02/07/2026
MUHADHARA!!!
A madadin Ƙungiyar Ɗaliban Bauchi da Gombe masu karatu a Jami'ar musulunci dake Nijar (BAGSU), nake amfani da wannan dama domin gaiyatar Al'umar musulmi mazauna cikin garin Bauchi da kewaye, muhadara ta musamman da ta shirya a garin Bauchi.
ana sa ran gudanar taron idan Allah Ya nufa a ranar Laraba 8/07/2026 a masallacin Juma'a dake Ƙofar Ran Bauchi tsakanin Magriba da Isha'i.
ana sa ran muhadarar za ta samu halartar;-
Ustaz Muhammad Shu'aib Al'adamawy
(Shugaban ƙungiyar ɗaliban arewacin najeriya)
Ustaz Ibrahim Hanafy Abdurrahman
(Abu Aneesah)
da sauran malamai da ƴan uwa dalibai.
Allah Ya bada ikon halarta Amin.
✍️ Y.A Ibrahim Alhilaly.
(President, BAGSU)