27/05/2026
“YADDA AKE NIYYAR YANKA RAGON LAYYA ”
—Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Yace:
“Ranar layya, a yayin da mutum yake yanka Rago, to ya halarto da zuciyarsa da tunanin cewa, shi mai sadukarwa ne, a shirye yake ya yi duk abin da Allah (Ta'alah) ya umurce shi koma menene, Ko ba da ransa ne, ko na ƴa’ƴansa ko dukiyarsa, sai gigarau, ya gigarama Rago wuƙa. Da wannan niyya ɗin, idan ya yi wannan to shi ne ainihin.
Allah yana kallon zuciya ne, k**ar yadda Allah (T) yake cewa: “Jinainai na abin yanka da kuke yankawa, da nama na abin da kuke yankawa ba ya zuwa wajen Allah, abin da yake zuwa wajen Allah (taƙawa) ne daga wajenku". Ina taƙawa yake? A zuciya, da wacce niyya ka yi layya?”
-Shaikh Zakzaky (H) jim kaɗan da kammala Sallar Babbar Idi da aka gudanar a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. A ranar Asabar ɗin 10 ga watan Zulhijjah, 1435 (4/10/2014).
— Tafsir Da Jawaban Jagora
-JawabanJagora
10/DhulHijja/1447
27/05/2026