27/07/2026
YAWAN MAGANA DA TASIRINTA GA RAYUWA
Ba kowace magana ce ake buƙatar faɗa ba. Wani lokaci, yin shiru ya fi magana amfani.
Yawan magana ba tare da tunani ba na iya sa mutum ya yi kuskure cikin sauƙi, ya faɗi abin da zai ba shi nadama, ko ya rasa natsuwa. Amma idan mutum ya saba yin magana cikin hikima, ya zaɓi kalmominsa, kuma ya yi shiru idan babu abin alheri, hakan yana ƙara masa mutunci da kwanciyar hankali.
Darasi:
Ka sanya kalmominka su zama masu amfani, masu gina zumunci, da kawo alheri. Idan kuma babu abin da zai amfanar, yin shiru na iya zama mafi alheri.
Allah Ya ba mu hikimar amfani da harshe ta hanya mai kyau, Ya sanya kalmomimmu su zama sanadin alheri. Amin.