21/06/2015
** DUNIYAR MUTUWA **
FITOWA TA 7
Bayan wucewar su (Munkar da Nakir) sai na soma jin wani zafi a qabarina, jikina ya soma makyarkyata, naji tsoron kada ace qofar wuta aka bude saboda tsananin zafi, amma ba abinda nake ji illa tsananin zafi wanda ke fitowa daga jikina.
Chan sai wasu Malaa'iku 2 sukazo min, sukace:
Assalamu Alaikum wr wb
Nace: Wa'alaikumus-salaam wr wb
Sukace: Mu malaa'ikune, munzo nuna maka aikinka a qabarinka, da kuma tattara kyawawan ayyukanka da ake maka kyautarsu daga nan har ranar qiyaamah.
Nace dasu: wallahi tunda na mutu nake ganin ababen tsoro, ban zaci haka abin yake da tsanani ba! Amma zaku amincemin nayi muku tambaya? Sukace Eh!
Nace: shin ina cikin Yan-Aljannah? Bayan duk wannan abubuwa da nasha, shin akwai wani abu da zai iya sanyawa Allah ya saani a wuta?
Sai sukace: kai Musulmi ne, abinda ya sameka, don kayi Imani da Allah Manzonsa ne,
Amam shiga Aljannah ko wuta, ba wanda yasanshi sai Allah, saidai muna so ka sa a ranka cewa: koda Allah ya sanyaka a wuta, to bazaka dauwama a cikinta ba, domin baka shirka, kana kadaita Allah!
Sai na soma kuka nace: To idan Allah ya sanya ni a wuta, kwana nawa zanyi cikinta?
Sukace: ka kyautata zato ga Ubangijinka kawai, kuma ka sani, shi mai karamci ne!
Don haka yanzu zamu soma nuna maka ayyukanka, tun daga sanda ka Balaga har zuwa qarshen numfashin ka a inda kukai hatsari!
Kuma zamu soma ne da sallarka, domin itace bambancin Musulmi da Kafiri!
Amma ka sani, duk wani aiki na kwarai da kayi bazaka ga sakamakon su ba, domin ayyukanka na qwarai dukkansu an sagale maka su!!!
Sai nace cikin mamaki: me yasa?
Kuma menene alaqar wannan da zaafinda nakeji kamar an tattaro zazzabin duniya an taara min a jikina??
Sukace: wannan na da Alaqa da abinda kakeji, saboda sakacinka wajen biyan baashinda ake binka na kudade da kaayayyaki! Kuma yanzu kana cikin Hatsari babba!!!
Nace cikin kuka: Ya za'ai kenan? Yanzu Bashi shine yasa aka tsaremin Ayyukana? Kuma nakejin wannan tsananin zaafin?
Sukace: Tabbas kuwa!!!
Yan uwa sai kuyi tunani, Mu gyara kafin lokaci ya qure mana!!!
Don jin cigaba
Mu hadu a fitowa ta 8
Yours in Islam NURA SANI MAGAJI