27/08/2026
BAMBANCIN KIRANMU DA SAURAN KIRAYE-KIRAYE
Daga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
“Kamar yadda mu ke cewa; abin da ya bambanta kiran da mu ke yi da wanda sauran su ke kiraye-kiraye shi ne batun meye tabbatar addini? Da yawan mutane su ba sun damu da tabbatar addininbane., kuma ba abin da ya dame su. Su abin da s**a dauka kawai kasar nan da mu ka samu kanmu a ciki bature ne ya zo ya ci mu da yaki ya kafa mana kasa ya hada mu da wanda y hada mu, ya dankara mana harshe, da tsari da komai da komai. Kuma k**ar dole ne a tafi a haka nan. Kuma abin da ya dame su kawai wasu-in ma suna da kishin addini, shi ne a ce Musulmi ne ya ke rike da manyan muk**ai shikenan abin da ya dame su. Kuma in nasu ya samu, kuma suna si su kuma su samu, in nasu ya samu su ma su samu.
"Saboda haka kawai ana ta jan mutane akan cewa wannan rikici ne kawai na siyasa tsakanin ace wane ne shugaba? Ta ina ya fito? Shikenan abin da ya dame su. Saboda haka su mutanensu su shiga ciki su rayu a ciki, shikenan an gama. Zai yiwu a sauya wannan al'amari? Za su ce sam ba zai yiwu ba. Ba zai yiwu addini ya dawo ba? Sai su ce maka tarihi kenan, da can ya yi mulki amma yanzu ba zai yi mulki ba-ba zai yiwu ba, saboda mene? Za su ce ai saboda kasar ba Musulmi ne zallah ba, ko wani abu mai k**a da haka nan.
"To wannan abin dayawan mutane bai dame su ba, kawai abin da za su samu ne su sa a cikinsu, in rayuwarsu ta yi daidai, to addini ya yi daidai. To kuma mafi yawan mutane haka na suke, fadin Imam Husaini a ranar Karbala; Ya ce mutane bayin duniya ne, in addini ya biya bukatar duniyarsu to ya yi, in kuwa ya cutar da duniyarsu, to kadan ke yin addini. Sai ya zama su wadanda su ka zo kashe Imam Husaini su a wurinsu shi ya saba ka'idar addini ne, saboda bai bi sarki ba, wai sarki zai mulki. Shi (Imam Husaini) ne alamin addini, shi ne Magajin Manzon Rahama (S) ba kawai ta fuskar (Jini ba).
"Kun san mutane s**an cewa jikan Annabi, kawia su na tsammanin mujarradin shi jikan Annabi ne saboda jini, ba haka bane, ya wuce nan. Shi ne Magajin Annabi, shi Manzon Allah ya kaddamar da magajinsa ya ce bayansa (Imam) Ali za a bi, bayan Ali sai Hassan (dansa) bayan Hassan sai Husaini. To bin Ali bin Annabi ne, bin Hassan bin Annabi ne, bin Husaini bin Annabi ne.
"To su kuwa mutane sai s**a dauka a'a wanda ke da sarauta shi ne za a bi. To wane ne sarki zamanin (Imam) Husaini? Yazidu ne dan Mu'awiya. Su a wurinsu shi ne za su bi, kuma shi ne addini, shi ne ma su ke kiransa sarkin Musulmi, ba ma sun ce masa sarkin Musulmi bane (kawai) sun ce masa sarkin Muminai, Mumini kuwa ai a lamarin ma wato ka ga in ka ce Mumini ai kana nufin kenan mai cikar imani kenan, s**a dauka duk wanda ya ce ya yi imani da Allah sunansa Musulmi ne, ba shi ne ma'anar AmirulMuminina ba, ma'anar AmirulMuminina; a cikin Muminai to shi ne babbansu, ba wai Muminai ne gasu da yawa shi ne sarkinsu ba, ba abin da ya ke nufi ba kenan, ba ga Muminai ne shi kuma ga sarkinsu ba, a'a, wane ne mai k**alar Imani bayan Manzon Allah? Shi ne wannan (Imam Ali AS) shi ne ya zama Amir a Imani, ma'ana Amir a Imani, an fahimta ai.
"Wa ya kai shi Imani baya ga Annabi? Babu. To shi ne Amir a Imani, ba yana nufin ga wadansu mutane duk sunansu Muminina ne kuma shi ne sarkinsu ba, ba abin da ya ke nufi kenan ba, su kuwa sauran mutane abin da su ka dauka kenan, sun dauka sarkin Musulmi (shi) kaga ga Musulmi ga kuma sarkinsu, ko ba haka ba? Yauwa. Su Musulmin nan kowane iri ne suke, ga su dai ga sarki, yauwa.
"To shi Imam Husaini wajibi ne a masa da'a, wujuban lallai a masa da'a, amma su ba haka su ka dauka ba, wanda su ka biyo shi duu sun dauka shi ma zai zama sarki ne su kuma su samu mukami, da s**a ga abin yanzu ashe ba sarauta za a samu ba-za a fille wuya ne, sai su ka gudu, sai wadanda s**a san matsayin Imam Husaini su s**a tsaya tare da shi. S**a san shahada tare da shi nasara ne, ta haka nan sai ya gwada ma duniya cewa ba ana bin Azzalumai bane, ba a bin su, ko da za su tsinke wuya ne, ana tsayawa ne kyam a tafarki har mutum ya bada ransa.
