jihar, tare da samun karɓuwa a tsakanin matasa, malamai da sauran al’umma. Sun yi iƙirarin cewa da an ba shi damar fafatawa a sahihin zaɓen fidda gwani, APC za ta samu ƙarin haɗin kai da kuma goyon bayan mambobinta a faɗin jihar.
Majiyoyin jam’iyyar sun bayyana cewa ficewar Pantami daga APC zuwa PDP ta sauya yanayin siyasar Gombe, inda dubban magoya bayansa s**a nuna goyon baya gare shi. Sun ƙara da cewa wannan lamari ya bai wa jam’iyyun adawa damar ƙara faɗaɗa tasirinsu a wasu yankunan jihar.
Wasu daga cikin mambobin APC sun nuna cewa da an gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci tare da bai wa kowa damar gwada farin jininsa, da jam’iyyar ba za ta fuskanci irin ƙalubalen da take ciki a yanzu ba. Sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su ɗauki darasi daga abin da ya faru domin tabbatar da adalci, gaskiya da haɗin kai a duk wani tsari na zaɓen cikin gida a nan gaba.