Sheikh Zakzaky Ikon Allah

Sheikh Zakzaky Ikon Allah Labbaika Ya Rasulullah!

13/04/2026

Sheik Zakzaky Exposes Nigeria Government's Role in Insecurity

RANAR TARIHI.....بسم الله الرحمن الرحيم. Syed Mojtaba Khamenei (Dz), ya zama Supreme Leader. Salawat Ala Muhammad Wa'aly...
08/03/2026

RANAR TARIHI.....

بسم الله الرحمن الرحيم.

Syed Mojtaba Khamenei (Dz), ya zama Supreme Leader. Salawat Ala Muhammad Wa'aly Muhammad (S).

— Muhammad Balaa Afuwaa

Na taba ji Jagora Sayyid Zakzaky (H) ya fadi cewa duk abun da kake tunanin zai faru, to idan ya faru ya zama ba jarabawa...
01/03/2026

Na taba ji Jagora Sayyid Zakzaky (H) ya fadi cewa duk abun da kake tunanin zai faru, to idan ya faru ya zama ba jarabawa ba kenan. Tunda kila zai zama ka shirya ma zuciyar ka daman tun kafin faruwar sa. Amma jarabawa shi ne abu ya faru wanda ko a mafarki baka taba tsammanin zai faru ba. Ba ka shirya masa ba ko kadan. Wannan shi ne jarabawa da ma’anar ta.

Mafi girma da munin jarabawar da mu ke tsoro a wannan gwagwarmayar to yanzu ta faru. Allah (T) cikin rahamarSa Ya zabi Ya dauki Jagora Sayyid Qa’id (R) a lokacin da mu ke tsananin bukatar shi. Wannan na nufin kenan ma’abota dagawa sun yi mafi munin abun da za su iya yi. Babu wani kisa, ko wata jarabawa da za ta zo ta fi wannan muni ko zafi a zuciya.

Sai dai kuma, duk da zafi da radadi da ke zuciyar muminai a wannan lokaci, kar mu manta cewa haka sunnar tafarkin nan yake. Tafarki ne na tsayuwa kyam, da kin mika wuya ga ma’abota dagawa har karshen numfashi, har tabbatuwar nasara (wanda shahada shi ne mafi koluluwar nasara da ma’abocin gwagwarmaya zai samu). Wannan tafarki ya dauki annabawa (as), da Imamai (as) da manyan bayin Allah.

Kar zuciya ta cire fata daga rahama da taimakon Allah (T). Lallai Allah (T) na tare da mu! Kuma daman mun san cewa manyan-manyan nasarori na biyo bayan manyan jarabawowi ne. Tabbas jinin Jagora mai girma da aka zubar, da na iyalan sa; Inshaa Allah shi ne zai share fagen kawo karshen ma’abota dagawa da zaluncin su a doron kasa.

Dangane da Jamhuriyya da duniyar mukawama kuma mun san cewa babu abun da zai tsaya. Daman Jamhuriyya falsafa ce, fikira ce; ba ta ginu akan mutane ko gine-gine ba ne, kamar yanda Jagora Shahid Sayyid Qa’id (H) ya fada. Saboda haka duk wanda aka rasa Allah (T) Zai tayar da wani a madadin sa, zai dauki tuta ya dora daga inda aka tsaya har zuwa nasara Inshaa Allah! Jamhuriyyar Musulunci ba zata taba kaiwa kasa ba. Burin makiya na ganin rugujewar ta ba zai taba tabbata ba da izinin Allah!

Kuma wannan jarabawa ne, kuma Inshaa Allah duk da girman sa zai wuce. Kuma Inshaa Allah natijar da wannan jarabawar zai bayar mai girma ne sosan gaske. Inshaa Allah!

- Najeeb Maigatari
01/03/26

01/03/2026

Address

Bauchi

Telephone

+2348032164800

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Zakzaky Ikon Allah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Sheikh Zakzaky Ikon Allah:

Shortcuts

Share