Katsina State Hisbah Board, Batagarawa Division.

Katsina State Hisbah Board, Batagarawa Division. Katsina State Hisbah Board, Batagarawa Division

17/07/2026

morning Morale �

KATSINA STATE HISBAH BOARDBATAGARAWA DIVISIONHON. MURTALA USMAN BANYE YA GWANGWAJE HUKUMAR HISBAH TA ƘANANAN HUKUMOMIN R...
13/07/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD
BATAGARAWA DIVISION

HON. MURTALA USMAN BANYE YA GWANGWAJE HUKUMAR HISBAH TA ƘANANAN HUKUMOMIN RIMI, CHARANCHI, ƁATAGARAWA DA TALLAFIN BABURA

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓun Rimi, Charanchi da Ɓatagarawa, Hon. Murtala Usman Banye, ya bai wa kwamandojin Hukumar Hisbah na Ƙananan Hukumomin Rimi, Charanchi, Batagarawa tallafin babura uku domin ƙarfafa ayyukansu na horo da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna, tare da sauƙaƙa musu zirga-zirga wajen gudanar da ayyukan hukuma.

An gudanar da miƙa baburan ne da yammacin ranar Lahadi, 12 ga Yuli, 2026. Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Malam Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), shi ne ya jagoranci karɓar baburan tare da kwamandojin Hukumar Hisbah na ƙananan hukumomin Rimi, Charanchi da Ɓatagarawa.

Wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin Hon. Murtala Usman Banye na ƙarfafa hukumomin da ke aiki wajen tabbatar da kyawawan ɗabi'u, zaman lafiya da bin koyarwar addinin Musulunci a tsakanin al'umma.

Shugaban Hukumar na Batagarawa DC Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Hon. Murtala Usman Banye bisa wannan karamci, tare da bayyana cewa tallafin zai taimaka ƙwarai wajen inganta ayyukan jami'an Hisbah a faɗin ƙananan hukumomin.

Hukumar ta kuma yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima da dacewa wajen ci gaba da yi wa al'ummarsa hidima.

Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit, KTSHB Batagarawa Division
28 Muharram, 1448 | 12 July, 2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,BATAGARAWA DIVISIONHUKUMAR HISBAH TA ƘARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA YI NASARAR CAFKE MASU AIKA...
12/07/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,
BATAGARAWA DIVISION

HUKUMAR HISBAH TA ƘARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA YI NASARAR CAFKE MASU AIKATA LALATA A GARIN AJIWA

A ranar Talata 7 ga watan Yuli 2026, wanda ya yi daidai da 23 ga watan Muharram, 1448, Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Batagarawa, ƙarƙashin jagorancin DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, ta samu nasarar cafke wasu da ake zargi da aikata lalata a garin Ajiwa bayan tashi daga kasuwa a ranar Talata.

Samamen ya gudana ne bayan da hukumar ta samu sahihan bayanan sirri dangane da ayyukan da ake zargin suna gudana a yankin. Bayan gudanar da bincike da sanya ido, jami'an Hisbah s**a kai samame inda s**a yi nasarar cafke waɗanda ake zargi suna aikata wannan mummunan aiki.

Bayan cafke su, an gudanar da bincike na farko, inda waɗanda ake zargin s**a amsa laifuffukan da ake tuhumar su da su. DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza ya yi musu nasiha mai ratsa zuciya tare da tunatar da su illar alfasha ga mutum da al'umma baki ɗaya. Haka kuma, hukumar ta ɗauki matakan da s**a dace bisa tanadin doka kafin mika su ga iyayensu ko masu kula da su domin ci gaba da bibiyar lamarin.

Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Batagarawa tana ƙara kira ga al'umma da su ci gaba da ba ta haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan duk wani abu da zai iya kawo barazana ga tarbiyya, zaman lafiya da kyawawan ɗabi'u a cikin al'umma. Hukumar ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da duk wani nau'in saɓon doka da lalata domin tabbatar da ingantacciyar tarbiyya da zaman lafiya.

Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit, KTSHB Batagarawa Division
12 July, 2026 | 28 Muharram, 1448

06/06/2026
KATSINA STATE HISBAH BOARD,BATAGARAWA DIVISION.KWAMANDAN HISBAH YA ZIYARCI DUKKAN GIDAJEN SAUKAN BAƘI DA KE ƘARƘASHIN ƘA...
06/06/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,
BATAGARAWA DIVISION.

KWAMANDAN HISBAH YA ZIYARCI DUKKAN GIDAJEN SAUKAN BAƘI DA KE ƘARƘASHIN ƘARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA

A ranar Alhamis, 4 ga Yuni, 2026, wanda ya yi daidai da 18 ga Zul-Hijjah, 1447AH, Kwamandan Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Batagarawa, DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, ya jagoranci wata tawagarsa domin gudanar da ziyarar gani da ido a dukkan gidajen saukan baƙi (Hotels) guda tara (9) da ke faɗin ƙaramar hukumar Batagarawa.

Tawagar ta haɗa da Mataimakin Kwamandan (ADC Special Services), Mal. Kabir Umar Sani da Sakataren Hukumar, Malam Abdullahi Yusuf Dandagoro, tare da sauran jami'an gudanarwa da shugabannin Outposts na ƙaramar hukumar.

