Qudsiyya Sirril faidati

Qudsiyya Sirril faidati من كان الله معه فمن عليه ,ومن كان عليه فمن معه، من وجد الله ،وجد كل شيء، و من فقد الله فقد كل شيء.

حسبن الله، فنعم الوكيل.

11/06/2026
Shehu yace Awa guda Idan kaba Allah ita, ma'ana Kayi Ibada cikin ta da ikhlasi tana jawo dukkan lokutan da ka ɓata ba ci...
11/06/2026

Shehu yace Awa guda Idan kaba Allah ita, ma'ana Kayi Ibada cikin ta da ikhlasi tana jawo dukkan lokutan da ka ɓata ba cikin Allah ba su dawo cikin Allah. Shehu yace shi yasa Lazumi safe da na yamma da Wazeefa da zikirin juma'a sun Isa su maida rayuwar mutum gaba ɗaya a cikin Allah.

A wani ƙauli Shehu yace Salla guda karɓaɓɓa tana raya dukkan sallolin da kayi waɗanda ba a karɓa ba, Shehu yace Salla karɓaɓɓa itace rayayyar sallah wadda aka sama ruhi, shi yasa Shehu yake ƙarfafa yin Sallah a cikin zawiyya don Shehu Ahmad tijjani yayi muna albishir da cewa Salla a cikin zawiyya karɓaɓɓa ce yanke ba shakku.

Ibn Ata'allah al-iskandari mawallafin littafin HIKAMU yace "Wa'ridi na zo ma Arifi ba zato ba tsammani saboda Allah ya n...
06/06/2026

Ibn Ata'allah al-iskandari mawallafin littafin HIKAMU yace "Wa'ridi na zo ma Arifi ba zato ba tsammani saboda Allah ya nuna mai cewa ba Kayan shi bane na Allah ne"

Tabbas haka abin yake, Wa'ridi yana sauka a zuciya ba tare da mutum ya san zai zo ba, ba ruwan waridi da Bagiren da kake ko halin da kake ciki, Wa'ridi na iya zuwa kana ban ɗaki amma ka yini a cikin zawiyya baka same shi ba, kuma Wa'ridi na iya zuwa kana kasuwa kana sabgoginka amma yaƙi zuwa lokacin da ka Himmatu wurin karatun Azkaranka, da misalai irin waɗannan da yawa masu saɓa ma hankali da zato. Saboda Halara tana nufin ta nuna ma Asha'bul Wa'ridat cewa Wa'ridi kayan ta ne ba nasu ba, tana saukar da shi lokacin da taga dama a Bagiren da taga dama, a halin da taka dama kuma a cikin zuciyar da ta so ta keɓanta.

Allah ya ƙara muna hasken Wa'ridatu muyi ta samun UPDATE daga Halara.

Ƙarin haske : Amma wasu lokuta sai mutum ya fara tafakkuri a cikin abu yana son ya fahimci abun sannan Wa'ridin wannan abin Yake sauka.

Daga cikin karatun da Khalifa Ibrahim Sheikh Aliyu Muhammad Bunza QS yayi na Littafin MAJLISOSAN SHEHU ALIYU QS:Shehu Al...
02/06/2026

Daga cikin karatun da Khalifa Ibrahim Sheikh Aliyu Muhammad Bunza QS yayi na Littafin MAJLISOSAN SHEHU ALIYU QS:

Shehu Aliyu Muhammad Bunza QS yana magana akan Sauƙin da aka samu na lokacin da ake ɗauka a Sadu da Allah ta hanyar Sawwaƙa yin Tarbiyya:

Shehu yace Kamar yadda tafiya a zamanin yanzu tafi sauƙi Bisa ga tafiya a zamanin da baya, haka tafiya cikin Allah tafi sauƙi a wannan zamanin bisa ga zamunan da s**a wuce.

Shehu yace Kamar yadda Allah yake sawwaƙa al'amurran duniya ta hanyar Ilmin kimiya da fasaha haka yake sawwaƙa neman Allah da samun Allah ta hanyar Waliyyai.

Note : A ƙarƙashin kulawar mawlanmu Shehu Aliyu Muhammad Bunza QS, shiga tarbiyya da samun wusuli bai wuce sati ɗaya, da yawa ma suna samun Fatahi a cikin kwanaki Biyu ko Uku, akwai waɗanda ma ke gane komi a cikin kwana guda.

Wannan falala ce daga Allah.

NURUL ABHAR yana ɗaya daga cikin gwala'gwalan Azkaran da Shehu Aliyu Muhammad Bunza QS ya fitar, Shehu yace Cigaban Litt...
22/05/2026

NURUL ABHAR yana ɗaya daga cikin gwala'gwalan Azkaran da Shehu Aliyu Muhammad Bunza QS ya fitar, Shehu yace Cigaban Littafin Shehu Ibrahim Radiyallahu ta'a'la anhu ne SIRRUL AKBAR. Shehu Ibrahim yayi ishara da bayyanar wannan littafin Bayan wafatinsa, a ƙarshen Sirrul akbar Shehu yana cewa :
وهذا التأليف لا ينتهي وفي وقت آخر يفعل الله ما يريد

"wannan littafin bai ƙare ba, a wani lokacin Allah zai gudanar da abinda ya nufa"

Nurul Abhar ala Sirrul akbar na Mawlanmu Shehu Aliyu QS shine cikon Sirrul akbar na Mawlanmu Shehu Ibrahim (r a). Shehu yace a Wani lokacin da ba zamanin shi Shehu ba, ALLAH zai gudanar da abin da yaso, ma'ana, wani sirri zai ɓullo cikin Sirrin da Shi Shehu ya Assasa. Kuma mu munyi imani kuma mun shaida Shehu na Ishara da wannan Sirrin da Shehu Aliyu QS yazo dashi ne.

