08/01/2026
🕌 MUSABAQAR ALƘUR’ANI MAI GIRMA (RAMADANIYYA) KARO NA BIYU............
TIRWUN QUR’ANIC COMPETITOR’S ASSOCIATION, BAUCHI (TIQCAS)
A cikin wannan wata mai albarka na Ramadan mai zuwa, ƙungiyar na farin cikin gayyatar al’umma, makarantu, malamai da daliban Alƙur’ani zuwa Musabaqar Alƙur’ani Mai Girma ta Ramadaniyya.
Wannan Musabaqa an tanade ta ne domin:
1. Ƙarfafa haddar Alƙur’ani
2. Gina tarbiyya da kyawawan ɗabi’u
3. Ƙara haɗin kai tsakanin makarantu da al’umma.
🏁 Tsarin Musabaqa
Musabaqar tana da matakai biyu:
1. First Stage (Mataki na Farko)
– Za a tantance mahalarta gwargwadon rukuni (Hizb).
2. Second Stage (Final / Mataki na Ƙarshe)
– Waɗanda s**a yi nasara a mataki na farko za su fafata a mataki ƙarshe.
📚 Rukunin Gasar (Categories)
1. 2 Hizb
2. 5 Hizb
3. 10 Hizb
4. 20 Hizb
5. 30 Hizb
SANARWA : Umar Almustapha
Secretary General, Co-ordinator Musabaqaat.
For......
Hafiz Salihu Badamasee Uba (Khadimul Qur’an)
Chairman, TIRWUN Qur’anic Competitor’s Association (TIQCAS)