Alhuda Islamic Society ABUJA

Alhuda  Islamic Society  ABUJA propagating ISLAM to the non MUSLIM

12/11/2021

Manzon Allah (Saww) yace: "Duk wanda yayi salati a gareni ko wacce Juma'a sau arba'in (40) Allah zai shafe Qananan zunubansa gaba daya"

- A wani hadisin yace: "mafi kusancin mutane a gareni ranar alkiyama sune wanda s**a fi yawaita salati a gareni."

- A wani hadisin yace: " wanda duk ya manta da yin salati a gareni hakika ya kaucewa hanyar Aljanna."

- Kuma yace: "babu wata addua face akwai hijabi tsakaninta da sama har sai an yi salati a gareni, idan akayi salati a gareni sai wannan addua ta keta hijaban nan a dagata zuwa sama." ma'ana duk wata addua da bawa zaiyi bazata wuce sama ba har sai yayi salati ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa'sallam. Shi yasa yana da kyau idan zamu roki Allah akan bukatun mu, mu fara da salati, kuma mu rufe da salati Ga Annabi (saww).

Allah (swt) yasa muna cikin masu rabo a wannan Rana.

11/10/2021
03/10/2021

FUNERAL PRAYER (SOLAATUL JANAZAH)

Bismillaahi Rahmani Raheem.

Praise be to Allaah (Lord of the universe)

Solaatul Janazah is a Fard Kifayah, and its procedure and details follow the sunnah of the Messenger of Allaah (peace and blessings be upon him). It is strongly recommended that as many members of the Muslim community as possible should join the funeral procession and Solaatul Janazah:

Six Rights of a muslim over another.

Narrated by Abu Huraira (may Allaah be pleased with him) that the Messenger of Allaah (may peace and bleasings be upon him) said: "Six are the rights of a Muslim over another Muslim. It was said to him: Messenger of Allaah, what are these? Thereupon he said:
When you meet him, offer him greetings.
When he invites you to a feast accept it.
When he seeks your council give him.
When he sneezes and says:" All praise is due to Allaah," you say Yarhamuk Allaah (may Allaah show mercy to you).
When he fails ill visit him.
When he dies follow his bier."
(Sahih Bukhari and Muslim)

The following describes this Solaat briefly:

1️⃣ There is no Azan or Iqamah for Salat ul Janazah which is offered with the participants standing and with the body of the deceased placed in front of them. There are no Rukus or Sujud to be performed in Salat ul Janazah1

2️⃣ It is preferable if those offering Salat ul Janazah form an odd number of rows with the Imam standing in the front facing the body of the deceased. He should stand in line with the head of a male deceased and with the midriff of a female deceased.

3️⃣ In the case of multiple deceased persons, the bodies should be placed in a row with those of men nearest to the Imam.

4️⃣ If Solaatul Janazah is being offered in the open, it is not necessary for the participants to take off their shoes so long as they are visibly clean.

5️⃣ The deceased and those offering the Solaat must be Muslims, and the body of the deceased and those offering the Salat must be in a state of ceremonial cleanliness
(Wudu or Ghusl).

NOTE

👉It is not obligatory to offer Solaatul Janazah for children who die before attaining the age of puberty as is clear from the following.

Narrated by Aishah (may Allaah be pleased with her) that Ibraheem (the son of the Messenger of Allaah (peace and blessings be upon him), died when he was eighteen months old, and The Prophet (peace be upon him) did not pray (Janazah) for him."
(Sunan Abu Dawood).

👉It is permissible to offer Salaatul Janazah for a child including a miscarried fetus.

The Messenger of Allaah (peace and blessings be upon him) said: "As for a fetus, the (Janazah) prayer may be performed for it, and Dua would be made that its parents be granted forgiveness and mercy."
(Musnad Imam Ahmad)

👉Solaatul Janazah must be offered even for a Muslim guilty of ignoring the teachings of Islaam (e.g, Solaat, Zakaat, prohibition of alcohol and Zina etc.). However, respected leaders of the community should refrain from participating in the Solaatul Janazah as a demonstration of their disapproval of the conduct of the deceased and as an admonition to others.

Summary of funeral prayer.