Daga cikin Falalolin Karatun wannan Azkaran na Nurul Abhar shine ALLAH na saukar ma wanda ya lizimce shi da SAKINAH, Mai karatun shi zai samu natsuwa, ba ƙaramin ha'li zai iya tayar mai da hankali ba, komi wahala komi talauci ba'za ka taɓa a fuskar mutum ba, saboda shi wannan NURUL ABHAR ɗin yana ɗauke da Sirrin TA'BUT ɗin nan na Bani Isra'ila wanda Allah yace Akwai natsuwar su (fihi sakinakum) a cikin shi. Wannan Nurul Abhar Sirrin wancan TA'BUT ɗin ne na lokacin ƊALUT da JALUT.

ALHAMDU LILLAH

JUMA'A KAREEM.

Ɗan uwa ka kasance mai gaskata al'amarin Allah a Duk Inda kake a kowane zamani kake ciki.Daga cikin karatun da Mawlanmu ...
21/05/2026

Ɗan uwa ka kasance mai gaskata al'amarin Allah a Duk Inda kake a kowane zamani kake ciki.

Daga cikin karatun da Mawlanmu Khalifa Ibrahim Sheikh Aliyu Muhammad Bunza QS yake yi na litattafin da ke ɗauke da Majlisosan Shehu Aliyu QS yayi bayani akan wannan sifar kamar yadda Shehu Aliyu Bunza QS yayi ta ba'yani akan ta, wato Sifar gaskatawa.

Khalifa yace Shehu na yawan cewa baka taɓa jin Inda Allah yace ويل للمصدقين ba, ma'ana "Bone ya tabbata ga masu gaskatawa" sai dai yace ويل للمكذبين , wato " Bone ya tabbata ga masu ƙaryatawa". Shehu yana ƙarfafa wannan magana da hadisin Manzon Allah SAW inda yake cewa halaye guda ba abin da ya kai su Alkhairi, kyautata zato ga Allah da kuma kyautata zato ga bayin Allah, sannan halaye Biyu ba abin da ya Kai su Sharri, munana zato ga Allah da munana zato ga bayin Allah. A nan kyautata zato ga bayin Allah ya na ɗaukar Sifar gaskata su Idan su ka zo da wani Al'amari daga Allah, munana zato garesu kuma yana ɗaukar Sifar ƙaryata su ba tare da hujja ta bayyana gareka ba.

Khalifa yace, amfanin mai gaskatawa shine bazai dawwama cikin wannan halin nashi ba har sai ya gaskata abinda gaskiya ne daga Allah kuma wannan abin ya zama silar tsira gareshi, haka ma cutar da ke tare da yawan ƙaryatawa shine mutum bazai gushe yana ƙaryatawa har sai ya ƙaryata abun da zai zama Silar ta'ɓewa gareshi domin abinnan da ya ƙaryata al'amari ne Kuma gaskiya ce daga Allah.

Ƙaryatawa ne ya halakar da yahudawa da nasara, kuma shi ya taɓar da Ma'su ƙaryata waliyyai, ya sa yan ɗariƙar mu ta tijjaniya s**a tabka hasarar Rashin Yarda da failar Shehu Ibrahim, Hakanan ne da Yawan Yan uwan mu yan faila suke cikin hasarar Rashin Yarda da SIRRIN FAILA na halarar Qudsiyya.

Allah ya bamu Sirri da ruhi da zuciyar gaskata duk wani al'amari da ya fito daga gareshi. Ya samu a cikin SIDDIQAN BAYINSA.

Allah (taba'raka wa ta'a'la) yana cewa :

قَالَ ٱللَّهُ هَٰذَا يَوْمُ يَنفَعُ ٱلصَّٰدِقِينَ صِدْقُهُمْ ۚ لَهُمْ جَنَّٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا ۚ رَّضِىَ ٱللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا۟ عَنْهُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Allah Ya ce: "Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma."

Allah ka sa mu kasance a cikin su ta kowace Fuska a bisa kowace ma'ana.

21/05/2026

Wannan Karatu ne na masu da'awar Haq'iqa ne

"Rashin sanin Allah shi ke sa a bayyanar da Sirrin Allah"

Masu da'awar su yan haq'iqa ne su saurari karatun nan da kyau, za'su fahimci abinda basu sani ba game da Sirrin Allah.

Khalifa Ibrahim Sheikh Aliyu Muhammad Bunza

Address

Birnin Kebbi/kalgo Road
Birnin-Kebbi

Telephone

+2349160334775

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qudsiyya Sirril faidati posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Qudsiyya Sirril faidati:

Share