24/01/2026
Dr. Jalo Jalingo da Shiekh Hassan Sautus Sunnah, idan kuka lura sun ɗora hannayensu a kan ƙirji, sannan hannayensu na dama na rike da guiwar hannayen hagu, wannan shi ake kira da Qabdu (قَبْضُ).
Idan kun sake lura, Shiekh Kabiru Haruna Gombe bayan ya ɗora hannayensa biyu a kan ƙirji, sai ya shimfiɗa tafin hannun dama a kan na hagu. Wannan shi ake kira da Wad'u (وَضْعُ).
Waɗannan salo dukkansu Sunnah ce ta Annabi Muhammad ﷺ. Sannan bayan ka yi Sunnar Qabalu ka kaurace wa Sadalu, to ya kamata ka dinga yin wannan Sunnah ma. Yau idan ka yi Qabdu gobe ko jibi sai ka yi Wad'u.
Allah ya ba mu ikon riƙo da Sunnar masoyinmu Annabi Muhammad ﷺ, Allah ya sa mu dace. Ameen.
Karatuttukan Malaman Musulunci ✍️