"Don haka ya zama abin koyi ga dukkan wanda za su biyo baya, su sani cewa da ace 'surrender' ga azzalumai da bin sarakai shi ne addini, to da shi ya bi. To kuma abin mamaki za ka ga mutane suna nikan gari su je su ziyarci Imam (Husaini) su taka su kuma sa bakaken kaya su daddaki kirji su yi koke-koke, amma in kana magana da su sai su ga su za a bi waliyin zamaninsu ne. In ce to kai ba ka ma fahimci abin da ya sa kla zo nan ba kenan ko?
"In ka ga mutum yanzu yana bin Yazidun zamaninsa, to in da ya zo wancan zamanin ne ku na tsammanin me zai yi? Yazidu zai bi, da kila ma in dan Muljanata ya ce ya je su tsinko kan Imam Husaini, shi zai je ya tsinko kai din, suna ganin ana bin sarki ne mai mulki, yanzu ba a yayin sarki ana yayin shugaban kasa ne, in dai ka na tunanin cewa wanda ke da iko shi ake bi-in shi tunaninka kenan, to lallai da ka yi zamani da Yazidu da Yazidu za ka bi, don shi ke da iko, ba ma (Yazidu ba) koda zamanin Annabi Musa ka ke, to da Fir'auna za ka bi, saboda Fir'auna ke da iko.
"To kun ga lokacin su mutanen Fir'auna sai s**a ga cewa lallai Fir'auna keda gaskiya, saboda shi keda mulki, shi kuwa (Annabi) Musa ba shi da mulkin komai, to wa ake bi? A nasu tunanin wa ake bi? Mai mulki, yauwa, mai gwamnati. To amma mu kuwa a wajenmu in ka tambaye mu sai mu ce wanda Allah Ya ce a bi. To ka gaya min, Allah Ya ce a bi Fir'aunoni ne? In da (Allah) Ya na son a bi Fir'aunoni ba zai aiko Musa da sako ba tunda ga Fir'auna. Ba Fir'aunoni ake bi ba, ana bin wanda Allah Ya aiko ne.
"To bayan Allah Ya aiko ManzonSa na karshe, daga nan sai bin wanda ya khaliftar, wanda Manzon nan ya khaliftar, daga nan sai kuma wanda suke bin tafarkinsa, an fahimta ai. Wa ke ce ma mutane a bi Allah a bi Manzo? To shi ne za a bi kenan, ba wanda ya ke cewa shi ke da mulki a bi shi ba. Ka san s**an cewa dole duk inda ka ke dole ka bi dokar kasa, to wa ya ce muku dokar kasa ne? Ba dokar kasa mu ke magana ba, muna batun cewa dokar da ya saba ma na Allah shima za ka bi ne? Abin da ake cewa kenan, dokar da ya saba ma na Allah shima za ka bi ne? Kun san wasu suna cewa kenan ku na nufin ba za ku bi dokar kasa ba? Ka ji wawaye! To yanzu ance muku yanzu in muna tafiya a titin mota sai mu bi hagu-mu ba za mu bi dama ba! Mu ci karo, in mun ga an sa jan haske mu danna a guje mu bi! Wannan ku wawaye ba abin da mu ka ce ba kenan, mu na ce muku abin da ya saba ma na Allah bai hau kan mu ba. Dole ne ya zama doka ba za ta saba ma na Allah ba.
"Su kuma wadannan sun ce ba ruwansu ma da Allah din, su ba ruwansu, su ba ma suna batun Allah ba ne, su abin da ya dame su daban. Kuma in suna dokarsu ba su tunanin Allah Ta'ala Ya ce, ko Manzon Allah Ya ce.
"To komawa ga nizamin addini shi ne ya zama cewa; an zo da nizamin da ba zai taba saba ma na Allah ba, wannan kuwa zai yiwu, kuma shi ya sa ma su ke jin tsoron yiwuwar nasa din ai. Shi ya sa kuma ka ga tunda aka samu Jamhuriyyar Musulunci ta Iran duk s**a dunga kuntata ma wannan Jamhuriyyar, sai dai su za a bi su, su ka dunga kuntata ma Jamhuriyya din, su ka sha mamakin duk kuntatawan da su ke mata ta wanzu, shekaru arba'in yanzu da shida, to a wannan karon ne su ka yi mafarkin rusa ta, da su ka ce sai su ka dandana, da su ka dandana kuda sai su ka ce a'a'a, ashe su na da karfi ne haka? Yanzu su na nan su na sake shiri na kumaji za su koma, muna fatan randa su ka koma kuma Allah Ya dada muzanta su fiye da muzanta sun da ya yi a baya.”
— Ɓangaren jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin rufe IVC wanda aka yi a shekarar 1447/2025 a gidansa da ke Abuja.
— Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky
14 Rabi'ul Auwal, 1448
27 August, 2026