17/03/2026
RUFE TAFSIRIN RAMADANA 1447BH - 2026HA
A jiya Litinin Malaminmu Mal. Nuruddeen Fateh (Sarkin Malaman Zango) ya rufe tafsirin dake gabatarwa a Masallacin Alaramma mai block dake unguwar Zango ta yamma, Bauchi.
Muna roƙon Allah (S.W.T) ya sakawa Malam da Alheri ya ƙarawa Rayuwarsa da Iyalinsa Albarka ya sanya a mizanin hasanat ɗinsa, mu kuma Allah ya bamu ikon aiki da abubuwan da muka saurara su amfane mu Duniya da Lahira, Allah ya kaimu baɗi da rai da lafiya da imani ya kuma bamu ikon halarta, Amin.