26/07/2024
MU TASHI TSAYE AKAN BADA GUDUNMAWA DOMIN CIGABAN ADDININ MUSULUNCI
Ta hanyar Aikin Agaji ne hanya mafi mahimmanci wajen bada irin wannan gudunmuwa cikin tsafta da ingantaccen tsari bisa biyayyar shugabanci.
Ba karamar Nasara bace ga dukkan wanda ya tsinci kan sa a irin wannan Aiki na Agaji, ace kana matashi Amma rayuwar ka kacokan ta ta'allaqa akan ganin Muslunci yaci gaba, sannan kuma ka bada lokacin ka, ka sa Dukiyar ka, ka sa Ilimin ka, komin ruwa, komin zafi, komin sanyi da tsananin rayuwa, kai lalle in Sha Allah akwai Rabo mai tsoka a ranar gobe kiyama ga dukkan mai irin wannan Aiki.
Lalle yan Agaji mu kula da kan mu wajen gudun Aikata abinda bai dace ba, sannan kuma mu kara dagewa wajen kare darajar Muslunci da musulmai.
Muci gaba da gwagwarmayar bisa tsarin da Addinin Musulunci ya shar'anta da kuma bin Dokoki da Tsari bisa yadda shugabannin mu s**a tsara akan doron Alqur'ani da Hadisan Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam)
Lalle ne muyi biyayya ga iyayen mu, malaman mu, shugabannin mu bisa Tarbiyya Islamiyya.
Muna Rokon Allah ya maida mana kunci da tsanani ya koma sauki da walwala cikin sauki ba tare da tada yamutsi da rikici ba.
Allah ya bamu hakurin wannan yanayi da muke ciki na Jarrabawa akan rayuwa.
Allah ya sa kowanne musulmi ya zamo mai bin karantarwar manzon Rahama akan doron Alqur'ani da sunnah.
Barkammu da safiyar Juma'ah mai Albarka
Naku
Shehu A. Abdurrahman Shehu A.A Gashua