Zauren Fiqhu 1

Zauren Fiqhu 1 Mun bude wannan shafin ne domin fadakarwa da kuma illimantarwa muna fatan zaku kasance tare damu
(1)

HUKUNCIN YIN AZUMIN NAFILA GA WANDA A KE BINSA BASHIN FARILLA:𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓:Shin ko ya halatta yin azumin nafila ga wanda a k...
31/03/2026

HUKUNCIN YIN AZUMIN NAFILA GA WANDA A KE BINSA BASHIN FARILLA:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Shin ko ya halatta yin azumin nafila ga wanda a ke binsa bashin farilla? shin dole ne sai ya fara gabatar da ramuwar wannan farillar sannan ya ke da ikon yin nafila ko kuma a'a zai iya yin nafila daga bisani kuma yayi farillar?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
An samu maganganun malamai k**ar guda uku akan haka:

1. Ƙauli na farko shi ne, Mazhabin Hanafiyya da Zahiriyya sun tafi a kan cewa kai tsaye ba tare da wani karhanci ba ya halatta mutum yayi azumin nafila kafin ya rama wanda a ke binsa na ramadan.
Dalilinsu na cewa ya halatta shi ne, s**ace ba wajibi ba ne ga wanda a ke binsa bashin azumi a ce sai ya ramashi cikin gaggawa, dan haka yana iya jinkirta yin ramuwar azuminsa zuwa wani lokaci na gaba, sannan s**a kafa hujja da wannan Hadisi na A'isha matar Mαnzoи Aʟʟαн (Sallallahu alaihi Wasallam) wanda take cewa:

"كان يكون علي الصوم من رمضان فما أستطيع أن أقضيه إلا في شعبان"
MA'ANA:
Ya kan kasance akwai ramuwar (azumin) ramadan a kaina amma ba na samun ikon rama shi har sai sha'aban ya zo.

Dan haka anan s**ace wani lokacin uzuri ya kansa A'isha ta kasa rama azumin da ke kanta har sai watan sha'aban ya zo ta ke ramawa.

Sannan s**ace abu ne sananne ga A'isha wajen kwaɗayinta na yin nafiloli, dan haka zeyi wahala a ce wai ba tayin azumin nafila musamman k**ar irin su: azumin tasu'a, azumin ashura, azumin ranar arfa, azumin sitta shawwal, da kuma azumin watan zulhijja.

2. Ƙauli na biyu shi ne, Mazhabin Malikiyyj da Shafi'iyya sun tafi a kan cewa makaruhi ne a kan wanda a ke binsa bashin azumin farilla kuma yace zeyi na nafila.
Dalilinsu kuwa shi ne, s**ace mutum ya fara biyan bashin da a ke binsa na azumi shi ne yafi muhimmanci a gare shi a kan ya shagaltu da yin azumin nafila, dan haka s**ace makaruhi ne.

3. Ƙauli na uku shi ne, Mazhabin Hanabila an samu ƙauli guda biyu a wajensu, akwai ƙaulin da s**ace ya halatta sannan akwai ƙaulin da s**ace haramun ne mutum yayi azumin nafila dole sai in ya fara rama wanda a ke binsa bashi tukuna, daga cikin dalilansu na cewa haramun ne sun kafa hujja da wannan hadisi ko da yake wasu Malamai sunce hadisin bai inganta ba:

"………ومن صام تطوعا وعليه من رمضان شيء لم يقضه لم يتقبل منه"
MA'ANA:
………Wanda yayi azumin nafila alhali akwai wani abu na ramadan a kansa da bai rama ba to ba za a karɓa masa (azumin nafilar da yayi ba)

To amma magana mafi inganci k**ar yadda mafi yawan Malamai s**a rinjayar itace, ya halatta mutum yayi azumin nafila musamman azumin da a ka iyakanceshi da wasu raneku na musamman k**ar azumin ranar arfa da sauransu, wanda idan lokacinsu ya wuce shikenan sun kuɓucewa mutum, to a nan ya halatta mutum yayi wannan azumin ko da kuwa ana binsa bashin na farilla da bai rama ba, sai dai duk da cewa ya halatta ayi to amma abu mafi kyau shi ne an fi son mutum ya gaggauta biyan bashin da a ke binsa na farilla.

Amma idan ya kasance azumin sitta shawwal ne Malamai s**ace mutum ba zai yi ba har sai in ya fara rama wanda a ke binsa na ramadan tukuna, domin wanda ya cika azumin ramadan to shi ne idan yayi azumin sitta shawwal za a bashi ladan k**ar yayi azumin shekara, dan haka sai Malamai s**ace wanda a ke binsa ramuwar azumi to ko da yayi azumin sitta shawwal ba shi da lada domin shi bai kammala azumin ramadan ba.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ



ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Follow TAMBAYA DA AMSA's WhatsApp channel. ‎Mun Buɗe wannan Channel ne domin Amsa Tambayoyin Al'ummar Musulmi baki ɗaya. Duk mai tambaya zaibi Admin ta private ya gabatar da Tambayarsa.
فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّڪۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
"Ku Tambayi Ma'abota sani idan yazama baku sani ba"

GROUP ADMIN: ✍️ 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟
+2348087788208
[email protected].‎ Join 47K followers for the latest updates.

