Nurul Islam Academy Dukku, Gombe State

Nurul Islam Academy Dukku, Gombe State Al-Ilmu Wat-tarbiyya Islamiyya

04/10/2025

Ya kai ɗan uwa musulmi, an kāma wāsa da hankalinka a wannan addini kénan, har sai ka iya banbancé tsaƙanin

1- Malami 🆚 Motivational Speaker,

2-Mai karatu daki-daki na zauré 🆚 wanda ya tsaƙuro daga syllabus

3- Mai Tarbiyyar Ruhi 🆚 kuma content creator.

Kai, ka jé ka saurari karatun , kai za ka fahimci ban-bancin tsaƙanin da

Ka ji yanda aka ɗauko Mas'ala daga tushénta filla filla, a bi ko wani fanni na ilimi a ji matsayar su akan wannan Mas'ala.

Gaskiya Malamai na Zauré,
Kuma shi karatu ba daga kafa camera bané.

10/06/2025
10/06/2025
10/06/2025

الحمد لله على نعمة الاسلام

12/07/2023

KUN LURA DA WANNAN BATU DA KYAU KUWA...?

Idan dayan su ya tashi neman Suna da Shuhura tsakanin al'umma a wasu 'Yan Shekaru da s**a gabata, to ya kan dirar da barikancinsa kan daya daga cikin jagororinmu kamar Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) ko babban Almajirinsa Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) ta hanyar shirya kage, sharri da karya.

Amma cikin shekarun nan, akalar tunanin dukkanin masu neman suna da shuhura cikin Wahabiyya da wancenansu, ya karkato kachokam kan Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H), kullum cikin bibiyar dukkanin motsinsa suke dan su samu abin kalaci a kiwonsu na neman aibobinsa...?

Hakan ya kasance ne saboda dalilai guda 2.

1- Irin Uslubin da Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) yabi wajen isar da da'awowinsa, har milyoyi s**a amsa kiransa zuwa ga Addinin ALLAH, kwatankwacinsa Maulana Prof. yake Jaddadawa, sai ya zamo kullum yana samun karbuwa a zukatan dubban al'umma, wannan abin yana hassala su. Domin Uslubine na jaddada sunnonin MANZON ALLAH (S.A.W) a aikace ba a da'awa ba.

2- Babban abinda Wahabiyanci ta ginu akai shi ne, wargaza hadin kan Musulunci, ta hanyar zagin duk Musulmin da bai kungiyarsu da sunaye munana, kamar Kaf*rai, Mushrikai, Yan Bidi'ah da sauransu, sai ya zamo shi kuma Maulana Prof. yana kira zuwa ga hanyar hadin kai, fahimtar juna da kuma barin aibata juna, wanda su kuma hakan idan ya kau, to zasu rasa jarin da suke habbaka kasuwancinsu na cinikayyar dulmiyarwa da suke.

A hakika duk abinda suke yi, na nuni ne izuwa ga tsada, daraja da kuma daukakar da ALLAH yayiwa Maulana Prof. akansu da dukkan Malamansu, dalilin kyautata koyinsa da MANZON ALLAH (S.A.W) da kuma bayin ALLAH managarta, kuma haka zasu yi iya yinsu, ba tare da sun cimma sa ba da izinin ALLAH.

MUNA ROKON ALLAH YA BASHI KARIYA DA KARIYARSA, YA TSARE SHI DA KULAWARSA.

ALHAMDULILLAH

Mu ma Abul-fathi ne
04/06/2023

Mu ma Abul-fathi ne

21/02/2023

KAR KA BADA RAYUWAR KA

Duk gatan da zakayi wa Dan takara ka bashi kuria da dukkan abin da zaka iya Amma banda Rai

KAR KA KASHE KAR KA BARI A KASHE KA

الحديث صحيح في الصحيحين، عن النبي -عليه الصلاة والسلام- أنه قال: إذا التقى المسلمان بسيفهما فالقاتل، والمقتول في النار قيل يا رسول الله هذا القاتل فما شأن المقتول؟ قال: لأنه كان حريصًا على قتل صاحبه.
Yazo a cikin Hadisi ingantacce acikin Bukhari da Muslim daga Manzon Allah sAw cewa "Idan Musulmai biyu s**a hadu da takuban su (s**ayi fada) to wanda ya kashe da Wanda aka kashe duk suna cikin wuta " sai aka ce Ya Ma'aikin Allah wannan Kam shi ya kashe to me sha'anin (laifin) Wanda aka kashe Kuma sai yace "Lallai ya kasance Yana kwadayin kashe Abokin fadansa.

Dan haka ina kira ga yan uwa Musulmai matasa musamman masu rike makamai da kar suyi kuskuren bata lahirar su ta hanyar gyara duniyar wani

Allah bamu zaman lapiya da shugabanni nagari.

30/09/2022

Allah Ka yi mana arzikin ni'imar son dangantakar Musulunci fiye da dukkan dangantaka

Allah mun gode a ni'imar Musulunci

Allah Ka sa mu cika muna Musulmai

Address

Balu Street 02
Dukku

Telephone

+2347037372278

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nurul Islam Academy Dukku, Gombe State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Nurul Islam Academy Dukku, Gombe State:

Share