First Aid Group Of Jibwis Nigeria

First Aid Group Of Jibwis Nigeria First Aid Group Of Jibwis Nigeria
(1)

International Conference Abuja 2026First Aid Group Of JIBWIS Nigeria  National Duty
14/08/2026

International Conference Abuja 2026

First Aid Group Of JIBWIS Nigeria
National Duty

12/08/2026

First Aid Group Of Jibwis Nigeria

VIDEO: AL-AMIN IBRAHIM

Hotuna: Jibwis Nigeria ta bude babban taro a majalisar Musulunci ta Duniya tare da hadin gwuiwar Rabidah a dakin taro na...
11/08/2026

Hotuna: Jibwis Nigeria ta bude babban taro a majalisar Musulunci ta Duniya tare da hadin gwuiwar Rabidah a dakin taro na Bola tunibu international conference centre Abuja.




First Aid Group Of Jibwis Nigeria

07/08/2026

Jibwis Nigeria
Shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a madadin kungiyar da haɗin gwuiwar kungiyar Haɗa kan Musulmai ta duniya (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY, na gayyatar Al'ummar musulmi zuwa gagarumin taron ƙarawa juna ilimi mai taken 'BAMBANCE BAMBANCE TARE DA ZAMAN LAFIYAR JAMA’A”

Taron wanda 'HAƊIN GUIWA NE TSAKANIN KUNGIYAR HAƊA KAN MUSULULMAI TA DUNIYA, MAI CIBIYA A ƘASAR SAUDIYYA (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY DA ƘUNGIYAR WA'AZIN MUSULUNCI TA KASAR NAJERIYA, JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA IKAMATIS SUNNAH.

-Za a buɗe taron conference ranar talata 11/August/2026 da misalin karfe tara na safe (9:00am) a kuma gama ranar laraba 12/August/2026 da rana 2:30pm.

-Za'a gabatar da Wa'azin kasa a harabar Masallacin JIBWIS dake helkwatar kungiyar a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja, daga yammacin laraba har zuwa daren alhamis.

-Safiyar alhamis 14/August/2026 kuma sai jama'a su koma garuruwansu.

Babban bako na Musamman, Shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Ahmad Bola Tunibu.

Uban Taro: Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad

Sauran manyan Baki sun haɗa da:
Gwamnoni Ministoci, Yan majalisu na tarayya da na jahohi, Iyaye Maluma, Sarakuna, yan kasuwa da sauran yan uwa musulmi dake fadin Naijeriya da sauran ƙasashen ketare.

Ana sa ran halartar manyan bakin Malamai daga manyan ƙasashen duniya insha Allah.

Sanarwa daga Sakataren JIBWIS' na ƙasa Sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe, ta ofishin kwamitin Labaru na babban taron.

Jibwis Nigeria

First Aid Group of Jibwis Nigeria  Ikhlasi, Cikar Uniform da kula da tsaftace uniform, Bin Doka da bin tsarin majalisar ...
06/08/2026

First Aid Group of Jibwis Nigeria
Ikhlasi, Cikar Uniform da kula da tsaftace uniform, Bin Doka da bin tsarin majalisar Agaji sune ginshikin samun nasarar mu a wannan Aiki mai Albarka.

Bugu da kari kuwa, Hakuri, Juriya da mai da hankali akan Aikin manyan turaku ne a tafiyar Aikin.

Mu cigaba da bada irin tamu gudummawar domin cigaban Addinin Musulunci da Ɗaukaka Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)

First Aid Group of Jibwis Nigeria
Daga: karantaswar Agaji Haɗin kai da Taimakon Juna
22 Safar, 1448
5 August, 2026

Assalamu AlaikumFirst Aid Group Of JIBWIS Katsina State Directorate.GAYYATAR DAURIN AURE!  Daraktan Agaji na jihar Katsi...
28/07/2026

Assalamu Alaikum
First Aid Group Of JIBWIS Katsina State Directorate.

GAYYATAR DAURIN AURE!

