08/04/2026
Waɗanda ke inkarin Sala'til Fatih ba'su da Ruhin haqiqa Muhammaadiyya a tare dasu, saboda Sala'til Fatih shine Mabuɗin fahimtar haqiqa Muhammaadiyya.
Fatihi lima ugliqa - Khatimi lima sabaqa - Nasiril haqqi bil haqqi - Ha'di ila' siraɗal mustaqeem. Waɗannan Haqiqoqin Asrarai ne na Ruhin Manzon Allah SAW, Kuma Halarori a cikin halarorin shi, Hasken su bazai sauka a zuciyar da bata karatun salatil Fatih ba.
Wanda Allah yayi ma baiwa ta azaliyya da Sirrin Ruhin Muhammaadiyya zai yarda da Sala'til Fatih yanke ba tare da wani shakku ba, Kuma Zai lizimce shi ko ba ɗan ɗariƙa bane shi, ko da bai lizimce karatun shi ba ba zai ƙyamace shi a Zuciyar shi ba.
Akwai bambanci tsakanin Shari'a Muhammadiyya da Haqiqa Muhammaadiyya, Shari'a Muhammadiyya itace Haqiqar zahiri da kowa ya sani ta Manzon Allah SAW, kamar : shine ke Annabin Allah ne, cikamakon annabawa ne, fiyayyen halitta ne, Ma'asumi ne, da sauran khususiyyoyin Ma'aiki na zahiri wanda duk Musulmi ya san dasu
Haqiqa Muhammaadiyya kuma tana bayani ne akan Ruhin Annabi SAW ba Bashariyar shi ba, Khususiyyoyin da Allah ya keɓance shi dasu na baɗini ba na zahiri waɗanda a cikin Zuciya Ake riskar ba acikin nassin qur'ani ba ko hadisi, Duk da yake akwai hadisan da ke ishara da wannan haqiqar amma sai da hasken Zuciya Ake Fahimtar ta.
Haka abin yake. Salatil Fatih Mabudi ne na Fahimtar wannan haqiqar manzon Allah ta baɗini ta ruhin Manzon Allah SAW. Don haka kada ka wahal da kanka wurin jayayya da wanda bai yi imani da Sala'til Fatih ba, bai da Ruhin haqiqa Muhammadiyya a tare dashi.
Shehu Ahmad tijjani (Radiyallahu ta'a'la anhu) Yace Sala'til Fatih Al'amari ILA'HIYYA ne, ma'ana daga Halarar Zatin Allah ya fito, to wanene yazo da Sirrin Halarar Zatin Allah in ba Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ba?