Narrated by Abdullah Ibn Abu Aufa (May Allaah be pleased with him) that "While offering the funeral prayer of one of his daughters, he recited four Takbir, and after the fourth Takbir he continued standing for a time equal to an interval between two Takbir, praying for her and seeking forgiveness of Allaah for her.'' Then he said: "The Messenger of Allaah (peace and blessings be upon him) used to do so.''
(Al-Hakim)

1️⃣. The Imam should raise his hands, recite the Takbeer, and then tie his hands as in all other Solaats. Those offering the Solaat should follow..

After the First Takbeer​: Recite Surat Al-Fatiha.

*1. Bismillaahir Rahmaanir Raheem
*2. Alhamdu lillaahi Rabbil 'aalameen
*3. Ar-Rahmaanir-Raheem
*4. Maaliki Yawmid-Deen
*5. Iyyaaka na'budu wa lyyaaka nasta'een
*6. Ihdinas-Siraatal-Mustaqeem
*7. Siraatal-lazeena an'amta 'alaihim ghayril- maghdoobi 'alaihim wa lad-daaalleen

2️⃣- ​After the Second Takbeer: Recite solaat Al-Ibrahimiyya to the end,

​Allaahumma salli 'alaa Muhammadin wa 'alaa 'aali Muhammadin, k**aa sallayta 'alaa 'Ibraaheema wa 'alaa 'aali 'Ibraaheema, 'innaka Hameedun Majeed. Allaahumma baarik 'alaa Muhammadin wa 'alaa 'aali Muhammadin, k**aa baarakta 'alaa 'Ibraaheema wa 'alaa 'aali 'Ibraaheema, 'innaka Hameedun Majeed​.

3️⃣- ​After the Third Takbeer:

Then everyone should offer Dua al Mayyah (a prayer for the mercy of Allaah to be visited upon the deceased) silently according to how it was narrated from The Messenger of Allaah (peace be upon him).

Some of them are:
👉Allaahum-maghfir lihayyinaa, wa mayyitinaa, wa shaahidinaa, wa ghaa'ibinaa, wa sagheerinaa wa kabeerinaa, wa thakarinaa wa 'unthaanaa. Allaahumma man 'ahyaytahu minnaa fa'ahyihi 'alal-'Islaami, wa man tawaffaytahu minnaa fatawaffahu 'alal-'eemaani, Allaahumma laa tahrimnaa 'ajrahu wa laa tudhillanaa ba'dahu​.
(O Allaah! forgive our living and our dead, those who are with us and those who are absent, our young and our old, our menfolk and our womenfolk. *O Allaah*, whomever you give life from among us give him life in Islam, and whomever you take way from us take him away in Faith. *O Allaah*, do not forbid us their reward and do not send us astray after them).

👉Allahummaghfir lahu, warhamhu, wa 'afihi, wa'fu 'anhu, wa akrim nuzulahu, wa wassi' mudkhalahu, waghsilhu bil-ma'i wath-thalji wal-baradi, wa naqqihi minal-khataya, k**a naqqaytath-thawbal-abyada minad-danasi, wa abdilhu daran khairan min darihi, wa ahlan khairan min ahlihi, wa zawjan khairan min zawjihi, wa adkhilhul-Jannata, wa a'idh-hu min 'adhabil-qabri, wa min 'adhabin-nar [if the dead person is a woman, one should change the ending of certain words in this supplication from hu to ha]
(O Allaah! Forgive him, bestow mercy upon him, pardon him, accord him a noble provision and make his grave spacious, wash him with water, snow and hail, purify him from sins as You have purified the white garment from soiling, give him a better abode in place of his present one, and a better family in exchange of his present one, and a better spouse in place of his present wife; admit him to Jannah and protect from the trial in the grave and punishment in the Hell)..

4️⃣- Then lastly after the Fourth Takbeer
Everyone should then offer prayers for the Muslim community in general, again silently.

5️⃣- And finally, end the prayer with Salaam to complete the Solaatul Janazah.
Salaam may be offered once to the right only, or once each to the right and then to the left as in all other prayers.
This would complete the Solaatul Janazah.

Convey/share the teachings of islam and gain reward.

