Hisbah development initiative Adamawa state command

Hisbah development initiative Adamawa state command HISBAH hani ga mummuna da kuma umarni da kyakkyawa bisa karantarwar Al-Qurani da Sunnah

Rundunar Hisbah Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Zuwa Ga Malama FatsumaRundunar Hisbah Development Initiative ta Jihar Adamawa t...
19/08/2026

Rundunar Hisbah Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Zuwa Ga Malama Fatsuma

Rundunar Hisbah Development Initiative ta Jihar Adamawa ta kai ziyarar ta’aziyya zuwa ga ɗaya daga cikin membobinta na Yola North Division, musamman a Wauru Jabbe Sub-Division, wato Malama Fatsuma, wadda take daga cikin iyaye mata da kuma Da’awah a ɓangaren mata na Rundunar Hisbah, bisa rasuwar mahaifiyarta.

A madadin Rundunar Hisbah Development Initiative ta Jihar Adamawa, muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga Malama Fatsuma da iyalanta baki ɗaya bisa wannan babban rashi da ya same su.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan marigayiyar, Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, Ya haskaka kabarinta, Ya kuma ba iyalanta da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban ƙalubale.

Haka nan muna roƙon Allah Ya kiyaye mana sauran iyaye, Ya ba su lafiya da tsawon rai cikin biyayya da imani. Allah Ya sa idan tamu ta zo, mu cika da imani, Ya sa ƙarshenmu ya zama kyakkyawan ƙarshe.

إنا لله وإنا إليه راجعون

Allah Ya jiƙan mamaciyar, Ya gafarta mata. Amin Ya Rabbal Alamin.

E-sign
Hisbah Media team

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHAlhamdulillah, a yau Alhamis, 23/07/2026, Hisbah Development Initiative (HDI)...
23/07/2026

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUH

Alhamdulillah, a yau Alhamis, 23/07/2026, Hisbah Development Initiative (HDI) Girei Division ta gudanar da ayyukanta na wa’azi da fadakarwa a Masallacin Jumu’a na Sangere.

Muna godiya ga Allah (SWT) da Ya ba mu ikon gudanar da wannan aiki na alheri cikin nasara. Allah Ya saka da alheri ga dukkan waɗanda s**a ba da gudummawa, s**a halarta, da kuma waɗanda suke ci gaba da tallafawa wannan aiki na kira zuwa ga alheri da hani daga mummuna.

🤲 Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ayyukanmu baki ɗaya, Ya sanya su cikin ma’aunin ayyukan alherinmu, Ya ƙara mana ƙarfi da ikhlasi wajen yi wa addininsa hidima. Ameen Ya Rabbal Alameen.

Hisbah Development Initiative (HDI)
Girei Division

📢 SANARWA GA MASU SHA’AWAR SHIGA AIKIN HISBAH A JIHAR ADAMAWAAna sanar da duk masu sha’awar shiga aikin HISBAH a Jihar A...
18/07/2026

📢 SANARWA GA MASU SHA’AWAR SHIGA AIKIN HISBAH A JIHAR ADAMAWA

Ana sanar da duk masu sha’awar shiga aikin HISBAH a Jihar Adamawa cewa ana karɓar bayanan masu neman shiga.

Duk mai sha’awa zai iya tuntuɓar mu ta hanyar kira ko tura saƙo (SMS/WhatsApp) zuwa wannan lamba:

📞 07040718715

Za a ba ku cikakken bayani game da tsarin shiga da sauran matakan da ake bi.

Allah Ya ba da sa’a.

DA’AWAH HISBAH DEVELOPMENT INITIATIVEGIREI DIVISIONA ranar Alhamis, 9 ga Yuli, 2026, Hukumar Hisbah Development Initiati...
10/07/2026

DA’AWAH HISBAH DEVELOPMENT INITIATIVE
GIREI DIVISION

A ranar Alhamis, 9 ga Yuli, 2026, Hukumar Hisbah Development Initiative Girei Division ta kai ziyarar da’awa zuwa Masallacin Jumu’a na Bajabure da ke Ƙaramar Hukumar Girei, Jihar Adamawa.

A yayin ziyarar, an gabatar da wa’azi mai cike da fa’ida wanda ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa guda biyu:

1. Illolin Hassada a Mahangar Musulunci, da kuma
2. Muhimmancin Girmama Shugabanni.

Wa’azin ya samu karɓuwa sosai daga al’ummar da s**a halarta, inda aka yi bayani kan yadda hassada ke lalata zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma, tare da jaddada wajibcin girmama shugabanni da bin umarninsu a cikin abin da ya dace da koyarwar addinin Musulunci.

Wa’azin ya gabata ne daga bakin Imam Ahmad Dalhatu Girei, wanda shi ne Chairman Da’awa, Central Zone.

Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka masa da alkhairi, Ya ƙara masa ilimi mai amfani, hikima da ƙarfin ci gaba da isar da saƙon addinin Musulunci. Allah Ya sa wannan wa’azi ya zama sanadin gyaran rayuwar al’umma baki ɗaya.

