05/12/2025
جمعة مباركة
Zikirin Juma'a
Daga cikin rukunan Tarikar TIJJANIYYA zikirin Juma'a yana da matukar muhimmanci,yan uwa muyi kokari a dinga ganin mu a cikin dahirar ba wai kawai mu dinga amsa sunan yaran SHEHU TIJJANI ba amma idan akazo dahira akasa ganin mu ba.
👉👉Halartar zikirin Juma'a yana kawowa mutum nutsuwa da kuma fadin zuciya,zakaji kanka tare da ALLAH da MA'AIKI S.A.W, zakaji kap duniya ba Abun da ke maka dadi fiye da zaman.
👉👉Zikirin Juma'a na kore kiyayyar juna da hassada da kulle kullen juna a zuciya, zakaji kowa ma ba ruwan ka dashi sai ALLAH da MANZON SA S.A.W, Zakaji inama a lokacin a dauki ranka ka koma ga mahalicci zuciyar na acikin irin wannan yanayin.
👉👉Zikirin Juma'a na mayar da ma'ajubi Harifi,a yayin da kake cikin dahirar zakana jin abun da Harifai keji k**ar kaima kana a cikinsu sai dai kakoma ma'ajubin ka idan aka tashi daga dahirar.
👉👉Zikirin Juma'a na kore yunwar mai jin yunwa yasa kaji kanka a koshe,sai dai yunwar ta dawo bayan katashi, yana sa mara lafiya yaji lafiyar sa ya cika k**ar ba wanda ma yakaishi lafiya.
Idan kayi fana'i acikin zikirin zakana jin wasu muryoyi wanda kai da kanka ma zaka tabbatar wannan muryar ba na mutane bane sai dai na Mala'iku tsarkaka.
ALLAH YASAKAWA SHEHU TIJJANI DA MAFIFICIN AL-KHAIRI