Imam Ridah Hausa

Imam Ridah Hausa Shafin Hausa na Haramin Imam Ridha (Reza) A.S dake Birnin Mashhad, Iran.

13/08/2026

Muna taya dukkanin Al'umma juyayi da ta'aziyyar Wafatin Annabin Rahama Muhammad(s.a.w.w) da jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Ridha(as).

✉️ Cikakken Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci zuwa ga Al'ummar Iran Game da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Tsakanin S...
18/06/2026

✉️ Cikakken Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci zuwa ga Al'ummar Iran Game da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Tsakanin Shugabannin Iran da Amurka


📲
https://t.me/MKhamenei_ha

📢 Sanarwa Ta Ɗaya daga Kwamitin Tunawa da Shahadar Jagora MujahidiDa sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai📝 Tare da taya m...
03/06/2026

📢 Sanarwa Ta Ɗaya daga Kwamitin Tunawa da Shahadar Jagora Mujahidi

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai

📝 Tare da taya murnar Babban Idin Ghadir Khum da kuma tunawa da cikar shekaru talatin da bakwai da rasuwar wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Khumaini (R.A), ana sanar da al’ummar Iran, ’yantattun mutane na Duniya, da masu kaunar jagoran juyin juya halin Musulunci da ya yi shahada, Ayatullah Al-Uzma Sayyid Ali Husaini Khamene'i (R.A), cewa hukumomin da abin ya shafa tare da kungiyoyin jama’a suna ci gaba da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan bankwana, jana’iza da kuma binne wannan shahidin mujahidi cikin girmamawa da daukaka.

Saboda haka, duk wasu jita-jita ko hasashe-hasashen kafafen yada labarai dangane da cikakkun bayanan wannan lamari ba su da inganci kuma ba za a dogara da su ba.

👈 Shirye-shirye, ayyukan yada labarai da sauran cikakkun bayanai game da wannan babban taro za a sanar da su a cikin sanarwar da kwamitin tunawa da shahadar jagora mujahidi, Ayatullah Al-Uzma Khamene'i, zai fitar nan gaba, in sha Allah.

📝 Ofishin Kula da Wallafa Ayyukan Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

🗓 3 ga Yuni, 2026


📲

Muna taya dukkanin mabiya wanann shafi namu murna da zagayowar ranar Ghadeer, ranar cika ni'ima. «الحَمْدُ للهِ الَّذِي ...
03/06/2026

Muna taya dukkanin mabiya wanann shafi namu murna da zagayowar ranar Ghadeer, ranar cika ni'ima.
«الحَمْدُ للهِ الَّذِي جَعَلَنا مِنَ المُتَمَسِّكِينَ بِولايَةِ أَمِيرِ المُؤْمِنِينَ وَالأَئِمَّةِ عَلَيْهِمُ السَّلام».

BARKA DA RANAR ARAFA...Wanda yake da Allah a wannan rayuwa to fa shine yake da komai, wanda kuwa ya rasa Allah to ya ras...
26/05/2026

BARKA DA RANAR ARAFA...

Wanda yake da Allah a wannan rayuwa to fa shine yake da komai, wanda kuwa ya rasa Allah to ya rasa komai.....

Daga cikin Addu'ar Imam Hussain(as) a ranar Arafa yana cewa:
🤲🏻 📿 "Ya Ubangiji, wanda ya rasa ka (to) me ya samu? wanda kuwa ya same ka me ya rasa"

«مَاذَا وَجَدَ مَنْ فَقَدَكَ، وَمَا الَّذِي فَقَدَ مَنْ وَجَدَكَ»

Ranar Arafa rana ce ta kara samun masaniya ga Allah T da kuma neman kusanci da shi, don haka a dage da Addu'o'i da Munajati.

Muna yi muku barka da wannan Rana ta Arafa.

📨 Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci dangane da ranar girmama harshen Farisanci da tunawa da Hakim Abulqasim Ferdo...
15/05/2026

📨 Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci dangane da ranar girmama harshen Farisanci da tunawa da Hakim Abulqasim Ferdowsi


📲

https://t.me/MKhamenei_ha/87

15/05/2026

Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya shugaba mai wannan zamani Al-imamul Muntazar(ajf).

09/05/2026

Masu bibiyarmu a wannan zaure mai albarka, sakon ziyara da addu'o'inku sun isa ga Imam Ridha(as).

Allah ya biya mana dukkanin bukatunmu baki daya.

A duk lokacin da damuwa ta yi maka yawa.... A duk lokacin da matsaloli s**a baibaye ka.... A duk lokacin da Bashi ya yi ...
09/05/2026

A duk lokacin da damuwa ta yi maka yawa....
A duk lokacin da matsaloli s**a baibaye ka....
A duk lokacin da Bashi ya yi maka katutu....
A duk lokacin da kake son farin ciki, nishadi da nutsuwa su zo maka ka yawaita Salati ga fiyayyen halitta da Iyalinsa tsarkaka.

اللّهم صلّ على محمد وآل محمد.🏵️

Imam Sadiq (as) ya ce:"Allah kaji ƙan mutanen da s**a kasance fitulu masu haskawa, sun kasance masu kira zuwa gare mu da...
06/05/2026

Imam Sadiq (as) ya ce:
"Allah kaji ƙan mutanen da s**a kasance fitulu masu haskawa, sun kasance masu kira zuwa gare mu da ayyukansu da jajircewar su, ba kamar wadanda suke watsa da sirrukanmu ba"

رَحِمَ اللهُ قوماً كانوا سراجاً ومناراً، كانوا دعاةً إلينا بأعمالهم ومجهودِ طاقتِهم، ليس كَمَن يُذيع أسرارنا

📚Tuhaf al-‘Uqul, p. 301

Address

Holy Shrine Of Imam Reza (AS), Mashhad
Mashad

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Ridah Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Imam Ridah Hausa:

Shortcuts

Share