04/01/2026
KUNGIYAR FITYANUL ISLAM TA KASA
SANARWA GA MANEMA LABARAI
KUNGIYAR FITYANUL ISLAM TA NIJERIYA.
Ta yi Allah Wadai da tsare Mataimakin Shuga aban ta na kasa,
SHEIKH SANI KHALIFA ABDULKADIR ZARIA
Na Tsawon kwana 24 batare da Shari,a ba .
Shuwagabanin kungiyar Fityanull Islam ta Nijeriya,
Sun Fitar da Kiran Gaggawa Ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro game da cigaba da tsare .
Sheikh Sani khalifa Abdul Kadir Zaria ba abisa ka'ida ba .
Wannan lamari ne Mai cike da Damuwa kwarai da Gaske,
Wanda ya Shafi babban jagora a Duniyar muslunci da kuma Al'umma
Sheikh Sani khalifa, Wanda Babban Mukaddami ne A Darikar Tijjaniya ,kuma Mataimakin Shugaban Fityanul Islam na kasa ,
Sannan Shugaban Majalisar Malamai (Ulama'u Commitee) Na Kasa ,
Yau kwanaki Ashirin da hudu (24) Kenan Yana tsare a hannun hukumomi ba tare da an Gurfanar da Shi a Gaban Kotu ba.
1.keta Hakkin Da kundin tsarin Mulki ya tanada
A karkashin kundin tsarin Mulki jamhuriyar Tarayya Nijeriya na Shekarar 1999,Bai kamata a tsare dan kasa fiye da Sa'oi 48 ba tare da Sa bakin Kotu ba.
Wannan tsawaita tsare shehin malami da ake Yi ,ya Saba wa hakkinsa Na dan Adam da kuma tsarin bin doka da oda.
2.TASIRIN WANNAN MATAKI GA ZAMAN LAFIYA
kasancewar Sa babban Jagoran Addini Mai mabiya milyoyi,
tsare Malam ba tare da fayyace Gaskiyar lamarin ba Yana Haifar da Fargaba,
Damuwa,da fushin Al'ummar muslumi,dalibansa,da iyalanshi .muna Kira da Gwamnati da tayi La'akari da tasirin wannan lamari Ga Zaman LAFIYA da jituwar Addinin A kasa.
3.GAME DA ZARGI DA AKE MASA
Duk da muna Sane da Zargin da ake Yi na karbar kudi Wanda aka Tura a Account dinsa Domin Gabatar da Addu'oi,Wannan lamari ne Wanda ya Shafi mu'amala ta Addini da ta mutum da Mutum muna JADDADA cewa Dole ne A bi hanyoyin Shari,a wajen Tabbatar da Adalci .
Idan Har akwai tuhuma ta Gaskiya ,kamata yayi a Gabatar da ita a Fili a Gaban Kotu.
BUKATAR MU
1.sakin Sa Cikin Gaggawa:
Ganin cewa shehin malamin Ya Amsa Gayyatar hukumomi da Kansa ,Wanda Hakan ke Nu