03/05/2026
⤵️LABARIN TAUSAYI 👇
Wata yarinya ce tana yawan zuwa wani studio ta saye CD
cassete a wajen wani saurayi, ashe son shi take yi, duk
lokacin da taje sayen cassete sai ta tsaya suyi hira, har ta fada
masa gidan su, ta bashi labarin iyayen ta.
Watarana sai tayi kwana bakwai bataxo ba! Sai saurayin nan
yaje gidansu da tayi masa kwatanci, domin ya tambaya lafiya
kwana 2 bai gane ta ba, bayan yaje, ya aika yaro sai mahaifiyar
ta ta fito, ta fada masa ai yau sati daya da rasuwar yarinyar,
nan take ya fadi ya suma, bayan an watsa masa ruwa ya
farfado... Yayi zugum Yana kallon su, sai mahaifiyar tace ya
shigo cikin gidan, ya shiga, ta jashi ta kai shi har dakin yarinyar,
suna shiga yaga hoton sa manne a bango, mahaifiyar ta bashi
labarin irin yanda yarinyar ke son shi, ta dauko tulin kasusuwan
da yarinyar ke saye daga gareshi, tace ka gansu bata taba
bude ko daya ba, na sha gaya mata idan taje wurin ka, ta fada
ma tana son ka. Ta aje kasusuwan kusa gareshi, ya diba su
daya bayan daya, ba wanda aka bude.
Ashe tana zuwa ne ta saye cassete, don kawai ta gan shi suyi
hira, sai kawai ya fashe da kuka! Mahaifiyar tace lafiya? Sai ya
bude mata cassete guda taga wasika a ciki, ashe shima duk Lokacin da taje siyan
cd da ta saye sai ya rubuta mata wasikar soyayyarshi aciki.
Yan uwa mata da maza in kina son mutum ki fada masa, kar
kiyi zurfin ciki. Allah sarki to wannan shine Allah yasa mudace ameen suma ameen 🙏