Source:FIQH CLASS

29/09/2021

YAYA ANNABI (ﷺ) YAKE YIN SALLAH, DARASI NA BIYU

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahama* Mai *Jinqai*_

_*4. KARATUN FATIHA:* Bayan *Manzon Allah (ﷺ)* Yayi Addu'ar Buɗe Sallah, Abu Na Gaba Da Yakeyi Shine Karatun Fatiha. Kafin Karatun Fatihar Yanayin A'uziyya Da Bismillah A Asirce, Sannan Ya Fara Karatun Fatiha._

_Karatun Fatiha Rukuni Ne Daga Cikin Rukunnan Sallah, Ta Yanda Duk Wanda Yayi Sallah Be Karanta Fatiha Ba Bashi da Sallah. Saboda Hadisin *Ubadah bn Samit (ra)*._

عن عبادة بن الصامت قال: أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: *(لا صلاة لمن لم يقرأ بفاتحة الكتاب)*
[رواه البخاري ومسلم]

_An Karɓo Daga *Ubadah bn Samit (ra)* Yace: Lallai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Babu Sallah Ga Wanda Be Karanta Fatiha a Cikinta Ba”.*_
_(Bukhari da Muslim)_

_*Manzon Allah (ﷺ)* Yanayin Karatunsa Ne Cikin Natsuwa Kuma Daki Daki, Ba Tare da Shigar da Wata Aya Cikin Wata Aya ba. Sannan Idan Yazo Ƙarshen Suratul Fatiha Bayan Yace: *(وَلا الضَّالِّينَ)*, Sai Yace: *(آمين)* A Sallar da Ake Bayyana Karatunta, Kamar Sallar Asubah da Raka'a Biyun Farkon Magariba da Isha'i da Kuma Sallar Juma'a. Amma A Sallar da Ake Asirtawa Karam Azahar da La'asar, Yana Cewa *“Ãmin”* Ɗinne a Asirce._

_*5. KARATUN SURAH:* Idan Ya Kammala Karatun Fatiha, Yana Karanta Abinda Ya Sauwaƙa Na Karatun Surah. Yakan Tsawaita Karatu a Sallar Asubah; Yana Karanta Kamar Aya Ɗari a Raka'ar Farko. Raka'a Ta Biyu Kuma Kamar Aya Sittin. Wani Lokacin Kuma Yana Karanta *SURATU QAF* da Mak**antanta Kamar *Suratu Ɗur*._

_A Sallar Magariba Kuma Yana Gajarta Karatu, Yana Yawaita Karanta:_
*{إِذَا زُلْزِلَتِ}* Ko *{وَالْعَادِيَاتِ}* Ko *(وإِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ)* Ko *(وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ)* Ko *(وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَا)*.

_A Sallar Isha'i da Azahar da La'asar Kuma Yana Tsakaita Karatu A Cikinsu. Sau Da Yawa Yana Karanta:_
*{لَمْ يَكُنِ}* Ko *{وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْبُرُوجِ}* Ko *{إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ}* Ko *{عَبَسََ وَتَوَلَّى}*

_Sai Dai Yana Tsawaita Sallar Azahar Sama da Sallar La'asar. Wannan Itace Sunnarsa da Ya Rayu Yana Aiwatarwa._

_*6. RUKU'U:* Bayan Ya Kammala Karatun Fatiha, Sai Yayi Ruku'u Yqna Mai Faɗin *(ALLAHU AKBAR)*. Yanayin Ruku'un Ne Cikin Natsuwa Ba Tare Da Gaggawa ba. Yanq Sanya Hannunsa Akan Gwiwowin Ƙafafunsa, Sannan Ya Miƙar da Bayansa Tare da Daidaitashi da Kansa Ta Yanda Bazakaga Wani Karkata a Bayansa ba. Bayan Ya Daidaita Sai Ya Karanta Ɗaya Cikin Waɗannan Tasbihan Guda Uku, Sau Uku, Ko Biyar Ko Sau Bakwai:_

*١. (سبحان ربي العظيم)*
_*1. SUHÃNA RABBI AL-AZEEM*_

*٢. (سبحانك اللهم ربنا وبحمدك اللهم اغفر لي)*
_*2. SUBHÃNAKALLÃHUMMA RABBANÃ WABI HAMDIKA, ALLÃHUMMAG FIRLI.*_

*٣. (سبوح قدوس رب الملائكة والروح)*
_*3. SUBBUHUN, QUDDUSUN RABBUL MALÃ'IKATU WAR RUH.*_

