13/08/2026
Hilar Rabi'ul Awwal Ta Bayyana
هَنِيئًا لِإِبْرَاهِيمَ لَاحَ هِلَالُهُ
هِلَالٌ بَدَا لِلنَّاظِرِينَ جَمَالُهُ
هِلَالُ رَبِيعٍ فِيهِ جَاءَ مُحَمَّدٌ
فَتَمَّ لَنَا الْبُشْرَى وَعَمَّ نَوَالُهُ
Fassara:
Albarka ta tabbata! Hilar Rabi'ul Awwal ta bayyana,
Hila ce mai kyawun gani ga duk mai kallonta.
Ita ce hilar watan da Manzon Allah ﷺ ya zo duniya,
Da zuwansa ne bishara ta cika, alherinsa kuma ya game duniya baki ɗaya.
💭 Watan Rabi'ul Awwal wata ne mai daraja a zukatan Musulmi, domin a cikinsa Allah Ya yi wa duniya baiwar aiko da Mafificin Halitta, Sayyidina Muhammad ﷺ, wanda Allah Ya sanya rahama ga talikai.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿وَمَآ أَرْسَلْنَٰكَ إِلَّا رَحْمَةٗ لِّلْعَٰلَمِينَ﴾
"Ba Mu aiko ka ba face a matsayin rahama ga talikai."
(Suratul Al-Anbiyāʾ: 107)
🤲 اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا محمد، وافتح علينا بركات شهر ربيع الأول، واجعل قلوبنا عامرةً بحبه، وارزقنا اتباع سنته ظاهرًا وباطنًا.
🌹 Maraba da watan Rabi'ul Awwal, watan hasken Manzon Allah ﷺ.