Gidajen saukan baƙin da aka ziyarta sun haɗa da:

1. Jakada Hotel
2. Shalele Hotel
3. Fa'eez Hotel
4. Hayat Hotel
5. Liyafa Palace Hotel
6. Green View Hotel
7. Jamvaali Hotel
8. Murjani Hotel
9. Kaita Guest Inn

A yayin ziyarar, Kwamandan ya tattauna da manajojin waɗannan wurare tare da jaddada muhimmancin bin dokoki da ƙa'idojin Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina. Haka kuma ya yi amfani da damar wajen tunasar da su nauyin da ke kansu na tabbatar da kyawawan ɗabi'u, tsaftar muhalli da kuma kare al'umma daga duk wani abu da zai iya zama barazana ga tarbiyya da zaman lafiya.

Kwamandan ya bayyana cewa Hukumar Hisbah za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gina al'umma mai nagarta, tsaro da kyawawan halaye, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A nasu ɓangaren, manajojin gidajen saukan baƙin sun nuna matuƙar farin ciki da wannan ziyara, tare da bayyana godiyarsu ga Hukumar Hisbah bisa ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da zaman lafiya da ingantacciyar tarbiyya a cikin al'umma.

Sun kuma sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da ba hukumar cikakken haɗin kai tare da kiyaye dokoki da ƙa'idojin da s**a dace.

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina tana kira ga daukacin al'umma da su ci gaba da bayar da gudunmawa da haɗin kai domin yaƙi da munanan ɗabi'u da duk wani nau'in ɓarna, domin samun al'umma mai cike da tsaro, zaman lafiya da ci gaba.

Allah SWT Ya ƙara wa Hukumar Hisbah ƙarfi da basira wajen sauke nauyin da aka ɗora mata na umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna.

Abdullahi Salihu Almujawwid, ASH
ICT Unit, KTSHB Batagarawa Division
20 Dhul-Hijjah, 1447AH | 06 June, 2026

06/06/2026

KWAMANDAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA YA ZIYARCI DUKKAN GIDAJEN SAUKAN BAƘI 9 DA KE BATAGARAWA

🕌 *SANARWAR DAWOWAR KARATUTTUKAN IMAM SALIHU ALHASSAN*Alhamdulillah, muna sanar da daukacin 'yan uwa musulmi cewa za a c...
04/06/2026

🕌 *SANARWAR DAWOWAR KARATUTTUKAN IMAM SALIHU ALHASSAN*

Alhamdulillah, muna sanar da daukacin 'yan uwa musulmi cewa za a ci gaba da gudanar da karatuttukan Imam Salihu Alhassan kamar yadda aka saba.

📖 Karatun Tsakanin Magrib zuwa Isha'i – a dukkan masallatai.

📚 Karatuttukan Zaure da sauran majalisun ilimi za su ci gaba a Masallacin Khalid Bin Walid, Dandagoro kamar haka:

• Bayan Asuba – Asabar da Lahadi
• Bayan Asuba – Alhamis
• Bayan Isha'i – Zauren Karatun Magidanta (Asabar da Lahadi)
• Bayan Isha'i – Zauren Karatun Ɗaliban Ilimi (Litinin da Talata)
• Bayan La'asar – Musaffar Alƙur'ani (Juma'a)

📅 Za a dawo daga yau Laraba, 03/06/2026.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya albarka a cikin wannan majalisar ilimi, Ya amfanar da mu da abin da za mu koya, Ya sanya shi hujja gare mu ba hujja a kanmu ba.

Sanarwa:
*Abdullahi Salihu Almujawwid*
07066862942 || 09126961553

Manufar Hisbah
09/04/2026

Manufar Hisbah




Gyara Kayan Ka...
30/03/2026

Gyara Kayan Ka...




KATSINA STATE HISBAH BOARD,BATAGARAWA DIVISION.​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA CAFKE WASU MATASA MASU K...
21/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,
BATAGARAWA DIVISION.

​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA CAFKE WASU MATASA MASU KITSO A RANAR SALLAH

​Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa, ƙarƙashin jagorancin DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, ta samu nasarar cafke wasu matasa 2 da kitse kansu bayan kammala sallar Idi.

Hakan ya auku ne a jiya Juma'a, 01 ga watan Shawwal, 1447 (daidai da 21 ga watan Maris, 2026) bayan kammala sallar Idi jami'an Hukumar s**a yi arba da waɗannan matasa guda da kitso a kansu. Jami'an sun garzaya da su a Ofishin Hukumar domin hukunta su.

An umurci matasan biyu da su kwance wa juna kitson, inda daga baya aka aske kawunansu a matsayin hukunci, bayan daga bisa DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza ya jagoranci yi masu nasiha, jan hankali da gargaɗi akan wannan aiki na su da s**a aikata.

Daga karshe, an nemo Matan da s**a yi masu kitson kuma an yi masu hukuncin da ya kamata.

Hukumar Hisbah na yi wa daukacin al'ummar musulmi barka da sallah, da fatan yin shagulgulan sallah cikin aminci, tare da guje wa saɓon Allah a yayin gudanar da shagulgulan.

​Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
02 Shawwal, 1447 | 21 March, 2026

Address

Batagarawa Low-cost
Batagarawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina State Hisbah Board, Batagarawa Division. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share