Batagarawa Local Government, Katsina State Hisbah Board

Batagarawa Local Government, Katsina State Hisbah Board Katsina State Hisbah Board Batagarawa Local Government Division

Manufar Hisbah
09/04/2026

Manufar Hisbah




Gyara Kayan Ka...
30/03/2026

Gyara Kayan Ka...




KATSINA STATE HISBAH BOARD,BATAGARAWA DIVISION.​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA CAFKE WASU MATASA MASU K...
21/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,
BATAGARAWA DIVISION.

​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA CAFKE WASU MATASA MASU KITSO A RANAR SALLAH

​Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa, ƙarƙashin jagorancin DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, ta samu nasarar cafke wasu matasa 2 da kitse kansu bayan kammala sallar Idi.

Hakan ya auku ne a jiya Juma'a, 01 ga watan Shawwal, 1447 (daidai da 21 ga watan Maris, 2026) bayan kammala sallar Idi jami'an Hukumar s**a yi arba da waɗannan matasa guda da kitso a kansu. Jami'an sun garzaya da su a Ofishin Hukumar domin hukunta su.

An umurci matasan biyu da su kwance wa juna kitson, inda daga baya aka aske kawunansu a matsayin hukunci, bayan daga bisa DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza ya jagoranci yi masu nasiha, jan hankali da gargaɗi akan wannan aiki na su da s**a aikata.

Daga karshe, an nemo Matan da s**a yi masu kitson kuma an yi masu hukuncin da ya k**ata.

Hukumar Hisbah na yi wa daukacin al'ummar musulmi barka da sallah, da fatan yin shagulgulan sallah cikin aminci, tare da guje wa saɓon Allah a yayin gudanar da shagulgulan.

​Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
02 Shawwal, 1447 | 21 March, 2026

Hotuna:- Yadda Kwamandan Hukumar Hisbah na karamar Hukumar Batagarawa ya gabatar da sallar Idi a filin makarantar Firama...
21/03/2026

Hotuna:- Yadda Kwamandan Hukumar Hisbah na karamar Hukumar Batagarawa ya gabatar da sallar Idi a filin makarantar Firamare ta Kafin Rabo, Dandagoro

Jiya Juma'a 01 ga watan Shawwal 1447, wanda ya yi daidai da 20 ga watan Maris 2026, DC Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza ya gabatar da Sallar Idi karama a Filin Sallar Idi na makarantar Firamare ta Kafin rabo da ke Dandagoro.

Bayan kammala sallar, shugaban ya gabatarwa jami'an Hukumar jawabai na faɗakarwa, tunatarwa da jan hankali, tare da fatan alheri da Barka da Sallah ga daukacin al'ummar musulmi.

Allah SWT ya karbi ibada, Allah SWT ya maimaita mana.

📸 Photo Credit:
Muhammad Jamilu

Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit, KTSHB Batagarawa Division
02 Shawwal, 1447 - 21 March 2026

Barka da Salla daga DC Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza
20/03/2026

Barka da Salla daga DC Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza

KATSINA STATE HISBAH BOARD,BATAGARAWA DIVISION​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA CAFKE WASU MASU SHAYE-SHA...
15/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,
BATAGARAWA DIVISION

​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA CAFKE WASU MASU SHAYE-SHAYE CIKIN UNGUWA A GOMAN KARSHE NA WATAN RAMADAN

​Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa, ƙarƙashin jagorancin DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, ta samu nasarar cafke wasu mutane 3 da yin shaye-shaye a cikin unguwa a kwanaki goman ƙarshe na watan Ramadan.

Hakan ya auku ne a jiya Asabar, 25 ga watan Ramadan, 1447 (daidai da 14 ga watan Maris, 2026) da dare bayan samame da jami'an hukumar s**akai. Bayan bincike da rahoto daga bakin masu laifin da aka k**a, biyu daga cikinsu suna da shekaru sama da 40, yayin da ɗayan yake da shekaru 20 kacal a duniya.

Bayan hukunci da s**a karɓa daga jami'an Hukumar ƙarƙashin jagorancin DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, DC yayi masu nasiha, jan hankali tare da kashedi bayan ya ambata masu irin tarin alherin da ke cikin aikata ayyukan alheri a goman karshen wannan wata na Ramadan, kuma sun tabbatar wa Hukumar cewa ba za a sake samun su da aikata wannan aiki ba, a ciki ko wajen wannan wata mai alfarma, tare da nuna godiyarsu ga Hisbah da jami'an ta.

Manufar Hukumar Hisbah shi ne tsaftace al'umma daga aikata ayyukan da Allah SWT ba ya so, da kuma nusanshe su abin da Allah SWT ke so kuma ya yarda da shi.

​Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
26 Ramadan, 1447 | 15 March, 2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,BATAGARAWA DIVISION​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA YI NASARAR CAFKE MASU AIK...
14/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD,
BATAGARAWA DIVISION

​HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA YI NASARAR CAFKE MASU AIKATA LALATA DA KETARE HADDI A WATAN RAMADAN

​Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa, ƙarƙashin jagorancin DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza, ta samu nasarar cafke wani saurayi da budurwa waɗanda aka samu da laifin yin lalata a cikin wani otal (hotel) da ke yankin.

Lamarin ya auku ne a jiya Juma'a, 24 ga watan Ramadan, 1447 (daidai da 13 ga watan Maris, 2026). Binciken farko ya nuna cewa budurwar ta ziyarci gidan su saurayin ne da sunan kai musu "kayan buɗe baki", sai dai daga bisani s**a yanke shawarar wucewa zuwa otal domin aikata wannan mummunan aiki na saɓon Ubangiji, musamman a cikin wannan wata mai alfarma.

Bayan samun rahoton da kuma cafke su, masu laifin sun amsa laifinsu filla-filla a gaban hukuma. DC Malam Sadiq Ibrahim Gyaza ya gudanar da tsauraran tambayoyi, inda daga bisani ya yi musu nasiha mai ratsa jiki da jan hankali game da illar alfasha. Hukumar ta tabbatar da yi musu kashedi mai tsanani tare da aiwatar da hukuncin da ya dace a kansu kafin mika su ga iyalansu.

​Hukumar Hisbah za ta ci gaba da kasancewa mai sanya ido da tabbatar da tarbiyya da kare mutuncin al'umma a kowane lokaci k**ar yadda doka ta tanada.

​Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
25 Ramadan, 1447 | 14 March, 2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD, BATAGARAWA DIVISION.HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA YI NASARAR CAFKE WANI MU...
13/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD, BATAGARAWA DIVISION.

HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA YI NASARAR CAFKE WANI MUTUM DA YA YI YUNKURIN LALATA DA WATA MATA DA SUNAN TAIMAKON KAYAN SALLAH

Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa karkashin jagorancin Kwamanda Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza ta samu nasarar yin ram da wani mutum wanda ake zargi da yunkurin yaudarar wata mata da nufin yin lalata da ita.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya yi alkawarin dinkawa matar da ƴaƴanta kayan Sallah, inda ya yi amfani da wannan damar wajen neman ta da lalata. Cikin ikon Allah Hukumar Hisbah ta samu rahoto kafin abin ya faru.

Bayan samun rahoto, dakarun Hisbah sun bi diddigin lamarin inda aka yi nasarar cafke wanda ake zargin a kafin ya aiwatar da wannan mummunan nufi nasa.

Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza ya yaba wa matar bisa jarumtar da ta nuna na kin amincewa da mika mutuncinta domin abin duniya, ya kuma ƙara da yi masu nasiha su biyun. Haka kuma, yana jan kunnen al'umma musamman mata da su kiyayi masu yaudara da sunan taimako.

Hukumar Hisbah za ta ci gaba da tabbatar da tarbiyya da kare mutuncin al'umma k**ar yadda doka ta tanada.

Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
24 Ramadan, 1447 - 13 March 2026

KATSINA STATE HISBAH BOARDBATAGARAWA DIVISION.SANARWAR ALHININ RASUWAR MAHAIFIN JAMI'INMU (ASH JAMILU ISMA'IL)Hukumar Hi...
13/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD
BATAGARAWA DIVISION.

SANARWAR ALHININ RASUWAR MAHAIFIN JAMI'INMU (ASH JAMILU ISMA'IL)

Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa, karkashin jagorancin Kwamanda Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza tana mika sakon ta'aziyya da alhini ga jami'inmu, ASH Jamilu Isma'il, bisa rasuwar mahaifinsa da ta auku.

An gudanar da jana'izar mamacin tun jiya k**ar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kwamandan Hisbah, a madadin daukacin jami'an hukumar, yana addu'ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa mamacin, ya sanya aljanna ce makomarsa, sannan ya ba iyali da abokan arziki juriyar wannan babban rashi. Muna rokon Allah ya sa dacewar gidan gaskiya ya fi masa na duniya.

Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
24 Ramadan 1447 - 13 March 2026

KATSINA STATE HISBAH BOARDBATAGARAWA DIVISIONHUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA TSINCI YARA MATA BIYU KUMA ...
08/03/2026

KATSINA STATE HISBAH BOARD
BATAGARAWA DIVISION

HUKUMAR HISBAH TA KARAMAR HUKUMAR BATAGARAWA TA TSINCI YARA MATA BIYU KUMA TA MAYAR DA SU GA IYAYENSU.

Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Batagarawa ƙarƙashin jagorancin Kwamandanta Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza ta tsinci yara mata guda biyu da suke ƙoƙarin komawa gida gab da lokacin shan ruwa a ranar 06 ga watan Maris 2026.

