Tijjaniya News Hausa

Tijjaniya News Hausa For Islam And Muslim , And Islamic Advice
Like our Page. By Muslims & for Islam

Watan Ramadan na farko ba tare da Shehi ba, Gaskiya mun yi matuƙar kewar sa. Muna Roƙon Allah ya Haskaka Ƙabarin sa.
06/03/2026

Watan Ramadan na farko ba tare da Shehi ba, Gaskiya mun yi matuƙar kewar sa. Muna Roƙon Allah ya Haskaka Ƙabarin sa.

YAU NE ZAGAYOWAR RANAR YAƘIN BADARA rana mai k**ar ta yau 17 ga watan Ramadan, aka gwabza Yaƙin Badar, wani babban yaƙi ...
06/03/2026

YAU NE ZAGAYOWAR RANAR YAƘIN BADAR

A rana mai k**ar ta yau 17 ga watan Ramadan, aka gwabza Yaƙin Badar, wani babban yaƙi mai muhimmanci a tarihin Musulunci.

A wannan yaƙi:
🔹 Musulmai: 313
🔹 Kafirai: 1000

Duk da ƙarancin adadi da kayan yaƙi, Allah (SWT) Ya ba Musulmai gagarumar nasara.

Sak**akon yaƙin:
✔️ An kashe daga cikin kafirai 70
✔️ An k**a fursunonin yaƙi 70
✔️ Musulunci ya samu ƙarfafuwa da ɗaukaka

Allah Madaukakin Sarki Ya ce:

"Ba ku kashe su ba, sai dai Allah ne Ya kashe su."
— Suratul Anfal (8:17)

Darasi daga Yaƙin Badar:
📌 Nasara tana tare da masu imani
📌 Haƙuri da jajircewa suna kawo nasara
📌 Taimakon Allah shi ne mafi girma

Allah Ya sa mu kasance cikin masu koyi da darussan wannan babban tarihi. 🤲




SABUWAR TAFIYA******(Ayi Sharing)***Kamar yadda duk wani musulmi mai hankali ya gane cewa yaƙi da Iran ba yaƙi bane da y...
06/03/2026

SABUWAR TAFIYA
*
**
***
(Ayi Sharing)
***

Kamar yadda duk wani musulmi mai hankali ya gane cewa yaƙi da Iran ba yaƙi bane da yan Shi'a, yaƙi ne da Musulmi, haka nan duk wani mai hankali ya gane k**a Sheikh Sani Khalifa, Wulakanta Tijjanawa a jami'a, da sauran su, ba yaƙi ne da jama'ar gari ko zawiyya ko wuri kaza ba, yaƙi ne da Shehu Tijjani RTA.

Don haka mun fitar da sabuwar tafiya wacce zata ajiye banbancin zawiyoyi da sauran saɓani dake tsakanin mu, za mu fuskanci yau da goben mu, don kare mutuncin mu.

Zamu samar da tsari
Tsarin zai samar mana da murya
Muryar zata samar mana da daraja

Muna gayyatar duk wani matashi da matashiya masu kishin Shehu Tijjani RTA daga kowani gari da kowani zawiyya, ga link din group din:

Link 👇
https://chat.whatsapp.com/K9sV5c3U7vGBrKi1zuxbfG?mode=gi_t

YA HIMMATUSH SHEIKHU

✍️✍️✍️ Sidi Sadauki 💕

ƳAR MAJALISAR AMURKA, MACE MAI KAMAR MAZA ILHAN OMAR: JARUMA, MURYAR ADALCI, KUMA ƘAYAR MAƘOGORON AZZALUMAI! ✊🏿🧕A yau in...
05/03/2026

ƳAR MAJALISAR AMURKA, MACE MAI KAMAR MAZA ILHAN OMAR: JARUMA, MURYAR ADALCI, KUMA ƘAYAR MAƘOGORON AZZALUMAI! ✊🏿🧕

A yau ina so in jinjina wa guda cikin matan da s**a kafa tarihi, wadda ta zama zakaran gwajin dafi a cikin zuciyar siyasar duniya—Ilhan Omar.
Ba wai kawai mace ce ’yar asalin Afirka da ta kai matsayin Majalisar Wakilai ta Amurka (Congress) ba, a’a, ita wata babbar murya ce da take magana a lokacin da wasu ke tsoron ko tari.
Me ya sa muke alfahari da ita?
A lokacin mulkin Donald Trump, mun ga yadda aka yi ƙoƙarin amfani da ikon Amurka da dukiyar al'ummarta wajen rura wutar yaƙe-yaƙe da ba su da ƙa'ida a sassa daban-daban na duniya. Amma Ilhan Omar ta zama "Kayar Makwarwa" a makogwaron Donald Trump.

Yaki da Barnar Dukiya: Ta fito fili ta nuna baƙin cikinta kan yadda ake watsar da biliyoyin daloli na harajin jama’a wajen kera bama-bamai da kai hare-hare (Illegal Wars) a ƙasashen waje, maimakon a yi amfani da kuɗin wajen inganta rayuwar talakawa.

Tsadar Gaskiya: Duk da kalaman kyama, barazana, da nuna wariyar da ta fuskanta daga fadar White House ta wancan lokacin, Ilhan ba ta taba ja da baya ba. Ta tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin ɗan adam, tana mai cewa: "Ba za mu zuba ido Amurka ta riƙa zaluntar ƙasashe marasa ƙarfi ba."