_*7. ƊAGOWA DAGA RUKU'U:* Bayan Ya Gama Tasbihin Ruku'u, Sai Ya Ɗago Ɗaga Ruku' Yana Mai Faɗin: *(SAMI'AL LAHU LIMAN HAMIDAHU)*, Bayan Ya Daidaita a Tsaye Sai Yace::_

*(حمدًا كثيرًا طيِّبًا مبارَكًا فيه، مِلْءَ السَّمواتِ ومِلْءَ الأرضِ، ومِلْءَ ما شِئْتَ مِن شيءٍ بعدُ)*

_*“HAMDAN KATHIRAN ƊAYYIBAN MUBARAKAN FIHI, MIL'AS SAMAWATI, WA MIL'AL ARDI, WA MIL'A MA BAINAHUMA, WA MIL'A MA SHI'ITA MIN SHAI'IN BA'ADU”.*_

_Wani Lokaci Yakan Ƙara da Cewa:_

*(أهلَ الثناءِ والمجدِ، أحقُّ ما قال العبد،ُ وكلُّنا لك عبدٌ، اللهمَّ لا مانعَ لِما أعطَيتَ، ولا مُعطيَ لِمَا منَعتَ، ولا ينفَعُ ذا الجَدِّ منك الجَدُّ)*

_*“AHLATH THANÃ'I WAL MAJDI, AHAQQU MA QÃLAL ABDU, WA KULLANÃ LAKAL ABDUN, ALLÃHUMMA LÃ MÃNI'U LIMÃ A'AƊAITA, WALÃ MU'UƊIYA LIMÃ MANA'ATA, WALÃ YANFU'U ZAL JADDI MINKAL JADDU”.*_

_*ALLAH KA DATAR DAMU KA BAMU IKON BAUTA MAKA YANDA KAKESO KUMA KA AMSHI BAUTAR*_

_Anan Zan Dakata, Sai Mun Haɗu a Darasi Na Gaba_

*سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وبَحَمْدكَ أشْهدُ أنْ لا إلهَ إلا أنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وأتُوبُ إِلَيْكَ*

_*✍🏽Abu Aysha Al-Maliky*_

27/09/2021

SUNNONI GUDA TAKWAS(8) DA IN A KA BARSU A SALLAH ZA A YI SUJADAR RAFKANUWA

1- Karatun surah(wacce a ke yi bayan an karanta fatiha).

2-Sirranta karatu a in da a ke sirrantawa ko bayyana karatu a in da a ke bayyanawa.

3-Faɗin: "Sami'allahu liman hamidahu", (in a ka barshi sau biyu).

4-Kabbara(ban da ta harama), in a ka bar guda biyu zuwa sama.

5-Tahiyyar farko.

6-Zama domin tahiyyar farko

7-Tahiyyar karshe

8-Zama domin tahiyyar karshe

Idan mai sallah ya bar wani abu cikin ababen da a ka lissafa a sama zai yi sujuda biyu kafin sallama(ƘABLIY).

Wanda ya bayyana karatu a in da a ke sirrantawa zai yi sujuda biyu bayan sallama(Ba'adiy)

Wanda ya sirranta karatu a in da a ke bayyanawa zai yi sujada biyu kafin sallama(Ƙabliy).

Madogara:

ترقيع الصلاة- سجود السهو على المذهب المالكي(39) و-المقدمة العزية للجماعة الأزهرية (105-104)

26/09/2021

YANAYI TAKWAS (8) MALA'IKU SUNA MAKA ADDU'A ACIKINSU YI KOKARI KA KIYAYESU.

1.lokacin daka tsaya a sahun farko a sallah.
2.zamanka a masallaci bayan gama sallah.
3.lokacin gaida Mara lafiya.
4.lokacin ziyaran dan'uwanka don Allah.
5.lokacin dakayi ma wani addu'an alkhairi batare da saninsa ba.
6.lokacin dakake koyar da mutane alkhairi.
7.lokacin dakake bacci da tsarki tareda kai.
8.lokacin dakake cin abincin sahur.

