12/11/2025
SHUGABAN FITYANUL ISLAM RESHEN BABBAN BIRNIN TARAYYA ABUJA IMAM Murabbi Mustapha-Kadai ALBARNAWY YA KARBI BAQUNCIN SHUGABAN NUSRET, MR. HUSEYIN SELVI NA QASAR TURKIYA (TURKISH)
A yau Laraba 12 ga watan Nuwanba, shugaban kungiyar Fityanul Islam reshen Abuja ya karbi Bakuncin Shugaban Nusret Educational and Cultural Co. Ltd. Nigeria. Na kasa baki daya Mr. Huseyin Selvi. A offishin Qungiyar Fityanul Islam reshen Abuja dake No 11 Ajesa street Wuse 2 Abuja.
A cikin ganawar tasu Shugaban na Nusret ya qaddamar da takarda ga Shugaban Fityanul Islam reshen Abuja, Imam Murabbi Mustapha Kadai Albarnawy wacce take dauke da neman hadin guiwar sa wajen shirya Workshop na kwana daya (One day workshop) a nan Babban birnin tarayya Abuja.
Tuni dai Ba tare da bata lokaci ba Shugaban Fityanul Islam reshen Abuja Imam Murabbi Albarnawy ya bada hadin kai da amincewa da wannan qudurin
Yayinda Shugaban nin guda biyu s**a Umarci mataimakan su da membobin su da su fara Shirye Shiryen gudanar da wannan workshop din na kwana daya
Zaman ya samu halartar Jagoririn Fityanul Islam reshen Abuja bangaren Uwar kungiya dana Agaji Kamar Ameera Sayyida Rukayya Sheikh Umaru Sanda, Alhaji Gambo Ngulak, Malam Ibrahim Shu'aibu Suddu, Malam Yusuf Dahiru Abubakar, Malam Mukaffa Ibrahim Malam Atiku Zuba da sauran su.
Sanarwa daga Mukaffa Ibrahim
P.R.O Fityanul Islam Abuja Branch.
12/11/2025