Jibwis Dutsin-ma

Call Directions Website Contact the place of worship

Jibwis Dutsin-ma La da'atan li makhluqin fi ma'siyatil khaliqi... Organization for eradicating innovations and establishing sunnah

Allah ka jikan magabatan mu, ka karbi ayyukan da s**a gudanar lokacin rayuwarsu.Jibwis Nigeria
15/09/2026

Allah ka jikan magabatan mu, ka karbi ayyukan da s**a gudanar lokacin rayuwarsu.

Jibwis Nigeria

🕌 SANARWA: SABABBIN LOKUTAN SALLAH NA DUTSIN-MA DA KUSA DA KEWAYEAssalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Sabbin l...
14/09/2026

🕌 SANARWA: SABABBIN LOKUTAN SALLAH NA DUTSIN-MA DA KUSA DA KEWAYE

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.

Sabbin lokutan Sallah guda biyar na Dutsin-Ma da kewaye, na yau:
📅 Litinin, 02/04/1448H = 14/09/2026
🕋 Lokutan Salloli:
🌙 Asuba: 5:10 na safe

☀️ Zuhur: 12:45 na rana.

🌤️ La’asar: 3:43 na rana.

🌅 Magariba: 6:32 na yamma.

🌙 Isha’i: 7:35 na dare.

Kamar yadda aka saba, idan an lura da wani kuskure ko akwai gyaran da ya kamata a yi, muna roƙon a sanar domin a gyara.

🤲 Allah Ya sa mu dace, Ya karɓi ibadunmu. Amin.

JIBWIS SOCIAL MEDIA
Dutsin-Ma Local Government

Hotuna: Taron da JIBWIS ta halarta wanda "World Muslim League" (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY) ta shirya kuma take gudanarwa ...
08/09/2026

Hotuna: Taron da JIBWIS ta halarta wanda "World Muslim League" (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY) ta shirya kuma take gudanarwa a halin yanzu a birnin Jeddah ta ƙasar Saudi Arabia. Manyan Malamai daga sassa na duniya wadanda aka gayyata sun samu halarta. Daga Naijeriya akwai JIBWIS wanda Shugaba Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, da sakataren kungiyar Sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe, da "Director Basic Education" Jibwis Nigeria, Ass Prof Ibrahim Abdullahi R/Lemo s**a samu halarta.

Allah ya dawo mana dasu lafiya. Amin.

Jibwis Nigeria

Assalamu alaikum. Ga sabon awon lokutan Salloli guda biyar na garin Dutsin-ma da kewaye daga yau Lahadi 24/3/1448h=06/9/...
06/09/2026

Assalamu alaikum.

Ga sabon awon lokutan Salloli guda biyar na garin Dutsin-ma da kewaye daga yau Lahadi 24/3/1448h=06/9/2026m.

Asuba 5 : 10
Zuhur 12 : 50
Asar 3 : 45
Magrib 6 : 40
Isha'i 7 : 43

Kamar dai yadda aka saba idan anga gyara a sanar domin a gyara.

Allah Yasa mu dace. Amin.

Assalamu alaikum. Ga sabon awon lokutan Salloli guda biyar na garin Dutsin-ma da kewaye daga yau Juma'a 13/3/1448h=28/8/...
28/08/2026

Assalamu alaikum.

Ga sabon awon lokutan Salloli guda biyar na garin Dutsin-ma da kewaye daga yau Juma'a 13/3/1448h=28/8/2026m.

Asuba 5 : 10
Zuhur 12 : 50
Asar 3 : 45
Magrib 6 : 43
Isha'i 7 : 45

Kamar dai yadda aka saba idan anga gyara a sanar domin a gyara.

Allah Yasa mu dace. Amin.

JIBWIS ta ziyarci Cibiyar yaɗa addinin Musulunci a ƙasar Birtaniya Shugaban JIBWIS Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau, ya ziya...
27/08/2026

JIBWIS ta ziyarci Cibiyar yaɗa addinin Musulunci a ƙasar Birtaniya

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau, ya ziyarci Babbar Cibiyar yaɗa addinin Musulunci mai suna PIETY ISLAMIC EDUCATION TRUST a birnin PLYMOUTH dake kasar England (United Kingdom)

A Lokacin Ziyarar, Babban Director mai kula da Cibiyar, da Babban Limamin cibiyar, sun bayyanawa Sheikh Bala Lau, da tawagarsa irin gudummawar da Cibiyar ke bayarwa wajen bunkasa addinin Musulunci a kasar Birtaniya. Sheikh Bala Lau ya basu tabbacin hada karfi da karfe don kara inganta da'awa a kasar England' da Nigeria insha Allah.
Ziyarar tayi nasarar tattauna muhimman batutuwa wanda zai taimakawa juna wajen harkokin Da'awa a kasashen.

Cikin tawagar akwai babban Sakatare na kungiyar Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, da Director Project Engr Ashiru Baban Dede da Babban Limamin Masallacin Seven Sisters dake Birnin London Sheikh Adurrazak Ibrahim.

Allah ya bada ladan ayyukan da ake gabatarwa kullum. Amin.