Daraktan Agaji na jihar Katsina Alhaji Garba Magaji Galadima a madadin Majalissar Zartarwa ta jiha da kuma Yan-Agajin jihar Katsina kwata na farin cikin gayyatar dukkan yan Agaji da abokan Arziki zuwa wajen Daurin Auran Dan gidan Alhaji Surajo Maida Agaji (State Discipline Officer) Malam Safwan Surajo Agaji.

kamar haka:
Ranar Juma'a 31/7/2026,
Lokaci: 3:00pm.
Wuri: Sabuwar Unguwa Wurin Magama Restaurant, Santar Ama Shopping Mall Katsina State

Allah ya bada ikon zuwa, Allah ya sama wannan Aure Albarka, Amin.
Ga wadanda basu sami damar halattaba ana bukatar Addu'o'inku na fatan Alkhairi.

✍️ Abubakar Idris Funtua
(State S.A Media ||, F.A.G Of JIBWIS Katsina State Directorate)
27/7/2026

First Aid Group of Jibwis Nigeria Taron kasashen Duniya haɗin Gwiwar Jibwis Nigeria/Rabiɗa ta Duniya akan cigaban Addini...
26/07/2026

First Aid Group of Jibwis Nigeria
Taron kasashen Duniya haɗin Gwiwar Jibwis Nigeria/Rabiɗa ta Duniya akan cigaban Addinin Musulunci.

International conference Jibwis Nigeria 11-12 August, 2026

Ba'a saukewa dukkan ɗan Agaji ba na ƙasashen Afrika. 'Yan Kuyi dandazon shigowa Abuja domin bada irin taku gudummawa.

first Aid Group of Jibwis Nigeria
26 July, 2026

26/07/2026

First Aid Group of JIBWIS Nigeria

First Aid Group of Jibwis Nigeria TARON MAJALISAR AGAJI TA ƘASA (JIBWIS NIGERIA) A GARIN SULEJA JIHAR NIGER  Majalisar  ...
26/07/2026

First Aid Group of Jibwis Nigeria
TARON MAJALISAR AGAJI TA ƘASA (JIBWIS NIGERIA) A GARIN SULEJA JIHAR NIGER

Majalisar Agajin Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta Ƙasa ta gudanar da taron ta na ƙasa a juma'ar da ta gabata a garin suleja ta jahar Niger a Najeriya. Taron wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin Daraktan Majalisar Agaji ta Ƙasa, Engr. Mustapha Imam Sitti.
Wakilai akalla mutum 70 daga jihohi 36 na Tarayyar Najeriya tare da wakilan kasa (National Officeer) mutum 52 tare da Babban Birnin Tarayya (Abuja) sun halarci wannan muhimmin taro.

A cikin taron, an tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi ci gaban ayyukan Majalisar Agaji da kuma ƙara inganta hidima ga al'umma, tare da ɗaukar muhimman shawarwari domin ci gaban aikin Agajin JIBWIS a faɗin ƙasa.

Allah Ya sanya albarka a cikin wannan taro, Ya ba da ikon aiwatar da dukkan kyawawan shawarwarin da aka cimma. Allah ya kai kowa Gida lafiya Amin

Jibwis Nigeria

MAJALISAR AGAJI TA GUDANAR DA TARO A GARIN SULEJA-JAHAR NIGER  Majalisar  Agajin Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sun...
26/07/2026

MAJALISAR AGAJI TA GUDANAR DA TARO A GARIN SULEJA-JAHAR NIGER

Majalisar Agajin Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta Ƙasa ta gudanar da taron ta na ƙasa a juma'ar da ta gabata a garin suleja ta jahar Niger a Najeriya. Taron wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin Daraktan Majalisar Agaji ta Ƙasa, Engr. Mustapha Imam Sitti.
Wakilai akalla mutum 70 daga jihohi 36 na Tarayyar Najeriya tare da wakilan ƙasa (National Officers) mutum 52 tare da Babban Birnin Tarayya (Abuja) sun halarci wannan muhimmin taro.

A cikin taron, an tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi ci gaban ayyukan Majalisar Agaji da kuma ƙara inganta hidima ga al'umma, tare da ɗaukar muhimman shawarwari domin ci gaban aikin Agajin JIBWIS a faɗin ƙasa.

Allah Ya sa albarka a cikin wannan taro, Yyaba da ikon aiwatar da dukkan kyawawan shawarwarin da aka cimma. Allah ya kai kowa Gida lafiya Amin

First Aid Group Of Jibwis Nigeria

Address

Utako Junction
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First Aid Group Of Jibwis Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share