Duniyar musulunci a yau

Duniyar musulunci a yau Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Duniyar musulunci a yau, Religious organisation, Abuja.

12/03/2026

"Idan sun gama da Iran za su koma kan Saudiyya, da sauran ƙasashen Musulmi...".

Wannan shi ne hujjar wasu masu cewa; dole a goyi bayan Iran, a yaƙuƙuwan da take yi da Izraila da Amerka. Don haka suke cewa; -wai- Iran ta zama garkuwa wa ƙasashen Musulmi.

To, wannar magana tana da ma'anoni guda biyu:

1- Idan suna nufin cewa; Izraila da Amerka sun shagaltu da Iran, saboda haka ƙasashen Musulmai sun tsira, saboda ba ta su ake yi ba, to sai in ce: wannan zai iya zama dadai, duk da cewa; ba dole ba ne hakan ya zama sababin ƙin yaƙarsu, saboda mun ga su Izraila da Amerkan, yaƙi ba ya shagaltar da su daga wani yaƙin, shi ya a yanzu ma, Izraila tana kai hare-hare ƙasar Lebanon, a daidai lokacin da take yaƙi da Iran. Kuma haka s**a yi a yaƙin watannin baya, har Houthis na Yemen su ma an kara da su.

2- Idan kuma suna nufin Iran ita ce garkuwa mai kare Musulmai, don haka idan an rusa ta to Musulmai sun rasa ƙasa mai tare musu faɗa, saboda Iran ita ce mai taimakon Muslunci, da taimakon ƴan'uwansu Musulmai, to a wannan sai na ce ba haka ba ne. A Tarihi Iran ba ta taɓa tare wa Musulmai faɗa ba, ko ta karɓa musu faɗa. Misali a kan haka; Iran a kullum suna kasuwanci da matsalar Falasɗinawa, amma Izraila ta yi shekara biyu tana ɓarin wuta a Gaza, tana ruguza yankin, amma Iran ba ta shiga faɗan ba, alhali tana da makamai masu linzami da za ta iya harbawa daga Iran su sauka a Izraila, su yi ɓarna. Amma a yanzu da aka tinkare ta, sai ga shi tana ta harba makamai masu linzami, masu isa har cikin Izraila.

Kuma ka duba ka ga irin ta'addancin da Iran ta yi a ƙasashen Musulmai, tana cikin ƙasashen da s**a taimaki Amerka ta rusa Afganistan.
Ita ta taimaki Amerka ta rusa Iraq, ta mamaye ta.
Ita ta taimaki Rasha ta Asad s**a yi kisan kiyashi wa Musulmai a Syria.
Haka Yemen, da Lebanon.
A yau kuma, ga shi tana ta kai hari a kan ƙasashen Musulmai, musamman ƙasashen yankin Gulf, da Jordan.
To don haka, ta yaya garkuwanka, mai ba ka kariya zai yi maka haka?.
VS

04/06/2023

Ayi da'awa ba tare da zagi da ci mutumci ba
Idan Kanada hujja ta ishe ka makami
Zage zage a bar ma yan tasha aikin su ne
Malami hujja an ka san shi da ita ba zage -zage ba . Karanto kace wan nan abin kafirci ne ga hujja, idan ba ka bari kai kafiri ne. Ba cin mutuncin kowa ka tsayar da hujja kawai!

SABODA KUDI SUN SAYAR DA ADDININSU DA MUTUNCIN SUHadakar kungiyar Darikar Tijjaniyya na Kasar Nigeria ta gabatar da Babb...
19/12/2022

SABODA KUDI SUN SAYAR DA ADDININSU DA MUTUNCIN SU

Hadakar kungiyar Darikar Tijjaniyya na Kasar Nigeria ta gabatar da Babban taron Mauludi na duniya a birnin Minna jihar Niger

Bisa la'akari da 'yan siyasa da aka gayyata a taron Maulidin, na ga akwai dan takaran Shugaban kasa a jam'iyyar APC Bola Tinubu da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC

Sunce taro ne na addini, sai muka ga sun gayyaci Tinubu dan takaran jam'iyyar APC da wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar APC, amma basu gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jamiyyar NNPP ba, basu gayyaci Alhaji Atiku Abubakar na jamiyyar PDP, to tunda taro ne na addini me ya hana a gayyaci Atiku da Kwankwaso?

A fakaice ana so a nuna wa Musulmin Arewa Shugabannin Darikar Tijjaniyyah da s**a shirya wannan taron zasu sa a mara wa Tinubu baya kenan a zaben Shugaban Kasa na 2023, taro ne na tallen Tinubu ba taro bane na Mauludi, shiyasa a gurin taron s**a nada Tinubu mukamin Grand Khadi na Tijjaniyyah

Wai yau Tinubu ne aka nadashi a matsayin Grand Khadi na darikar Tijjaniyyah, mutumin da ko Fatiha mai kyau bai iya karantawa ba, matarsa da 'ya'yansa duka ba Musulmai bane, babu Musulunci a gidansa, sai yiwa Allah kishiya kadai ke a gidansa

Ya kamata al'ummar Musulmi mu gane, ana so a saye mana Malamai da kudi domin su marawa makiyin mu baya, mutumin da akwai alhakkin jinanen rayukan 'yan arewa Musulmi a wuyansa, gaskiya wannan abin takaici ne

Allah Ya sauwake أمين

25/11/2022

Subhanallahi wa bihamdihi
Subhanallahil aziim
100 times morning and evening.