✍️ Ibrahim Babajo
Commander, Hisbah Development Initiative, Girei Division

BITAR HORAR DA SABBIN MEMBOBIN HISBAHAlhamdulillah.A yau, Rundunar Hisbah ta Jihar Adamawa, Central Zone, Yola North Div...
26/06/2026

BITAR HORAR DA SABBIN MEMBOBIN HISBAH

Alhamdulillah.

A yau, Rundunar Hisbah ta Jihar Adamawa, Central Zone, Yola North Division, ta samu nasarar gudanar da workshop (bita) ga sabbin membobinta na Hullere Detachment.

An gudanar da wannan bita ne domin ƙara wa sabbin membobin ilimi da fahimta kan ayyukan Hisbah, manufofinta, dokoki da ƙa’idojin aiki, tare da bayyana musu matsayin Hisbah a cikin al’umma da irin gudummawar da ake sa ran za su bayar wajen tabbatar da zaman lafiya, kyawawan ɗabi’u da bin doka.

Haka kuma, an yi wa mahalarta cikakken bayani kan makaman aiki (working tools) na jami’in Hisbah, hanyoyin gudanar da aiki cikin hikima da adalci, muhimmancin ladabi da kyakkyawar mu’amala da jama’a, da kuma yadda za su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da tsoron Allah.

Rundunar ta nuna jin daɗinta da yadda sabbin membobin s**a nuna himma, biyayya da sha’awar koyon aiki, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su kasance jakadu nagari na Hisbah a duk inda s**a samu kansu.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su ikon amfani da ilimin da s**a samu wajen yi wa addini da al’umma hidima, Ya sa wannan horo ya zama alheri ga rundunar Hisbah da daukacin al’ummar Jihar Adamawa.

Allah Ya ƙara ɗaukaka Hisbah, Ya ba ta nasara a dukkan ayyukanta. Amin.

E-sign
Hisbah Media and publicity

📢 SANARWAR NEMAN YARO DA YA BATAAna sanar da al’umma cewa wani yaro mai suna Shehi Mahmud, mai shekaru 14, ya bata tun j...
21/06/2026

📢 SANARWAR NEMAN YARO DA YA BATA

Ana sanar da al’umma cewa wani yaro mai suna Shehi Mahmud, mai shekaru 14, ya bata tun jiya da misalin karfe 3:30 na rana.

An gan shi na karshe a Bakin kasuwar Jimeta Modern Market da misalin karfe 3:30 na rana. A lokacin da ya bata, yana sanye da jallabiya (Jumfa) mai launin shudi mai duhu (Navy Blue). Tun daga wannan lokaci ba a sake ganinsa ko jin labarinsa ba. Iyalansa da danginsa sun yi kokarin nemansa amma har yanzu ba a gano inda yake ba.

Muna rokon jama’a da hukumomin tsaro da su taimaka wajen gano shi domin a tabbatar da dawowarsa gida lafiya. Duk wanda yake da wani bayani da zai taimaka wajen gano inda yake, da fatan zai tuntubi lambobin da ke kasa ko kuma ya kai rahoto zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da shi cikin gaggawa.

Suna: Shehi Mahmud

Shekaru: 14

Jinsi: Namiji

Tufafin da yake sanye da su lokacin da ya bata: Jumfa mai launin shudi mai duhu (Navy Blue)

Wurin da aka gan shi na karshe: Bakin kasuwar Jimeta Modern Market

Ranar da ya bata: Jiya

Wanda ya bayar da rahoto:
Mustapha Mahmud (Dan’uwansa)

Lambobin Tuntuɓa:
07039686848
09043420443

Za mu matukar yaba da duk wani bayani da zai taimaka wajen gano shi da kuma dawo da shi gida lafiya.

E-sign
OC intelligence
YOLA NORTH DIVISION

MISSING CHILD REPORTThis is to inform the public that a child named Shehi Mahmud, a 14-year-old male, has been missing s...
21/06/2026

MISSING CHILD REPORT

This is to inform the public that a child named Shehi Mahmud, a 14-year-old male, has been missing since yesterday at approximately 3:30 PM.
He was last seen opposite Jimeta Modern Market at about 3:30 PM. At the time he went missing, he was wearing navy blue clothing. Since then, he has not been seen or heard from. Family members and relatives have made efforts to locate him, but his whereabouts remain unknown.

We kindly appeal to the public and security agencies for assistance in locating him and ensuring his safe return. Anyone with useful information regarding his whereabouts is urged to contact the numbers below or report to the nearest police station immediately.

Name: Shehi Mahmud
Age: 14 Years
Gender: Male
Last Seen Wearing: Navy Blue Clothing jumfa
Last Seen Location: Opposite Jimeta Modern Market
Date Missing: Yesterday

Reported By: Mustapha Mahmud (Brother)

Contact Numbers:
07039686848
09043420443

Any information that may help in locating him will be greatly appreciated.

