Abdullah Dumus

Abdullah Dumus عبدٌ ضعيفٌ حقيرٌ فقيرٌ إلى رحمة مولاه.

Innā lilLahi wa Innā ilaiHi raji'un !!!Muna miƙo ta'aziyyarmu ga dukkan ƴan uwa TIJJANAWA ƴan FAIDHA, bisa wannan babban...
28/11/2025

Innā lilLahi wa Innā ilaiHi raji'un !!!

Muna miƙo ta'aziyyarmu ga dukkan ƴan uwa TIJJANAWA ƴan FAIDHA, bisa wannan babban rashi da muka yi.

Tabbas mun yi rashin da ba za mu iya kwatanta nauyinsa a zukatanmu ba. AlLah Ya bamu juriyar ɗaukewa, Ya azurta mu da albarkar Shehi, Ya kyautata rayuwarmu a bayanshi, Ya kyautata ƙarshenmu don albarkar Sayyiduna RasululLahi SallalLahu alaiHi Wa aliHi Wa sallam.

Wal Abdu lilLah !

27/11/2025
A life well lived ..
27/11/2025

A life well lived ..

Innā lilLahi wa Innā ilaiHi raji'un !!!Muna miƙo ta'aziyyarmu ga dukkan al'ummar musulmi, tabbas mun yi rashin da ba za ...
27/11/2025

Innā lilLahi wa Innā ilaiHi raji'un !!!

Muna miƙo ta'aziyyarmu ga dukkan al'ummar musulmi, tabbas mun yi rashin da ba za mu iya kwatanta nauyinsa a zukatanmu ba. AlLah Ya bamu albarkar Shehi, Ya kyautata rayuwarmu a bayanshi.

Innā lilLahi wa Innā ilaiHi raji'un !!!

_Abdullah Dumus

26/11/2025

اللهم إني أعوذ بك
من شر سمعي
ومن شر بصري
ومن شر لساني
ومن شر قلبي
ومن شر منيي

Illolin auren ɗan bid'a ga mace Ahlus-Sunnah.Tabbas wannan maudhu'i ne mai muhimmanci da kyawun gaske da ya kamata malam...
25/11/2025

Illolin auren ɗan bid'a ga mace Ahlus-Sunnah.

Tabbas wannan maudhu'i ne mai muhimmanci da kyawun gaske da ya kamata malamai ko ɗaliban ilmi masu bincike su yi rubutu a kansa, musamman a wannan zamanin da farautar imani ta zama ruwan dare, zamanin da mutum zai iya yini a salihi ya wayi gari a ɗalihi, zamanin da ba wani a cikin masu daraja da ake shayin daɓawa maganar da aka ga dama.

Mace halitta ce mai rauni komai kafuwarta a Sunnah dole ko ba-daɗe ko ba-jima -in dai har da soyayya- sai ta bi mijinta a cikin Aƙida da fahimtar addini. Don haka dole iyaye suna buƙatarsu kula sosai da wanda za su baiwa aure, domin su kuɓutar da ƴaƴan da AlLah Ya basu amana.

Za mu ɗauki wannan maudhu'i da Ummu Ammara ta ɗauko mu yi masa abin da ya dace da yardar AlLah.

Dalilin shine ita ta kalli maudhu'i ne ta ɓangarenta na wahabiyanci, da na bi littafin na samu laƙabi Ahlus-Sunnah tana nufin ƴan ɓangarenta ne banda sauran Musulmi. Mu za mu bi maudhu'in da adalci irin na ɗaliban ilmi ba masu taimako ko aiki ga fahimtarsu ta addini.

Ustaziya Ummu muna godiya da kika jawo hankula mu zuwa wannan maudhu'i mai muhimmanci.

__Abdullah Dumus

Iyaye a ji tsoron AlLah, a kiyaye yiwa ƴaƴa mata auren dole, hakan na iya jefa yara da yawa cikin halakar da kune sila. ...
24/11/2025

Iyaye a ji tsoron AlLah, a kiyaye yiwa ƴaƴa mata auren dole, hakan na iya jefa yara da yawa cikin halakar da kune sila. Ba a yiwa zuciya dole.

Maza ku yiwa kanku karatun ta nutsu ku bar duk wacce ta nuna ba ta ƙaunarku ƙarara, akwai irinta dubu, ku dangana ku barwa AlLah zai sauya muku da wacce ta fita komai. Ƙin yin haka na iya haddasa muku matsalar da za ta iya kaiwa ga rasa rai ko wani sashe na jiki.

Address

Dutse

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdullah Dumus posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share