YADDA AKE YIN SALAATUT TASBEEH::𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓: Assalamu Alaikum malam Yaya ake yin Salaatut Tasbeeh? Menene ingancin ta?:𝐀𝐌𝐒𝐀...
31/03/2026

YADDA AKE YIN SALAATUT TASBEEH:
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamu Alaikum malam Yaya ake yin Salaatut Tasbeeh? Menene ingancin ta?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
W Alkm Slm W Rhmtul Laah.

Salaatut-Tasbeehi wata Sallah ce mai raka’o’i huɗu wadda ake karanta Tasbihi har sau ɗari uku a cikinta. Lafazin Tasbihin shi ne: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’.
Ma’ana: Tsarki ya tabbata ga Allaah, kuma Godiya ta tabbata ga Allaah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, kuma Allaah ne mai Girma.

Shari’ar Musulunci ta kwaɗaita wa masu Imāni yin wannan sallar. Tana jawo wa musulmi gafarar Zunubansa na farko, da Zunubbansa na ƙarshe, da Zunubbansa daɗaɗɗu, da Zunubbansa sababbi, da Zunubbansa da ya yi cikin kuskure, da Zunubbansa da ya yi da gangan, da Zunubansa ƙanana da Zunubbansa manya, da Zunubbansa na ɓoye, da Zunubbansa na bayyane.

Kuma an so a riƙa yin wannan sallar sau ɗaya a kowace rana in da hali, ko sau ɗaya a kowane mako, ko sau ɗaya a kowane wata, ko sau ɗaya a kowace shekara. Idan kuma ba haka ba, to sai ya yi ko da sau ɗaya a cikin rayuwarsa.

Haka mālaman Hadisi irin su: Al-Imām Muslim, da Al-Imām Abu-Dāwud, da Al-Imām As-Subkiy da Al-Hāfiz Ibn. As-Salāh, da Al-Hāfiz Ibn. Hajr Al-Asqalāniy, da Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihim) duk sun kyautata wannan hadisin saboda yawan hanyoyinsa.

Kamar kuma yadda aka samu wasu malaman irin su: Al-Imām Al-Baihaqiy yana cewa: ‘Abdullāh Bn Al-Mubārak ya kasance yanā yin Salātut-Tasbihi, kuma sashen mālaman ƙwarai (Sahihai) sun riƙa koyonta daga sashensu!’

SIFFAR YADDA AKE YIN SALAATUT TASBEEH:

1. Da farko musulmi zai yi shiri irin shirinsa na sallah, yayi alwala sannan ya fuskanci alƙibla, ya yi niyyar yin Salātut-Tasbihi a zuciyarsa ba a baki ba, yana mai furta kabbarar harama da bakinsa.

2. Zai ɗora hannun damarsa a kan na hagunsa a bisa ƙirjinsa k**ar dai yadda tsayuwar mai sallah ta ke, sannan ya karanta Fātihah da Sūrah bayan ‘Du’ā’ul Istiftāhi’.

3. Bayan ya kammala karatun Sūrāh, sai ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma sha biyar (15), sannan ya yi kabbara ya yi ruku’u.

4. A cikin ruku’u bayan ya ƙare zikirorin da aka saba yi, sai ya sake faɗin ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sai kuma ya ɗago daga Ruku’un.

5. Bayan ya gama zikirorin ɗagowa da tsayuwa da bayan ruku’u sai kuma ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10), sannan ya yi sujada.

6. Bayan ya gama zikirorin da aka saba yi a cikin sujada sai kuma ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sai kuma ya ɗago daga sujadar.

7. A zama tsakānin sujadu biyu zai karanta zikirorin da aka saba yi a wurin kafin ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sannan ya koma ya yi sujada ta biyu.

8. A cikin sujada ta biyu zai karanta zikirorinsa k**ar yadda ya yi a sujada ta farko, sannan ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Sai kuma ya ɗago daga sujadar ta biyu ya zauna.

9. A cikin wannan zaman da mālaman Fiƙ-hu suke kira ‘Jilsatul Istirāhah’ babu wani zikiri da ake yi a asali, don haka sai dai kawai ya ce: ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau goma (10). Daga nan sai kuma ya miƙe tsaye zuwa raka’a ta biyu.

10. A cikin raka’a ta biyu zai yi k**ar yadda ya yi a raka’a ta farko, sai kuma ta uku sannan ta huɗu.

A kowace raka’a, zai ga ya faɗi ‘SUBHĀNAL LĀH, WAL HAMDU LIL LĀH, WA LĀ ILĀHA ILLAL LĀH, WAL LĀHU AKBAR’ sau saba’in da biyar (75) ke nan. A cikin raka’o’in huɗu kuma ya samu faɗi har sau ɗari uku (300) kenan daidai!

Allaah ya ƙara mana taimako da himma a kan karatun Hadisi da Aiki da Shi.