Jibwis Nigeria

MARKAZU IMAM LAWAL DUTSIN-MA TA YI WALIMAR KAMMALA DAWRAH AKAN LITTAFIN "RISALATI FI DAMMI DABI'I LIN NISA"Makarantar Is...
27/08/2026

MARKAZU IMAM LAWAL DUTSIN-MA TA YI WALIMAR KAMMALA DAWRAH AKAN LITTAFIN "RISALATI FI DAMMI DABI'I LIN NISA"

Makarantar Islamiyya ta IMAM LAWAL ta kammala tare da gudanar da walimar Dawrah akan littafin dake cikakken bayani akan jinane na Mata wanda Sheikh Uthaimin ya wallafa.

Walimar wadda akayi a jiya Laraba 10-3-1448h/23-8-2026m a harabar Makarantar ta samu halartar Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa Ikamatis Sunnah reshen wannan karamar hukuma ta Dutsin-ma Alhaji Badamasi Sulaiman Karofi.
* Sheikh Bashir Aliyu Zakariyya (Mataimakin Sakataren Majalissar Malamai) kuma Sakataren Kwamitin Ilmi da Ilmantarwa.
* Sheikh Awwal Idris Assalafi (Shugaban Kwamitin Da'awa) kuma Mataimakin Shugaban kwamitin Ilimi da Ilmantarwa.
* Malam Tanimu Bala Dutsin-ma (Jami'in hulda da Jama'a PRO) kuma Shugaban kwamitin Social Media na karamar hukumar ta Dutsin-ma.

Malama Safiyya Ibrahim Gafai ce ta gabatar da Dawrar littafin ta kwanaki Uku inda aka samu halartar Malamai da Dalibai Mata sama da Dari da Ashirin.

Duk a lokacin walimar an gabatar da kyaututtuka guda biyu ga Malama Safiyya data karantar da littafin da kuma shedar halarta (Certificate) ga mahalarta Dawrar.

A Jawabin shi Shugaban kungiya ya bukaci Ɗaliban da s**a halarci Dawrar da su fadada karatun wannan littafi zuwa sauran sassan wannan karamar hukuma ga sauran Mata admin fa'idantuwa da ilimin da yake dauke da shi.

A nashi jawabin Shugaban kwamitin Da'awa ya tabbatar ma Shugaban da cewa in sha Allahu za ayi hakan banda komawa ba.

Daga karshe Shugaban Markaz din Ustaz Nasir Adam Awwal ya jaddada godiyar su ga Allah da Ya basu ikon farawa da kammala wannan Dawrah cikin nasara, tare da alwashin cigaba da yin hakan a nan gaba in sha Allah.

Jibwis Dutsin-ma.

MU SAN MALAMAN MU.....6Sheikh Bashir Aliyu Zakariyya (Abu-Sulaim)(Dr in view in sha Allah)* Mataimakin Sakataren Majalis...
26/08/2026

MU SAN MALAMAN MU.....6

Sheikh Bashir Aliyu Zakariyya (Abu-Sulaim)
(Dr in view in sha Allah)

* Mataimakin Sakataren Majalissar Malamai, Jibwis Dutsin-ma.
* Sakataren Kwamitin Ilmi da Ilmantarwa, Jibwis Dutsin-ma.
* Imam Na'ib.
* Malami, Dalibi, mai Da'awa
* Ga Boko ga Sittin.

Allah Ya kara ma rayuwa albarka.

Sheikh Bala Lau ya ziyarci ofishin jakadancin Naijeriya a kasar BirtaniyaShugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil bid'ah wa i...
25/08/2026

Sheikh Bala Lau ya ziyarci ofishin jakadancin Naijeriya a kasar Birtaniya

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil bid'ah wa iƙamatis sunnah Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yakai ziyara Babban Ofishin Jakadancin Nigeria dake birnin London a kasar Birtaniya. Tare da Shugaba akwai babban Sakatare na kungiyar ta JIBWIS ta kasa Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe da Director Project na Kungiyar Engr. Ashiru Baban Dede da Babban Limamin Masallacin Seven Sisters na Birnin London Sheikh Abdul Razak Ibrahim.

Kamar yadda shafin Jibwis Nigeria ta ruwaito, babban Jakadan Nigeria a UK (High Commissioner) Ambassador Amin Dalhatu tare da banyan jamian Ofishin Jakadancin ne s**a karbi Shugaba da tawagarsa. Angabatar da jawabai na Shugabanci tare da yiwa Nigeria adduoi na Alkhairi.

An kammala Ziyarar ta sada zumunci tare da mutunta juna cikin nasara.

Allah ya bada ladan ziyara. Amin.

Jibwis Nigeria

23/08/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuh.

TUNATARWAR DAURAH TA MATA.

Wannan Markazi na Farin cikin TUNATAR da Yan uwa MATA cewa wannan Daurah zata fara Gudana GOBE IN SHA ALLAH.

LITININ:- 24/08/2026
ZUWA
LARABA:- 26/08/2026.

LOKACI:- 09:00 Safe.
ZUWA
Karfe 12:00 na Rana.

Domin Tuntuba:-
08130807002. Or 07066487799.

A Iso Lafiya.

Address

Dutsin-Ma

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Dutsin-ma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis Dutsin-ma:

Shortcuts

Share