28/05/2026
AREWA MUN ZAMA ABIN TAUSAYI
Maigirma Shugaban Kasa Tinubu ya amince da fara matakan tantancewa da bin ka’idoji domin aiwatar da manyan tashoshin jiragen ruwa guda biyar da ake shirin ginawa
An dauki wannan matakin ne da nufin dawo da sama da kashi 70 cikin 100 na kayayyakin Nigeria da ake jigilar su zuwa wasu kasashen Afirka
Tashoshin jiragen ruwan da za'a gina da gyarawa sun hada da:
(1) Jihar Lagos - Tashar Ruwa ta Badagry
(2) Jihar Ondo - Tashar Ruwa ta Olokola
(3) Jihar Akwa Ibom - Tashar Ruwa ta Ibom
(4) Jihar Cross River - Tashar Ruwa ta Bakassi
(5) Jihar Rivers - Tashar Ruwa ta Bonny
Sai dai babban abin takaici da kuma abin tausayi da haushi shine yankin Arewacin Nigeria bai amfana da wannan aiki da za'a yi ba, wato ba'a yiwa Arewa adalci ba
Tsohon Shugaban Kasa Marigayi Muhammadu Buhari ya bada kwangilar gina tashar ruwa a yankin Arewa wato Baro Inland Water Port dake cikin Jihar Niger karamar hukumar Agaie, kusa da Kogin Niger ta yanda manyan jiragen ruwa masu dakon kaya daga Kasashen duniya zasu dinga zuwa Arewa kai tsaye su sauke kaya
Sannan Shugaba Buhari ya bada kwangilar gina Kaduna Inland Dry Port, wato busasshiyar tashar jirgin ruwa da ke kan kasa, ba a bakin teku ba, zai kasance ana kawo kaya daga manyan tashoshin ruwa kamar Apapa ko Tin Can Lagos zuwa Kaduna ta jirgin Kasa ko mota, sannan a yi duk harkokin kwastam da jigilar kaya a gurin
Tsakani da Allah ya kamata ce wannan Gwamnatin ta aiwatar da aikin tashar ruwa da na kan kasa da Gwamnatin Buhari tayi kudirin ginawa, a kalla dai yankin Arewa ya amfana, kuma an yiwa Arewa adalci, amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garin su
Mutanen Arewa ku hada kai, ku nema wa yankin mafita, domin ba shakka ana barin yankin Arewacin Nigeria a can karshen baya
Allah Ya bamu mafita na alheri