Ya Allah kasanyamu acikin su Amin ya wahidulkhahar

20/09/2021

YAWAITA SALATI A DAREN JUMMA'A DA KUMA RANAR JUMMA'A GA MAFI ALKHAIRIN HALITTU SAW

Manzon ALLAH (saw) yace'; MAROWACI shine wanda aka ambace ni a wurin da yake, kuma bayyi salati a gare ni ba. Tirmidhi ya ruwaito

Manzon ALLAH (saw) yace;
Ku yawaita salati a gare ni ranar jumma'a' da daren jumma'a' duk wanda yayi salati a gare ni guda daya ALLAH zaiyi masa goma !
[ حسنه الألباني في «السلسلة الصحيحة» برقم (١٤٠٧) ]

*اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيد*

Domin shiga Wattsap Group ; 08032216394

Rasheedah Bintul Islam

19/09/2021

MU KOYI IBADAR MU! "WATO SALLAH" DARASI NA 029

YANDA AKE KIRAN SALLAH (1)

Yadda Ake Kiran Sallah:-

1– Yadda ake kiran sallah shi ne, *“Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, Ashhadu an la’ilaha ilal lah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Hayya alal Salah, Hayya alal Salah, Hayya alal falah, Hayyah alal falah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha ilal Lahu”* [Muslim ne ya rawaito shi.

2– Yadda ake Iqama: “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Hayya alal Salah, Hayya alal falah, Qad Qamatus Salatu, Qad qamatus Salah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha ilal Lahu”.

*_Abinda Ake Son Wanda Ya Ji Kiran Sallah Ya Yi:-_*

1– Ya faɗi irin abin da mai kiran sallah ya faɗa, sai dai wajen faɗin “Hayya alal Salah, Hayya alal Falah” sai ya ce, “La Haula wala Quwwata Illa Billah” [Bukhari ne ya rawaito shi..

2– Bayan an gama kiran sallar sai ace, “Ashhadu an la’ilaha wahdahu, la sharika lahu, wa anna Muhammadan Abduhu Wa Rasuluhu, Raditu billahi Rabban, Wa bi Muhammadin Rasulah, Wa bil islami dinan” [Muslim ne ya rawaito shi.

3– Ya yi wa Annabi Sallallahu Alahin Wasalam salati bayan gama kiran sallar, sannan ya ce, “Allahumma Rabba Hazihid Da’awatit Tammati, Wassalatil Qa’imati, Ati Muhammadanil Wasilata wal Fadilah, Wab’ashu maqaman mahmudanil lazi wa’addahu” [Bukhari ne ya rawaito shi.

4– Ya yi wa kansa addu’a tsakanin kiran sallah da iqama, saboda addu’a a wannan lokacin ba a mayar da ita, saboda faɗin Manzon Allah Sallallahu Alahin Wasalam “Haqiqa addu’a tsakanin kiran sallah da iqama ba a mayar da ita” [Ahmad ne ya rawaito shi.

Mu Haɗu a Darasi Na Gaba In Allah Ya Kaimu.

18/09/2021

SUNNONI GUDA TAKWAS(8) DA IN A KA BARSU A SALLAH ZA A YI SUJADAR RAFKANUWA

1- Karatun surah(wacce a ke yi bayan an karanta fatiha).

2-Sirranta karatu a in da a ke sirrantawa ko bayyana karatu a in da a ke bayyanawa.

3-Faɗin: "Sami'allahu liman hamidahu", (in a ka barshi sau biyu).

4-Kabbara(ban da ta harama), in a ka bar guda biyu zuwa sama.

5-Tahiyyar farko.

6-Zama domin tahiyyar farko

7-Tahiyyar karshe

8-Zama domin tahiyyar karshe

Idan mai sallah ya bar wani abu cikin ababen da a ka lissafa a sama zai yi sujuda biyu kafin sallama(ƘABLIY).

Wanda ya bayyana karatu a in da a ke sirrantawa zai yi sujuda biyu bayan sallama(Ba'adiy)

Wanda ya sirranta karatu a in da a ke bayyanawa zai yi sujada biyu kafin sallama(Ƙabliy).

Madogara:

ترقيع الصلاة- سجود السهو على المذهب المالكي(39) و-المقدمة العزية للجماعة الأزهرية (105-104)




TELEGRAM:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM:
https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v

Address

NO 36 KINSHASA Street WUSE ZONE 6
Abuja

Telephone

+2348033617147

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alhuda Islamic Society ABUJA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Alhuda Islamic Society ABUJA:

Share