Kishin Al'umma: Ita ce muryar da ke tunatar da duniya cewa yaƙi ba mafita ba ne, kuma ikon shugaban ƙasa bai ba shi damar keta dokokin ƙasa da ƙasa ba don kawai son ransa.

Mace Mai Hijabi, Mai Jarunta!
Ilhan Omar ta nuna mana cewa ba lallai sai kana da bindiga za ka yi yaƙi ba; gaskiya da jajircewa sun isa makami. Daga sansanin ’yan gudun hijira na Utange zuwa babban zauren majalisar dokokin Amurka, labarinta na nuna cewa adalci ba shi da iyaka.

Muna jinjina miki Jaruma! Ke ce muryar waɗanda ba su da murya. Ke ce kika tsaya wa duniya lokacin da ake neman mai ƙalubalantar zalunci da yaƙe-yaƙe ba bisa ƙa'ida ba.

CIKIN NASARORIN IRAN AKAN ISRAEL DA AMERICA.Ma'aikatar tsaro ta America Ta Tabbatar Da cewa, Iran na yunƙurin ganin baya...
05/03/2026

CIKIN NASARORIN IRAN AKAN ISRAEL DA AMERICA.

Ma'aikatar tsaro ta America Ta Tabbatar Da cewa, Iran na yunƙurin ganin bayan Donald Trump.

Don haka muna ƙara Roƙon Addu'a a wurin Al'ummar Musulmi baki ɗaya, Allah ya Ɗora Iran akan Waɗannan Azzaluman.

Iran Ta Ce Za Ta Kai Hari Kan Duk Wani Jirgin Ruwa Da Ya Yi Kokarin Wucewa Ta Mashigar Hormuz -Majiya : Aljazeera
03/03/2026

Iran Ta Ce Za Ta Kai Hari Kan Duk Wani Jirgin Ruwa Da Ya Yi Kokarin Wucewa Ta Mashigar Hormuz -

Majiya : Aljazeera

Tsawon lokacin da Sheikh Sani Khalifa Zariya ya yi a tsare a hannun jami'an gwamnati ba tare da ya bayyana a gaban kotu ...
02/03/2026

Tsawon lokacin da Sheikh Sani Khalifa Zariya ya yi a tsare a hannun jami'an gwamnati ba tare da ya bayyana a gaban kotu ba duk da an yi ta zama a kotun, ya sanya Al-majiran Sa da Masoyan Sa da ma Iyalan Sa cikin zullumi da tambayoyi k**ar haka.

1. Shin Khalifa yana raye?
2. To idan yana raye ma, shin yana cikin ƙoshin lafiya a matsayin sa na dattijo mai yawan shekaru?.

Wannan tambayoyi su Mutane ke fatan jin amsar su daga hukuma.
A ƙarshe muna fatan Allah ya ƙara ma Khalifa Lafiya, Allah ya mayar da shi cikin iyalinsa lafiya.

MU GANE ALLAN, ALLAHNE.  Ranar da aka kashe Sayyadina Hamza kisa na wulakanci, ALLAH bai bude kasa ta hadiye makasanba, ...
01/03/2026

MU GANE ALLAN, ALLAHNE.

Ranar da aka kashe Sayyadina Hamza kisa na wulakanci, ALLAH bai bude kasa ta hadiye makasanba, bai saukar musu da wata narko ta azababa, ANNABI (S.A.W) yayi fushi mai matukar razanarwa, har yayi alwashin daukar fansa mai tsanani a kan wadannan makasan.

TUNI SAI HALARARSA (S.W.T) TA AMSA AL'AMARIN SAI GA WAHAYI DA ALLAH KE CEWA.

وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُمْ بِهِ وَلَئِنْ صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِلصَّابِرِينَ

وَاصْبِرْ وَمَا صَبْرُكَ إِلَّا بِاللَّهِ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُ فِي ضَيْقٍ مِمَّا يَمْكُرُونَ

Sai gashi, ba'a dauki lokaci ba sai da ALLAH ya damka ikon dukkanin wadannan makasa karkashin ANNABI (S.A.W) an kashe wasunsu, wasunsu kuma sai s**a musulunta.

Baku lura ba, bai sauke wuta daga sama ko wata tsawa ga su Yazidu da s**a kashe jikokin ANNABI (S.A.W) ba, amma dai karshensu bai kyau ba.

WANNAN ABIN DA YA FARU JARABAWACE GA DUKKANIN MUSULMI, AYATOULLAHI YA BAYYANA NEMAN JIBANCINSA GA ALLAH, SAI ALLAH YA KARBESHI DOMIN YI MASA AIKIN DA SHI BA ZAI IYA BA.

KU SAURARA KUGA IKON ALLAH.

WALLAHI TALLAHI ALLAH BA ZAI BARI BA.
~ Muhammad Usman Gashua.

🤲
19/05/2025

🤲

12/05/2025

Mauludi na Musamman.

Karatu na musamman daga Bakin Sheikh Usman Mani (Chairman na Munazzamah na Gashua Bade L. G. A).

Gagarumin Mauludin Annabi ﷺ ƙarƙashin Ƙungiyar Agaji ta Munazzamatu Fityanul Islam Garin Azbak (Branch of Gashua Bade L. G. A).

A YI SAURARO LAFIYA.

Address

Sabon Gari
Gashua

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tijjaniya News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Tijjaniya News Hausa:

Share