Da'iratul Abna'ul Faidhati ibrahimiyya

Da'iratul Abna'ul Faidhati ibrahimiyya Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Da'iratul Abna'ul Faidhati ibrahimiyya, Religious organisation, Abuja.

08/09/2025
Umarnin Da Ubangiji Yaiwa Banu Isra'ila Na Gode Masa Bisa Wasu Ni'imomi Da Yai Musu Tare Da Tuna Yininnikan Da Akai Musu...
08/09/2025

Umarnin Da Ubangiji Yaiwa Banu Isra'ila Na Gode Masa Bisa Wasu Ni'imomi Da Yai Musu Tare Da Tuna Yininnikan Da Akai Musu Wancanenka Ni'imah A Ciki Yana Wajabta Mana Mu Al'ummar Sayyiduna Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Tunawa Da Yinin Haihuwar Shugaba Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Da Godewa Ubangijin Sa Bisa Ni'imar Samun Sa Da Musuluncin Da Yazo Mana Da Shi

A Cikin Al'ƙura'ni Mai Mai Girma Cikin Suratu Ibrahim Ubangiji Ya Gayawa Annabi Musa Alaihissalam Cewa:

"وذكرهم بأيام الله" "Ka Tunatar Da Su Yininnikan Ubangiji"

Ma'ana Ya Tunatar Da Su Kwanukansu Na Shan Wahala A Hannun Fir'auna Da Kuma Kwanukan Tsiransu Daga Azabtarwarsa Da Kuma Samun Ni'imomin Ubangiji Kalakala Ta Dalilin Samuwar Annabi Musa Cikin Su Da Sallamawarsu Da Soyayyar Su Gare Shi Sannan Su Godewa Ubangiji Akan Haka

Ni'imar Samun Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Da Littafin Sa Ta Fifici Ni'imar Samun Annabi Musa Alaihissalam Da Littafin Sa Kamar Yadda Al'ummar Sa Ta Fifici Dukkan Al'ummu A Wajen Ubangiji

Wannan A'ya Ta Ishi Ma'abota Imani Da Hankali Yin Maulidin Maulana Rasululallahi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam

Murabbi Ismail Mustapha-Kadai
Chief Imam Of Kokosa, Karshi,Karu Local Government Nasarawa State & Chairman Fityanul Islam Of Nigeria Abuja Fct Branch

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Da'iratul Abna'ul Faidhati ibrahimiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share