Bayan tambayoyi da aka yi wa yaran sun tabbatar da cewa ɗayar su ce ta gayyaci ɗayar domin su je wurin mahaifiyarta daga garin Rimaye zuwa Dandagoro, duk da cewar ita ma bata san wurin da mahaifiyar tata take ba.

Daga karshe an yi nasarar gano mahaifan yaran kuma aka haɗa su da su, bayan da Kwamandan Mal. Sadiq Ibrahim Gyaza yayi masu gargaɗi game da fita gida ba tare da sanin iyayensu, sannan ya bayyana masu cewa idan s**a ƙara aikata hakan Hukumar Hisbah za ta Hukunta su.

Abdullahi Salihu Almujawwid
ICT Unit KTSHB Batagarawa Division
18 Ramadan 1447 - 07 March 2026

🔊  *SANARWAR MUHADARORIN RAMADAN NA (MATA)*🔊📍 *_Khalid Bn Walid Foundation_*A madadin wanann cibiya mai suna a sama muna...
06/03/2026

🔊 *SANARWAR MUHADARORIN RAMADAN NA (MATA)*🔊

📍 *_Khalid Bn Walid Foundation_*

A madadin wanann cibiya mai suna a sama muna farin cikin sanarwa tare da gayyatar yan uwa musulmi (Mata),zuwa wajen Muhadara daya shirya kuma za ta gudana insha Allah k**ar haka:

*Maudu'i*
📌 _*SIYASA DA MUSULUNCI*_.

*_Malami mai Gabatarwa:_*
📌 *Mal. Nura Gwanda Aliyu*

*_Rana:_*
📌Asabar
18 Ramadan,1447
07-03-2026

*_Lokaci:_*
📌Karfe 10:00am (Na safe)

*_Wuri:_*
📌Masallacin Juma'a na Usamatu Bn Zaid,Sabuwar Unguwa Dandagoro Katsina

✅ *_MAHALARTA_*
👉 Mata

✅Ku kasance da shafin Facebook na Jibwis Dandagoro domin kallon karatukan kai tsaye(Live) Insha Allah ta wannan link din.

🔵Facebook
👇👇👇👇👇
https://www.facebook.com/jibwisdandagoromedia/

✅Ko Sauke Audio a zaurukanmu na WhatsApp ko Telegram ta wadannan links din.

🟢WhatsApp
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/I1EMVH6DtO76VZpSR9reBt

🟦Telegram
👇👇👇👇👇👇👇
https://t.me/joinchat/FGDPxdyJD3UxZmNk

*Allah ya amfanar damu da abinda ake karantar da seemu,Ameeeeen*

*_JIBWIS DANDAGORO_*
17 Ramadan,1447
06-03-2026

🔊  *SANARWAR MUHADARORIN RAMADAN NA (MATA)*🔊📍 *_Khalid Bn Walid Foundation_*A madadin wanann cibiya mai suna a sama muna...
27/02/2026

🔊 *SANARWAR MUHADARORIN RAMADAN NA (MATA)*🔊

📍 *_Khalid Bn Walid Foundation_*

A madadin wanann cibiya mai suna a sama muna farin cikin sanarwa tare da gayyatar yan uwa musulmi (Mata),zuwa wajen Muhadara daya shirya kuma za ta gudana insha Allah k**ar haka:

*Maudu'i*
📌 _*MUHIMMANCIN CIYAR DA DUKIYA FISABILILLAH CIKIN WATAN RAMADAN*_.

*_Malami mai Gabatarwa:_*
📌 *Sheikh Dr Aminu Usman Abu Ammar (Hafizahullah)*

*_Rana:_*
📌Asabar
11 Ramadan,1447
28-02-2026

*_Lokaci:_*
📌Karfe 09:30am (Na safe)

*_Wuri:_*
📌Masallacin Juma'a na Usamatu Bn Zaid,Sabuwar Unguwa Dandagoro Katsina

✅ *_MAHALARTA_*
👉 Mata

✅Ku kasance da shafin Facebook na Jibwis Dandagoro domin kallon karatukan kai tsaye(Live) Insha Allah ta wannan link din.

🔵Facebook
👇👇👇👇👇
https://www.facebook.com/jibwisdandagoromedia/

✅Ko Sauke Audio a zaurukanmu na WhatsApp ko Telegram ta wadannan links din.

🟢WhatsApp
👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/I1EMVH6DtO76VZpSR9reBt

🟦Telegram
👇👇👇👇👇👇👇
https://t.me/joinchat/FGDPxdyJD3UxZmNk

*Allah ya amfanar damu da abinda ake karantar da seemu,Ameeeeen*

*_JIBWIS DANDAGORO_*
10 Ramadan,1447
27-02-2026

Address

Batagarawa Low-cost
Batagarawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Batagarawa Local Government, Katsina State Hisbah Board posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share