21/05/2026
AN YABA WA GWAMNA MALAM UMAR NAMADI FCA AKAN YADDA YAKE HIDIMTAWA ALQUR'ANI A JIHAR JIGAWA DAGA KARAMAR HUKUMAR MIGA.
An Gabatar da wannan Yabo Neh a wurin Bude Musabaqar Alqur'ani Matakin Karamar Hukumar Miga,yayin da yake Gabatar da jawabin Sakataren Hukumar Ilmi Matakin Farko na Karamar Hukumar Alhaji Muhammad Gambo Ishaaq Isawa yayi jinjina ga me Girma Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi FCA bisa yadda ya jajirce Harkar Alqur'ani take Cigaba a Jihar Jigawa ta yadda har Musabaqar Alqur'ani ta Kasa wannan Jiha ta dauki Nauyi a wannan Shekarar.
A Masa jawabin wakilin Islamic Education Bureau Alhaji Aminu Salisu Deputy Director Circular department ya Bayyana yadda Megirma Gwamnan Jihar Jigawa yake Baiwa Ma'aikatar su duk irin gudunmuwar da s**a bukata da wacce ma Basu Bukata bah,yace wannan Nasarar ta samo Asali Neh dalilin jajircewar Executive Secretary Islamic Education Bureau Dr Mubarak Abdulwahab Hassan.
A Karshe Megirma Kaigaman Dutse Hakimin Miga Wanda megirma Sarkin Miga ya wakilta ya Bude wannan Musabaqar da Sunan Allah me Rahama me Jin Kai.
✍️
Ashaabul Qur'an Foundation Tv