22/11/2022

MASOYA ANNABI NA HAKIKA BA SA YIN MAULIDI

Su Ahlus Sunna da s**a ce ba za su yi Maulidi ba, ba -wai- k'in Annabi (saw) ne ya sa haka ba -Allah ya tsare su-, kamar yadda ake rudan jahilai ake fada musu hakan, a'a, su sun ce ba za su yi Maulidi ba ne saboda su Mabiya Sunnar Annabi (saw) ne.
To menene ma'anar Sunnar Annabi (saw)?
Ita ce koyarwar Annabi (saw).

Don haka tun da su Ahlus Sunna ne, ma'ana mabiya Sunnar Annabi (saw), to sun bincika Sunnar ta Annabi (saw), tun daga farko har karshe amma ba su ga inda Annabi (saw) ya yi umurni ko ya kwadaitar ko ya yi ishara zuwa ga Bikin Maulidi ba. Kawai iya abin da s**a gani a Sunnar Annabi (saw) na abin da ya shafi haifuwarsa shi ne; yin Azumi a ranar Litinin, Annabi (saw) ya kasance yana Azumi a duk ranar Litinin din, sai aka tambaye shi a kan haka, sai ya ce: saboda a ranar aka haife shi.

Kuma Ahlus Sunna sun san cewa; asali Kiristoci ne suke yin Bikin Maulidin Annabi Isa (as). Kuma sun san cewa; Annabi (saw) ya hana al'ummarsa koyi da Yahudawa da Nasara a lamura na rayuwa b***e kuma lamura na Addini, matukar Addininmu bai zo da shi a cikin Alkur'ani ko Hadisan Annabi (saw) ba.

Saboda haka, abubuwa biyu ne s**a sa Mabiya Sunnar Annabi (saw) ba sa yin Maulidi:
(1) Maulidin ba ya cikin Sunnar Masoyinsu kuma abin koyinsu Annabi Muhammadu (saw).
(2) Maulidin koyi ne da Kiristoci masu yin Christmas, wato Bikin Murnan haifuwar Annabi Isa (as), kuma Annabi (saw) ya hana mu koyi da su a harkokin rayuwa b***e a Addini.

Saboda haka, abin tambaya a nan, don Allah wanene masoyin Annabi (saw) na hakika, tsakanin Ahlus Sunna masu koyi da shi a Addini, da kuma 'Yan Maulidi masu koyi da Kiristoci?!

09/11/2022

The issue of Religious Bigotry did not start from the North

Let's go back to 1962, when a Northern Muslim, Abubakar Tafawa Balewa registered Nigeria as a member of the World Council of Churches and International Bible Society in 1963, no complain from the Muslim North.

Saturday was a working day in Nigeria until 1973, Gowon, a Christian minority from the North declared it a work free day, to enable the Seventh Day Adventist Church to worship, no complain from the Muslim North.

In February 1979, Olusegun Obasanjo denied Ahmed Deedat, an Islamic Preacher, entry into Nigeria, no complain from the Muslim North.

In 1982 pope John Paul II was welcomed to Nigeria by a Muslim, Alhaji Shehu Shagari.

Reinhart Bonke, a Christian Crusader, had a free enterance to Nigeria at will, no complain.

Abacha welcomed Pope John Paul and established Papal Square along Kubwa express way, no complain from Muslims.

But in 1986 when Babangida registered Nigeria as a member of the Organization of Islamic Conference (OIC) there was a riot in Lagos, Portharcout, Enugu, orchestrated and organised by CAN.

Pls who are the Religious Bigots?

Just recently, the Nigeria Supreme Council for Islamic Affairs distanced itself from all kinds of politics, but what about CAN?

In 2013, a Private Jet belonging to the CAN President was intercepted in South Africa loaded with foreign currency, imagine it belonged to the Sultan?

So people of God, let's ask ourselves who are the real Religious Bigots before we make another major mistake as a people.

02/10/2022

Sau da yawa mai ilimin addini idan ya yi kuskure ko laifi, ilimin shi kan gaya masa gaskiya ya gyara, amma wanda bai karatun addini ba bai ma ganin gaskiyar sau da yawa kuma idan aka gaya masa sai ya dauke ka makiyin shi.

Kar ka zauna baka karatun addini.

08/04/2022

Dafatan jama'an musulmai kowa yasha ruwa lafiya.

Allah ya sa mu aikata dai-dai.
11/01/2022

Allah ya sa mu aikata dai-dai.

Guzurin safiya 💦
05/12/2021

Guzurin safiya 💦

Allah ya karba mana addu'o inmu kuma ya zaba mana abu mafi alkhairi!!
01/10/2021

Allah ya karba mana addu'o inmu kuma ya zaba mana abu mafi alkhairi!!

Address

Abuja

Telephone

+2348160042255

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar musulunci a yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share