10/01/2026
Muhimmancin Sadar da Zumunta (Silatur-Rahim).
Sadar da zumunci yana nufin kyautatawa ga 'yan'uwa na jini (k**ar iyaye, yayye, ƙannai, kawunnai, gwaggonni, da sauransu) ta hanyar ziyara, taimako, gaisuwa, da kyautata musu zato.
ALLAH (SWT) ya haɗa jin tsoronSa da kiyaye zumunci a wuri ɗaya don nuna girman al'amarin.
" وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ وَالْأَرْحَامَ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلَيْكُمْ رَقِيبًا.."
Manzon ALLAH (SAW) ya ce:
" مَنْ سَرَّهُ أَنْ يُبْسَطَ لَهُ فِي رِزْقِهِ، أَوْ يُنْسَأَ لَهُ فِي أَثَرِهِ، فَلْيَصِلْ رَحِمَهُ"
"Wanda yake son a yalwata masa a cikin arzikinsa, ko a jinkirta masa ajalinsa (a sanya albarka a rayuwarsa), to ya sadar da zumuncinsa."
A wani hadisin kuma, Annabi (SAW) ya yi gargaɗi:
" لاَ يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَاطِعٌ"
"Mai yanke zumunci ba zai shiga Aljannah ba."
Darussan da ke ciki:
•Hanyar Samun Arziƙi: Mutane da yawa su na neman kuɗi ido rufe, amma sun manta cewa kyautatawa 'yan'uwa makusanta yana ɗaya daga cikin manyan asiran buɗewar kofofin arziki.
•Haɗin Kai: Zumunci yana ƙarfafa soyayya da haɗin kai a cikin dangi.
•Tsoron ALLAH: Yanke zumunci babban zunubi ne da ke iya hana mutum shiga Aljannah, koda kuwa yana yawan sallah da azumi.
Ya ALLAH ka bamu ikon sadar da zumuntar mu, albarkar Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam.