07/04/2022
FASSARAR RUHUL ADAB (5)
أعـــوذ باللــه من الشـيطن الرجيــــم
بـــــــسم اللـه الرحــمن الرحــــــيم
اللهـم صل علي أبو الفاطـــمة سيدنا محمد رنبز بن عبد الله و علي آله حق قدره و مقداره الـــعظيم
Bayan haka Yan uwa ina muku Barka da wannan lokacin ,K*m kai tsaye zamu Dora daga inda na tsaya a satin daya gabata.
K*ma zamu tashi baiti na 12.
Shehu yaci gaba da cewa ....
12) ولازم الخضور والسكونا
كذا ك خلوة تعين حين
K*ma Ku lazimci natsuwa ta kankan dakai da K*ma natsuwa ta zahiri
Haka na kebancewa yayin karanta lazimin zai taimaka sosai da sosai
13) واطلب مربيا خبيرا ناصحا
كامل عرفان إما صالحا
K*ma ka nemi shehi murabbi Wanda ya kewaye da komai K*ma me nasiha
Wada yake ciki da maarifa K*ma shugaba Salihi.
......
To Yan uwa Anan Akwai Jan hankali sosai Wanda ya kamata kowa ya santa
Lallai dole ne mutum ya ne mawa kansa shehi
Wanda kunga a yanzu ba haka akeyi ba
A yanzu shehi ne yake Neman muridai
Amma ba miridai ne suke zaban shehi da Kansu ba
To sharadi na farko shine kafin ka karbi darika wajibinka ne ka ne mawa kanka shehi
Shine ta hanyar bibiyar shehu nan kafin ka ta'allaka kanka da shi
Ka duba kaga shin ya kewaye da darikar.
Shin ya kewaye da hukunce hukuncenta
Shin yana da saukakawa ko yana tsananta wa muridai da dorawa muridai takalif
Shin yacika da maarifa ko kuwa , Kada kaje ka ci karo da Dan gyara samun SAA ya angizaka rami
Ta hakane zaka gane ya yake ya halayensa suke da dabi'unsa shin yana koyarqa Abu Annabi da shari'ar Annabi ko K*ma ba haka yake ba
Sabida baa bin ka'idar yanda aka shimfida tafiyar
Mina fata Allah ya gyara mana K*ma ya sanya irin wannan fadakarwa domin samarin mu su fahimci ma in aka dosa
To kunga Ashe shehu yana bamu shawara da cewa ba a wajen kowa zamu je mu karbi darika ba , Aa lallai Mi caje mu bincika mu kuma natsuwa kafin zabar shehi.
Domin duk Wanda ka zaba ya zaa shehinka to fa ka daka masa rayuwrka ne gaba daya.
To kuwa kunga dole a natsu a sami direba ko K*ma a afaka a cikin hadari.
To yan uwa Anan nake son in tsaya gobe InshaAllah.
Nasrul Ilm Hausa CI.
Sheikh Sherif Umar ABDEL'aziz RTA.