WOMEN’S “GORON SALLAH” PROGRAM HELD IN YOLA SOUTHThe Hisbah Development Initiative (HIDI), Yola South Division, on Satur...
12/04/2026

WOMEN’S “GORON SALLAH” PROGRAM HELD IN YOLA SOUTH

The Hisbah Development Initiative (HIDI), Yola South Division, on Saturday successfully organized a women’s program tagged “Goron Sallah” in a peaceful and well-coordinated atmosphere.

The event was attended by top Hisbah officials at the state level, including the State Commander, Deputy State Commander, as well as other key stakeholders. Zonal Commanders were also present, particularly from the Central Zone, which comprises Yola South, Yola North, Hong, and Girei Local Government Areas.

The program attracted prominent women leaders and dignitaries from within and beyond the community. Special guests and invited speakers delivered insightful lectures focusing on religious values and social development.

Key Lectures

Topics discussed during the program included:

The role of women in Islam

The importance of Islamic education in contemporary society

The speakers emphasized the critical role women play in building a morally upright and progressive society.

Purpose of the Program

The initiative was aimed at:

Strengthening unity and cooperation among women

Promoting awareness of Islamic teachings

Reinforcing the role of Hisbah in societal reformation

Conclusion

Participants expressed satisfaction with the organization and content of the program, describing it as impactful and timely. Many also called for the continuity of such initiatives.

The Hisbah Development Initiative, Yola South Division, reaffirmed its commitment to promoting moral values and fostering community development in line with Islamic principles.

TARON GORON SALLAH NA MATA HISBAH DEVELOPMENT INITIATIVE YOLA SOUTH DIVISIONA yau ne aka gudanar da taron mata na Hisbah...
12/04/2026

TARON GORON SALLAH NA MATA HISBAH DEVELOPMENT INITIATIVE YOLA SOUTH DIVISION

A yau ne aka gudanar da taron mata na Hisbah Development Initiative (HIDI), Yola South Division, wanda aka yi wa lakabi da “Goron Sallah”, cikin nasara da armashi.

Taron ya samu halartar manyan baki da shugabanni daga matakai daban-daban, ciki har da State Commander, Deputy State Commander, da kuma shugabannin yankuna (Zonal Commanders), musamman daga Central Zone wanda ya hada da Yola South, Yola North, Hong, da Girei LGAs.

Haka kuma, taron ya samu halartar fitattun mata masu ruwa da tsaki a al’umma, da s**a hada da manyan baki na musamman, tare da masu jawabi da s**a gabatar da muhimman darussa kan addini da zamantakewa.

Muhimman Jawabai

A yayin taron, an gabatar da lakcoci masu muhimmanci da s**a shafi:

Gudummawar mata a addinin Musulunci
Muhimmancin ilimin addini a wannan zamani

Jawaban sun kara haskaka rawar da mata ke takawa wajen gina al’umma mai inganci da tarbiyya.

Manufar Taron

Manufar wannan taro ita ce:
Karfafa zumunci da hadin kai tsakanin mata
Fadakar da mata kan muhimmancin addini
Karfafa rawar da Hisbah ke takawa wajen gyaran al’umma

Kammalawa
Taron ya gudana cikin nasara, inda mahalarta s**a nuna gamsuwa da shirye-shiryen da aka gabatar, tare da fatan ganin irin wannan taro a gaba.

Hisbah Development Initiative Yola South Division na ci gaba da jajircewa wajen kawo cigaba da tsaftace al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.

Today, the Hisbah Development Initiative, Yola North Division, under the leadership of Aliyu Samaila Yahya (Divisional C...
10/04/2026

Today, the Hisbah Development Initiative, Yola North Division, under the leadership of Aliyu Samaila Yahya (Divisional Commander, Yola North), paid an official visit to the office of the Fityanul Islam Charity Organization, Yola North LGA Branch.

The visit was highly successful, as the Hisbah delegation was warmly received by members of the Fityanul Islam organization with great respect and hospitality. Both parties expressed mutual appreciation and a strong willingness to collaborate towards the promotion of peace, moral discipline, and societal development.

During the meeting, the Divisional Commander, Aliyu Samaila Yahya, delivered a comprehensive presentation on the Hisbah organization. He highlighted its objectives, functions, and the vital role it plays in maintaining law, order, and moral values within the community. He also provided a brief historical background of the organization, along with its achievements.

In response, the leadership of the Fityanul Islam Charity Organization commended the efforts of the Hisbah corps and pledged their full support and cooperation in all initiatives aimed at community development and social reform.

The visit served as an important platform to strengthen mutual understanding, unity, and partnership between the two organizations.

In conclusion, the Hisbah Development Initiative reaffirmed its commitment to extending similar visits to other charitable organizations and relevant institutions in order to foster collaboration, exchange ideas, and enhance overall community development.

This visit forms part of the division’s broader strategy to build stronger relationships with stakeholders and promote collective responsibility in societal growth.

May Allah bless and guide our efforts.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisbah development initiative Adamawa state command posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share