02/04/2026
DA ƊUMI-ƊUMI:🔥 Atiku zai jagoranci taron manema labarai kan janye sahalewar shugabancin ADC daga INEC
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, zai jagoranci shugabannin ‘yan adawa da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar siyasa wajen gudanar da taron manema labarai kan batun janye sahalewar shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) daga hannun wani ɓangare na jam’iyyar.
An shirya gudanar da taron ne yau Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026, da ƙarfe 1:00 na rana, a Shehu Musa Yar’adua Centre da ke birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da taƙaddama kan sahihancin shugabancin ADC, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce da zarge-zarge tsakanin ɓangarorin jam’iyyar, musamman bayan matakin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka.
Ana sa ran manyan ‘yan siyasa da jagororin jam’iyyun adawa za su halarci taron, inda za a fayyace matsayarsu tare da bayyana matakan da za su ɗauka dangane da wannan rikici.
Wannan mataki na iya ƙara ɗumama siyasar ƙasar nan gabanin babban zaɓen da ke tafe, yayin da rikice-rikicen cikin gida ke ci gaba da girgiza wasu jam’iyyun siyasa.