Ina ga wannan bayani ya amsa wannan fatawar, in shaa’al Laah.

Wal Laahu A’lam.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

Follow TAMBAYA DA AMSA's WhatsApp channel. ‎Mun Buɗe wannan Channel ne domin Amsa Tambayoyin Al'ummar Musulmi baki ɗaya. Duk mai tambaya zaibi Admin ta private ya gabatar da Tambayarsa.
فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّڪۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
"Ku Tambayi Ma'abota sani idan yazama baku sani ba"

GROUP ADMIN: ✍️ 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟
+2348087788208
[email protected].‎ Join 47K followers for the latest updates.

_🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Haqiqa A Cikin Dare Akwai Wata Sa'a Wadda Bawa Musulmi Ba Zai Dace Yana Mai Roqon Allah Wan...
31/03/2026

_🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Haqiqa A Cikin Dare Akwai Wata Sa'a Wadda Bawa Musulmi Ba Zai Dace Yana Mai Roqon Allah Wani Alkhairi A Cikinta Ba, Face Ya Bashi Wannan Abin.🌹🌹_

Muslim

SUNNONIN RAWATIB::𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓:Assalamu malam dan Allah ina neman bayani akan nawafil 12 da ake son mutum yayi a kullum:𝐀𝐌𝐒𝐀...
31/03/2026

SUNNONIN RAWATIB:
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamu malam dan Allah ina neman bayani akan nawafil 12 da ake son mutum yayi a kullum
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Sunnonin waɗanda ake cewa: rawatib guda goma sha-biyu ne wanda ambaton falalarsu yazo acikin hadisin ummu habiba yardar Allah takara tabbata agareta, duk wanda yabasu kulawa yana yinsu Allah zai gina masa gida A'aljannah, sune:

Raka'a biyu kafin sallar asuba, da raka'a huɗu kafin sallar azahar, da raka'a biyu bayanta, da raka'a biyu bayan magariba, da raka'a biyu bayan isha'i.

Lokacin nafilar da'ake kafin ayi sallar farillah yana shiga dazarar lokacin sallar farillar yashiga, idan akayi kiran sallar asuba ko azahar to lokacinta yashiga kafin ayi sallar farillah.

Sannan dazarar an kammala sallar farillah lokacin nafilar da'ake bayan sallah yashiga har zuwa fitar lokacin sallar farillar.

Sannan ana yinsune raka'a biyu- biyu, ayi sallam ba'a haɗesu ayisu gaba ɗaya.

Bai k**ata ga musulmi yayi wasa wajan yin sallar nafilar da'akeyi lokacin sallolin farillah, ko jinkirta yinsu alokacinsu saidai inda uzuri, k**ar mantuwa ko rashin lafiya ko shagaltuwa dawani abu wanda yake dolene alokacinsu, saboda abunda ke ciki na kubcewar lada mai girma gawanda yakiyayesu alokacinsu.

Idan sun kubcewa mutum toya duba yagani saboda uzuri s**a kubuce masa, k**ar bacci ko mantuwa ko shagaltuwa, ya halatta yaramasu akowanne lokaci yaso.

Idan ba saboda wani uzurine baiyisuba to bai halatta ya ramasuba, idan yaramasu bashi da lada, saboda duk wata ibada wacce take da lokaci kayyadadde tana wucewa da wucewar lokacinta.

Idan s**a kubcewa mutum saboda wani uzuri, ya halatta yaramasu akowanne lokaci yaso cikin dare ko rana.

WALLAHU A'ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ

Follow TAMBAYA DA AMSA's WhatsApp channel. ‎Mun Buɗe wannan Channel ne domin Amsa Tambayoyin Al'ummar Musulmi baki ɗaya. Duk mai tambaya zaibi Admin ta private ya gabatar da Tambayarsa.
فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّڪۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
"Ku Tambayi Ma'abota sani idan yazama baku sani ba"

GROUP ADMIN: ✍️ 𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟
+2348087788208
[email protected].‎ Join 47K followers for the latest updates.

*AZUMIN FARAREN KWANAKI (AYYAMUL BHIDH) NA WATAN SHAWWAL, 1447 A.H*Daga Abu Huraira (R.A) Yace: "Badaɗi na yayi min wasi...
31/03/2026

*AZUMIN FARAREN KWANAKI (AYYAMUL BHIDH) NA WATAN SHAWWAL, 1447 A.H*
Daga Abu Huraira (R.A) Yace: "Badaɗi na yayi min wasiyya da abubuwa guda uku, ba zan bar su ba har na mutu; azumin kwanaki uku a kowane wata, sallar walaha da kuma yin wutiri kafin nayi bacci" (Bukhari)
Manzon Allah (S.A.W) Yace: "Azumin kwanaki uku a kowane wata yana dai dai da Azumin shekara" (Bukhari da Muslim)
*Azumin zai k**a*
*LARABA 1/4/2026*
*ALHAMIS 2/4/2026*
*JUMA'A 3/4/2026*
Mai nuni zuwa ga aikin alheri k**ar mai aikatawa ne.



22/02/2026

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zauren Fiqhu 1 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share